du, saboda ya raina mata hankali ita ze kalla yace yana so harma ya samu Abban su? Ai kuwa seya gane kurensa, ze san ita ba sa'ar wasan sa bace.
Tana barin gurin Abbaya fito daga daki yana murmushi yace "Ja'ira, Allah dai ya shirya Umaimah yasa ta dena abinda takeyi"
Mama dake jimami ta amsa da "Amin dai, amma Alhaji zancen nanda watan nan daka qara daga qafa. Aurefa ba abin gaggawa bane, dole seta samu wanda suka daidaita ya ga ze iya da ita tukunna dan kasan bazaayi abu a gurguje ba ba tareda an fahimci juna ba ba fata ba daga baya ta falle halinta mutum yazo yana cewa an rufe shi".
Seda ya zauna yaja shayin data saisaita masa kafin yace " Nasani nima na fada ne kawai saboda na qara tsoratar da ita dan tana tsaye ta labe ba tafiya tayi ba, dukda haka da gaske nake ta mayar da hankali ta tsayar da Miji dan naga sako sakonda taga ana mata ya saka take duk iyashegen da takeyi, dan haka karma ki kuskura ta gane ba haka bane".
Umaimah kuwa Haka ta kwana tana juya maganar fito da miji a wata daya, toh ta ina zata fara ma bayan tunda Qasim ya fasa kamar wanda ya tafi da duk farin jininta ko a hanya wani be sake tare ta da sunan soyayya ba.
Idan ta tuna wai Lawan yace yana sonta kuwa wani takaici ne yake taso mata, ta quduri niyyar qare masa tanadi tsaf duk randa sukayi ido hudu kuwa.
Washe gari guraren 10 sega Yaya Aminu da sabuwar waya Infinix me kyau ya kawo mata. Ta karba tayi godiya kafin ta kunnata ta jona a chaji ta wuce makaranta dan daman shiri take.
Fix lecture ce ta wani malami da be samu ya gama musu darasin sa ba ga lokacin Exam yayi. Tana shiga Ajin ta hango Rumasa'u da yanzu ko kallon arziqi ba tayiwa inda suke se ta zarce gurin nata dukda su Halima dake mata magana suna nuna mata gurin da suka tanadar mata amma bata kula ba.
Sallama tayi musu ka gaisa da wadanda ke kusa da Ruman kafin ta zauna akan desk din gabanta tace
"Hajiya Ruma fushin ne har yanzu baa sakko ba" dauke kai gefe Ruma tayi tace
"Fushi? Aini ba fushi nake ba Umaimah, buqatata ne bakyayi a cikin rayuwar ki shi yasa na fita na barki da masu hali da ra'ayi irin naki tunda bakya son gaskiya".
"Uhm to yanzu dai ai komai ya wuce, bayan haka fa keda Nabila kukayi cacar baki ba dani ba amma da kika tashi kikayi mana kudin goro gaba daya"
"Ai sanda take zagina ta kirani mayya kurmancewa kikayi da kika kasa magana ko kuwa? Kinga dan Allah matsamun a nan ga malam nan ya shigo" ta qarasa tana janyo littafi daga cikin jakarta.
A kusa da ita Umaimah ta zauna har aka qare lecture din dukda Ruman ba kulata take ba, malamin na fita ta sake kafa mata surutu har seda Rumah ta sakko daga fushin tace mata
"Na haqura amma dai bazan sake jerawa dake ba in dai kina tare da wadancan da basu san ciwon kansu ba" ta fada tana hararar Nabila da tun zaman Umaimah a gun hankalin na kansu.
"Baki haqura ba kenan, itama Nabilan zan mata magana zata baki haquri akan abinda tayi shikenan?"
"Ba shikenan ba, kinsan ni a rayuwa bana jurar wulaqanci bazan tsaya wata banza ta gaya mun magana ko da da nake musu shiru kin sani ba tsoron su nake ba kawaici ne amma yanzu daidai nake da kowacce yarinya a cikin su"
"Ohni Rumah kin zama masifaffiya toh dai dan Allah kiyi haquri" Umaimah ta sake fada
"Shikenan, na haqura"
Da haka suka miqe gaba daya suka nufi qofa. A kusa da su Fauziyya Umaimah ta tsaya tana cewa
"Ku tashi muje mu karbo exam card"
"Yar wulaqanci se yanzu kika san damu bayan kina shigowa muka baki seat amma kika share kikayi tafiyarki abin ki" Fauziyyan ta fada, Nabila kuwa tabe baki tayi suna yar harara da Rumasa'u dake gaisawa da Halima Amarya.
A waje suka zauna saboda Me bayar da Exam card dinbe riga ya qaraso ba,
"Waini meya farune Ruma da Nabila naga se wani fizge fizge kukeyi lafiyar ku kuwa?" Halima ta fada tana kallo su. Fauziyya ce ta labarta mata abinda ya faru tsaf se ta kalle su gaba daya tace
"Ai gaskiya ta fada muku, wallahi Umaimah idan baki canza wannan halin ba babu namijin da ze iya zama dake. Kai gidan aure fa ya wuce duk yanda kuke hasashensa, kunga dai zazzafar soyyar nan da mukayi da Hayati to wallahi ko sati bamu rufa ba muka fara bala'i kawai dan ya bar wayarsa na dauka ina bincike.
Da na zata shwarwarin banzar da muke a nan zasu kawo mun mafita na hau na zauna akai ashe qara tabarbara abubuwa kawai zanyi badan Allah yaso ni Anty Zully tamun orientation ta gayamun gaskiyar abinda yake akwai ba ai inaga da yanzu wani zancen ake ba wannan ba.
Toh wallahi tun wuri in zakuyi hankali kuyi in ba haka ba, jikin yarinya ne ze fada mata"
"Gashi can an bude office din, ku tashi muje" Umaimah ta fada da rashin bama maganar Halima Muhimmanci, suka miqe gaba daya Halima nacewa
"Ina nan da daya da daya zaku same ni, dadina da gobe ai saurin zuwa" suka rankaya office din. Kwankwasawa sukayi aka basu izinin shiga suka tura kai gaba dayan su ciki, mutumin na zaune akan kujerar sa se wani akan kujerun da suke a gefe suna Hira suka shiga Umaimah ce akan gaba tayi sallama karaf idanunsu s