NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 40

anta yasha wanka da wata danyar Shadda Fara gurin gaba daya ya karade da Qamshin turarensa. *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 4 Ya ganeta, amma da alama it bata gane shi ba tace,qasa qasa ta harareshi tace "Ka tsorata ni wallahi, kuma bansan qofar shigan ba. Daga gidan Maman Asad nake ta bada naman suna a kawowa Hajiya" ta qarasa tana miqa masa ledar Naman. Se yayi gaba yana cewa "Muje na nuna miki" Tsabar neman magana irin nata bibsa take a baya tana kwaikwayon tafiyar sa da yake yi cikin nutsuwa kamar me qirga takunsa. Gulmarsa take a zuciya tana cewa "Ji yanda yake wani yanga dan Allah kamar mace ya ware qafa yayi sauri Aa se batamun lokaci yake" a haka ya tura babbar qofar dake part din farko ya shiga da sallama ta rufa masa baya. "Zauna, bari nayi mata magana inaga tana sama" ya fada yana wucewa matakalar bene, seta nemi daya daga kujerun palour ta zauna tana bin ko ina da kallon. Kayan cikin palour sun dan tsufa amma da yake masu kyau ne da asalin tsada ga kuma ingantacciyar tsafta da suke samu seya boye tsufan nasu. Ko ina qalqal se daukar ido yake ga qamshin turaren wuta daya hadu da sanyin Ac suka qarawa gurin nutsuwa ta musamman. Babban Enlargement photo dake kafe a bangon palor ta ringa kallo, Wanda take kyautata zaton shine megidan tareda matar gidan se yaransu guda bakwai maza biyu mata biyar. Kallon su take tanaso ta tuna inda tasan fuskar dan kusan duk kamar su daya sedai wasu sunfi wasu haske a ciki amma ta kasa tunawa. Bataji sakkowarsu ba se maganar babbar mace da take cewa "Sannu da zuwa yammata" Zamowa tayi daga kujerar tayi ta shiga gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska. Kanta a qasa saboda kwarjinin da matar tayi mata ta miqa mata ledar tana cewa "gashi inji Maman Asad tace a kawo" "Toh naman suna ne aka biyo mu dashi dukda bamu shiga ba? An gode Allah ya raya Ummu-salma, kice mata tayi haquri wallahi qafata ce ta motsa abinda ya hanani fitowa kenan amma in sha Allahu zanzo naga baby" Hajiyan ta fada kafin ta cigaba da cewa "Qanwarta ce ko qanwar Habibu?" "Qanwar tace ni" Umaimah ta bata amsa cikin qaguwa, to tambayar kuma ta mecece haka. Ita kuwa Hajiya cikin son janta da hira ta ci gaba da cewa "Allah sarki ban taba ganinki ba, na dan san qannen nata kuma musamman Nuratu indai tazo takan shigo mu gaisa" "Gwana uwar an cusai kenan, wato taga qaton gida har wani shiga take su gaisa Allah ya sawwaqawa Yaya Nuratu dai" Umaimah ta fada a ranta a fili kuwa tace "Allah sarki ai Nuratun nake bi, nice autar su a Mata" se ta miqe tsaye "Aa badai tafiya ba kuma muna cikin yar hirar mu, gashi ma ko ruwa baa kawo miki ba 'Habiba kina ina ne? Ki kawo mata ruwa" Hajiyan ta fada. Se ta fara tafiya tana cewa "Aa wallahi babu komai Hajiya bari naje aiki mukeyi ne se an jima" "Toh shikenan ki gaida gida na gode, se kin sake shigo mana ko, yaya sunan yar tawa?" "Umaimah" ta bata amsa tana dan murmushi "Toh Umaimah ki gaishe da Hajiyayyen nagode kinji" daga nan sukayi sallama ta fice kamar wadda take akan qaya. Tana fita Khalil ya fito daga wata qaramar qofa ya canza kayan jikinsa zuwa dogon wadon jeans da T-shirt yanata zuba qamshi. "Sannu Babana mutanen zazzau kunsha hanya amma kunyi sauri kamar wanda kuka taho a iska" Seda yasha ruwan da aka kawowa Umaimah bata sha ba kafin yace "aikinsan yanzu hanya ta gyaru sunci qarfin aikin titin sosai shiyasa tafiyar take sauri kuma bamu zauna ba ana daura auran muka taho harda Amaryar dan a shirye suke suma" "Masha Allahu Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana na yan baya lafiya, kana kallo dai daga sa'anninka gashi nan layi ya fara zuwa kan qannenka sun fara aje iyali kai ko kunya baka ji sedai kasa shadda ka tafi daurin aure ka kasa yunquri kai azo naka" Hajiya ta fara qorafin nata na kullum indai aka yi zancen aure. Murmushi yayi ba tareda ya bata amsar maganar tata ba ya waiwaya yana duban palour yace "ta tafi kenan" "Wacece?" Hajiyan ta tambaye shi, seda ya sake kurbar ruwa kafin yace "Umaimah" shikansa se da yaji wani iri, yama akayi ya riqe sunanta?/yanda ya kira sunan seka rantse shiya rada mata shi. Kallonsa Hajiya tayi da mamaki jin ya kama sunanta, "ka santa ne daman?" Ta tambaye shi tana tsare shi da ido. Seya duburburce, ya manta shaf da halin Hajiyar tasa, yanzu abinda be faru bama tunda akayi haka seta qullo shi wai wa ma ya aike shi nuna ya santa ne? Koda yake yarinyarce, ta shige masa yanda beyi zato ba. "Magana nake maka ka tsareni da ido kayi shiru, ko baka ji me nace bane?" Ta fada ganin gaba dayama hankalinsa baya gurin, se yayi firgigit yana shafa kai yace "Aa fa Hajiya ni ban san ta ba, sau daya na taba ganinta d
🏠