sallama suka fito ganin dalibai nata zuwa karban exam card zaman shi kuma kamar yana raba masa hankali.
"Ka gaida Hajiya dan Allah, insha Allahu qarshen satin nan zamu shigo da madam tunda sunyi arba'in" Nasir ya fada daidai sanda suka isa inda Khalil ya ajiye Lifan dinsa.
"Aa abokina ina motar ne naganka da Mashin kuma?" Nasir din ya sakw fada.
"Kai rabu da motar nan, kasan 306 da matsalar belt, haka kawai ina tafiya se ya cire kai na gaji dai kawai na siyar da ita na siyi wannan yafi mun na shiga ko ina hankalina a kwance".
"Tab, gaye iya gaye ashe gurgune" Nabila Sani ta fada tana kallon Khalil dake buga machine, tunda suka fito ta saka su zama a kujerun da suke kusa da Office din saboda harga Allah Khalil din ya tafi da imaninta, jira take ya fito tasan ta yanda zata yi masa magana se ga wannan big turn off din, ashe ma wankan ne kawai aljihu babu ko sisi.
"Arziqi nufin Allah ne, kuma dan kin ganshi da lifan shine aka ce miki matsiyaci ne wallahi Nabila ki dena abinda kike shiyasa har yau kika rasa ko wanda ze kiraki a waya ki rage dare" Umaimah data kalli Khalil din itama ta juya tana gayawa Nabila.
"Allahu akbar, Allah ka nuna mana Annabi, yau Umaimah ce takewa wani fadan yayi ba daidai ba lallai inda ranka kasha kallo" Halima ta fada cikin sigar tsokana dan daman ita gwanace.
"Se ku tashi mu tafi ai" Nabilan ta fada a fusace fuu tayi gaba suka rufa mata baya suna sake caccakarta.
Murmushi Khalil da duk abinda suka fada yaji yayi dan da dan qarfi suke maganar bayan haka yana da kunne sosai, Kallon Nasir yayi dake danna waya yace
"Nas kodai na shiga gurin nan ne, dagaske fa yarinyar nan tamun over taking"
"Abokina ka shiga kawai mana tsoron me kake ji, babu komai in sha Allahu tsamu tsaya maka kawai dai ka shirya ina qara gaya maka akwai daru" Nasir ya fada yana bashi hannu,
"Shikenan zanyi tunani akai" daga nan sukayi sallama ya buga mashin dinsa yayi gaba. A bakin get ya sake haduwa dasu suna jiran abin hawa, sukayi ido hudu da Umaimah ta kuwa murguda masa baki da harara yayi mata murmushi ya wuce abinsa.
Cikin taimakon Allah suka qare jarabawarsu tsaf saura jiran sakamako, ranar ansha hotuna anyi celebration, akwai Dinner da suka shirya yi an dade ana hada kudi daman dan harda anko suka fita Umaimah ta biya kudin komai amma bata jin zataje, tasan ma baza'a barta ba yanzu kuwa da take gudun laifi bazata fita babu izini ba. tunda suka fara jarabawa daman a faduwar gaban abinda yake gaba take, furucin Abba na idan bata fitar da Miji ba ze bada ita sadaka na bala'in damunta ta kuma rasa yanda zatayi.
Ta nemi shawarar Rumasa'u akan maganar tace mata tayita Addu'a kawao Allah ya yi mata zabi na gari, ta kuma ce mata ta gwada neman wanda taga hankalinta yafi kwantawa dashi cikin samarinta na baya ko Allah zesa a dace amma babu nasara.
Duk wanda tayi qoqarin bugun cikinsa akan batun aure zillewa suke, qiriqiri suke nuna mata suna sonta da gaske amma bazasu iya da halinta ba wannan abin na bala'in qona mata rai, ita wane hali ne da ita?
Shin laifi ne dan kayi kishin abinda kake so su ba abin alfaharin su bane ma ace ana kishin su?
Kusan sati da gama makarantar su babu wanda yace mata qala akan batun aure, ba kamar baya ba yanzu komai ya dawo daidai a gidan itace ma take dararewa wani lokacin saboda gudun kar a diro mata da maganar fito da Miji katsahan. Fita ce dai aka hanata, dan ko Islamiyyar da take zuwa Asabar da Lahadi ma Abban ya soke yace yawo ne kawai, daidai gwargwado ta samu ilimi ta zauba agida tayita tilaqar abinda ta sani amma fita indai bada dalili me qarfi ba be yarda ba.
Ana haka Yayarsu Anty Hajiyayye ta haihu, dayake CS akayi mata da farko akace a dawo da ita gida ta zauna idan jikinta ya warware seta koma tunda a can babu mataimaki ga yara kuma amma Abban su yaqi, daga qarshe dai dakyar Mama ta lallabashi akan tunda Umaimah bata komai taje ta zauna mata tareda wata mata da aka samu har zuwa sanda zata warware.
Seda ya kafa mata warning sosai ya kuma jawa Hajiyayyae kunne akan duk in yaji ba daidai ba se ranta yafi na kowa baci haka ta tattara ta tafi gidan Yaya Hajiyayyen.
Washe garin suna da yake ba taro sukayi ba bayan an gama suyar nama an kasa Yaya Hajiyayye ta bata tace ta shiga gidan da yake kallon nasu takai.
Dogon Hijabi har qasa ta dora akan Doguwar rigar material din jikinta fuskar nan kamar ko yaushe babu ko digon kwalli akan ta amma da yake kyanta daga Allah ne se gata ta fito shar abin ta.
Tun daga wajen gidan ta tabbatar da gidan masu arziqi ne, idan ma a yanzu babu to tabbas da an samu ta tura qofar get din da take a bude ta shiga qaton compound din gidan da sallama. Babu kowa a tsakar gidan, taja ta tsaya ganin qofofi biyu ne manya bata san wanne ne ta shiga ba, gashi ma ta manta ta tambayeta wa zaa kaiwa dan qila mata biyu ne a gidan.
Daga bayanta taji ance
"Ya kika tsaya? Bismillah ki shiga suna ciki" seta juya a firgice dan bataji takun takalma ba se magana kawai, ido hudu sukayi da Khalil dake tsaye a bay