NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 99 of 136

ya Amma abinda yafi damuna koni bai taba kirana ba ko sau da har zuwa Yau". "A'a Zainab mu duka masu laifine lokacin daya kamata a saurare shi kowa baya ya juya masa, Banda Mai biyaya bane yanda Allah ya daukaka shi ko ganinsa basai yayi Mana wahala ba? Amma yaro Mai ladabi da biyyayya mun taru mun yi masa naqi ba dole yayi nesa damu ba". Saita balle da kuka, da kyar Ammi ta lallasheta tayi shuru. Sannan tayi mata sallama tana Kara jaddada Mata zuwan tare da fadin ta turo direbanta ya daukota Dan gidanta zata sauka tunda anan tabar motar data zo gurin Hajiyar da ita a Ranar data wuce YAMAI. Aunty Badi'a ce ta karaso kusa da Ammin tana fadin "ina ganin soyayyar uwar miji da matar d'a amma ban taba ganin irin taku ba inaga yanda Hajiya Inna ke sonki ko Yallabai Bata so haka gashi ta kwallafa rai kan Mahmud kamar me" Zama sukayi a Kan sofa daya dake cikin dakin. "Wlh Ni kaina Aunty Ina jinjina yanda Hajiya ke Sona da dukanin yarana shi yasa sau da yawa idan wani Abu ya taso a gidan bana Bari taji ko labarin sa Dan nan da nan zata tashi hankalin gidan sai Kuma abun ya Zama wani Abu daban Dan Kullum gani sukeyi na Gama da kowa a gidan ballentana abinda ya biyo bayan rigingimun da akayi wanda suka saka na baro musu gidan,sai Abun ya Kara zafi ganin irin tujarar da general yayi da irin hukuncun daya yanke". Dan nisawa Aunty Badi'a tayi kafin tace. "Abinda dai baiyi tsabta ba Kam sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba, Daman shigowa nayi muyi magana akan hukuncin da Zaku yanke ne hada Mahmud Aure da 'yar aminiyarki matar takawa, tun a jiyan naso mu tattauna sai nayi Baki sauka cinye lokacin, me ze Hana ki Bari aga dawowar tasa tukunna sannan kiyi masa tayin yazo yaga yarinyar idan Allah yasa tayi masa a irin matar da yake ra'ayin ta Zama iyalinsa Kinga shike Nan idan Kuma an samu sabainin haka Daman ba'a amsa ba bare zumuncin ku ya samu matsala ko ya Kika gani?". Shiru Ammi tayi tana nazarin maganar matar yayan nata Kuma 'yar uwa abokiyar shawara. "To ai abin dubawa Aunty kada fulani taga ban kyauta mata ba tayi min na huce ace na buda Mata kasa a ido bazan iya ba, idan Allah ya dawo dashi mijin mace hudu ne idan Yana da wadda yake muradin aure ya Kara da ita Dan nasan bazeki Haura'ul Insiyya ba, duk abinda ake nema ga Diya mace Allah yayi Mata ga uwa uba nasaba". "Haka ne Allah ya dawo Mana dashi lfy ya Kuma zaba abinda yafi Alkhairi, Amma dai in ina Raye wlh ba Mai yiwa yarona dole ba ruwana da Amincin ku can tsaninku" Baki Ammi ta Kama tana Fadin "Tofa kaji masu 'ya'ya wato kin nuna side ko?" "Ki fadin koma meye Amma dai a barmin yaro ya samu peace of mind gaskiya, shi bashi da idon ganin matan ne? Ina cewa kasashen duniya yake yawo Kinga kuwa wane irin Mata ne be gani ba, Kuma da bakinki kike fadin yace shi da wadda yake so daman biyayya ce kawai zeyi ya karbi auren da aka bashi Amma komai Daren dadewa zeyi wani auren to ki cire kanki a cikin jerin masu tilasta 'ya'yan su auri abinda sukeso, ki bishi da addu'ar Allah ya hada shi da abokiyar Zama ta gari kawai, se kimarki ta karu a idanunsa ki Zama abokiyar Shawarar sa babu abinda ze rufe Miki Amma kina shigo Masa da irin wannan zance ze Miki wani aji na daban, baze saki jiki dake ba balle kisan menene matsalarsa, ki tsaya kiyi nazarin abin nidai shawara ce na baki" Tunda Aunty Badi'a ta Fara Kora bayani jikin Ammi yayi sanyi saboda suk abinda Aunty Badi'ar ta fada gaskiya ne, nisawa Ammin tayi "haka ne Aunty wannan observation ne me kyau hakan zanyi Daman fulanince ta Fara kawo maganar Naga Kuma ya dace na Bata goyon baya, Amman in Sha Allah zanbi Shawarar ki...✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI ✨✨✨ Page 33. MAMAN FATEEMAH. ________Zahra ta Dade a kwance tana sakawa da kwancewa, wani irin yanayi takeji a jikinta ita abun har mamaki yake Bata "Wai menene hakan" tayi tambayar da ba Mai Bata amsa. abinda takeji wani Abu ne na daban Wanda Bata taba Jin irinsa ba akan kowane da namiji ba, cikin kankanin lokaci ya cika Mata zuciya ita abun har kunya yake Bata,ta gama bore harda su somewa dasu wunin Asibiti Kuma yanzu a wayi gari a ganta dumu dumu cikin soyayyarsa ai da kunya wlh. Wani tunanin ta qarayi Bata San lokacin data rufe idonta ba tana ambaton "Ya Ilahiy wlh abun da matukar Allah ka agajeni gaskiya idan hakan ta kasance naji kunya". Ta fada tana qara qanqame jikinta. Saida ta Kusan Bata minti talatin tana abu daya sannan ta yunqura da kyar ta tashi,wanka tayi ta shirya cikin English wears yellow irin shaking material din Nan sai sukayi Mata wani irin kyau Karamin mayafi ta rufe gashinta dashi black Mai shara shara ana kallon bakin gashinta Mai santsi da laushi ta cikin gyalen, sama sama ta fesa turarenta ta fito parlourn ba kowa sai kamshin freshner da turaren wuta kawai sai Kuma sanyin A/C daya ratsa ko Ina,cikin takunta na nutsuwa ta doshi kitchen inda take jiyo motsin zilai a cikinsa. Sansanyan kanshi ta ya Fara shiga hancinta zilan kafin ta karasa shigowa. "Masha Allah! Uwar dakina dawisu sarkin ado, Allah ya ba
🏠