n kunyar kallon tsabar idona ki tarewa wani Kato fada Dan nace masa lusari kika Kare min tas har kina fadin na Kama ki na runguma ko kina min kallon Dan duniya ko? humm Ashe ma duka nine lucky din a cikinsu dama na San abin nawa ne Aida saina dama daddawata da moda a lokacin Dan wlh a Ranar sai da na Raina kaina Banda mutum besan gobensa ba Aida saina Yi wandaqata a lokacin" fuskarta ta rufe da tafin hannunta dayan, da gaske so yake ya koya Mata fitsara taga alama shima ba kyalle bane cikakken zani ne. Idonsa ne ya sauka q gurin data cire hijabin.
"wow!! Masha Allah! Koke fa Amma da kin zumbuda hijabi Kamar wata matar liman ai yanzu hirar zatafi Dadin yi ki kawar min da tunani kowa daga zuciyata sai naki, Baki fada min abinda kukayi jiya ba Naga harda spare girki a waje" .
Zaro ido tayi tana dubansa "waye fada maka nunyi wani Abu a gudan?
"Nina gani kinsan nabar idona daya a Nan na taho da daya, ga Kuma Dan gidana magaji shine yayi min voice note ya bani labarin selfishness din da kikayi na kawai su Abba Kika garar arziki ta juma'a Kika ware min iyayena Mata, shi yasa Kika saye zuciyar su Abba da Baba malam kenan,? Kullum maganar daya ce ga amanar yarinyar Nan ka kula da ita Ashe dai tushiyar Baki kike bayarwa".
"Kai wlh ba haka bane ai gani nayi idan na kaiwa Abba Kamar na bawa Ammah ne, haka Baba malam ma ai Iya Abula na bawa koba haka ba"
"Eh kusan Hakan ne amman dai da gyara, Kuma kike wani cewa Abula ko 'yar Karar Nan Babu nifa sunan tsohuwata ne,amma kici gaba da fada wata Rana kunya zakiji idan Kika fada a gabanta tunda bakinki ya Saba fada kinsan dai mu mutanen karkara bama Raina abun fada can zakiji zance ya zagaye cikin kauyen mu ace Mamuda ya auro 'yar birni ko sunan Inna Bata sayawa gatsau take fada".
Kai ta Dade tana tadan turo Baki irin na sakatattun yaran Nan tana fadin "Nifa ban sani ba Ina janta ne tunda sunan kakata ne babar su Ammah zakace min waye waye nima ai Mamana ce ba taka bace Kai kadai yanda kayi kutse a gurin Amma Nima haka zanyi a gurin Mamana harda Hjy Inna".
"Kice nayi celebration ana son da Ammi, inye matar Mahmudun ba, fada min wace addu'ar kike min Dana kasa kallon ko wace mace da sunan so tun bayan kin shigo rayuwata, da dai bana musu da kowa Amma a kanki humm har bore Saida na koya, oya fada min sirrin inji?"
Shiru tayi saboda ji tajeyi kamar zir take a gabansa, Amma ta lura shi ko a jikinsa kamar ma be damu da yanda take din ba.
"Kinyi shiru ko abun sirri ne baza"a fada min ba?"
"To me kake so na fada maka".
"Komai ma, me kike fadawa samarin ki idan sunzo zance? Nima yau zancen nazo Wanda ban samu damar yi ba a baya shine yanzu nike qara'i".
Batasan sanda tayi dariya ba "Au dariya ma na baki ko? Shike nan wlh nifa a kanki na iya zance me yawa da mace ada daga Ammi sai Hjy Inna kawai nake doguwar Hira sadu, nasan duk ranar da Hjy ta ta ganki sai tayi Miki ciwon Baki tace dan kwali yaja hula kinsan meta fada lokacin Dana fada Mata mgnr ki?" Girgiza kai tayi alamar A'a.
"Cewa tayi idan na cika cikakken namiji na shiga duniya na nemoki, Ni kuma nayi wani Alkawari daga ni sai Allah saina bata mamaki wlh".
Kama Baki tayi tana Dan Zuba masa sexy eyes dinta wadan da ke rikita Masa lissafi.
"Kakar taka zaka bawa mamakin duk soyayyar da kake yi Mata kace za'a ganku a rana?".
Kai ya gyada Mata yana gyara kwanciyarsa.
"Yes ai kece mahadin aikin da zanyi na Bata mamakin ko bazaki tayani ba?".
"Ni kuma meya hadani da dabin ku?"
"Kina son sani na fada Miki?"
"Uhm".
Karan doorbell ne ya dakatar dashi daga kokarin bayanin da ze Fara mata.
"My precious Afuwan naji ana bukatar shigowa Bari naje I will call you later, take care by".
Ya tura mata wani hot kiss Yana kashe Mata ido ya sauka daga online din.
********
DAMAGARAM.
Waya ce a kunnenta tana magana cikin tsantsar ladabi kamar tana gaban Mai magabar, cikin ladabi ta Fara fadin "wlh Hajiya ba haka na fada Masa ba cewa nayi kada ya tura kowa Abuja nayi booking din flight ne daga Abuja Zuwa sokoto, tunda Yaya ishaq jirgin Abuja ya yi min booking Kuma nace masa ko nazo sokoto bana son a turo min kowa yanda na fita Ni kadai haka bake bukatar dawowa ni kadai kinji yanda mukayi dashi ai nace masa Zan dawo Amma gani yake kamar gaba zan karayi"
"To ai yanda Kika gindaya Masa dokar ne yake tantamar hucewar taki, kiyi hakuri Zainab anyi Miki ba dai daiba Amma ki zama mai yafiya akan laifin da akayi Miki kema sai Allah ya yafe Miki naki kura kuran, ki Kara godewa Allah kece karama ke Kuma Allah ya daukaki naki Dan fiye da kowa a dangi ki dauka abinda ya faru jarabawarsa ce tazo a haka,Daman Allah swa yace shin bana jarabceku ba? to ki dauka hakan rubutaccen al'amarine daga Allah idan aka daure wata Rana sai labari, shi ba yaro karami bane da za'ace ya bata kawai yayi Mana fushi ne inaji a jikina Yana kusa da dawowa garemu da izinin Allah, ai kawunsa mustapha yace min ba abinda ya tsaya a harkokinsa Dan yana bibiyar lamuransa a yanar gizo yaga komai yana tafiya daidai".
"Nima Ina bibiyar lamarin nasa Haji