NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 96 of 136

i daya ya Baki ci da Sha amma ki Kira Masa aure Shirin film humm zakiyi bayanin film da alama komai normal yake tafiyar Miki ko Aunty zilai?" Dariya tayi "A'a babu ni a cikin wannan maganar kunga tafiya ta". Ta wuce kitchen da plate din abincin ta. " Kinga Sauko kiyi serving din ku, ni ban iya abinda Kika iya ba ku Kenan bakinku ba kintsi ku dunga sakin magana irin haka Ina Dadi Kinga kin Kori Aunty zilai daga wurin". Tasowa tayi ta sauko kusa da zahrar tana fadin "lallai kina Jin Dadi irin wannan garar haka sauko sa'ada Wai Ina Mai gidan na Dan kwana biyu ban ganshi ba?" Plate din ta ture gefe ta dauko tissue tana goge bakinta. "Yayi tafiya jiya baya Nan". Tsayawa mujiba tayi da cin abincin. "Bayanan Kamar ya?" "Kamar yanda na fad'a Miki yaje taron gamayyar Qungiyoyin da suke taimakawa ilimin makarantun government Dana allo a Nigeria da wasu kasashen Africa, to a Nan zone din namu na north east shine aka dauka a Bauchi state, a jigawa da Kano ma duk suna da nasu wakilan tunda state uku suka dauka". "Masha Allah kice wata Rana ku sai turai tunda Mai gida ya Fara irin wannan babbar harka ai ku hannu sama chololo lallai mutuniyar kinzo da goshi". Tsaki tayi wlh ki raba kanki da camfi Wai nazo da goshi to tun kafin nazo yake aikinsa Kuma tafiyar ma dagawa sukayi tun ba labarina a rayuwarsa zasuyi abarsu Nima da abinsa na same shi sai yanzu ne dai ta Kara tasowa. Haka suka dunga Hira har Kusan magariba sannan suka tafi Zahra ta Basu kilishi da biscuits masu yawa. Saida magaji ya Fara Kai sakon Baba Malam sannan ya karasa gida, yauma aikin Ammah ne lokacin daya shiga parlourn ta ba kowa sai Alawiyya tana saka turaren wuta da freshner tambayarta yayi Ina Ammah? Tace Masa taji dakin Abbansu can ya nufa da basket din da ledar knocking tare da sallama a kofar falon Mamace ta amsa Masa ya bude ya shiga da alama wani Abu suke tattaunawa. Gaishe da Abban yayi sannan ya gaishe dasu Ammah Yana aje basket din da ledar Naman da aka kunshe cikin poil paper. "Abba gashi inji Adda Zahra tace a kawo maka". Mama ce ta taso tana fadin"Kai Masha Allah lallai wannan 'yar tana ji da Abbanta". warmers din ta Fara cirowa tana bude miyar falon ya cika da kamshi Curry da spices. "Abban ne yace "magaji sannunka Kaima lallai uwata ta haifu Allah ya yiwa wanna aure Albarka ya tsane idon makiya wlh naji Dadi kwarai da gaske a Miko min nan Naga abinda uwata ta kawo min". Ya fada Yana mik'awa magaji bugun Abuja biyar zuwet. "Na gode Abba, Kuma ta bada an kaiwa Baba Malam ma ya fada Yana nufar kofa. "Masha Allah nasan uwata zatayi abinda yafi haka". Cikin rawar jiki mama ta kinkimi basket din ta Kai gurin da Abban yake zaune ta dora akan coffee table, sannan ta dauko ledar, ledar yace ta bude lafiyyayan dambun naman rago ne yasha kayan Hadi ya sayu jawur dashi sai Kamshi ke tashi, Dina yayi yakai Bakinsa ya tauna Yana fadin "Masha Allah uwata ta Gama min komai wlh har Raina Ina son yarinyar Nan bilhaqqi uba ta daukeni sak duba ki gani Rabi'a ga Asma'u a zaune amma Ni ta yowa wannan garar Kai madallah, Yau abincin ki sai dai yayi hakuri na uwata zanci". Ya fada yana kallon Ammah. 'yar dariya tayi Ammah tana fadin "Ana ta sabon d'a wa yake ta tsohon da inji barmani choge". "Gaskiya kam, ai Babu Mai shafewa Zahra Zane a gurin Abba" Mama ta fada. "Ki Fadi ki Kara Zahra yarinya ce mai tsananin yi min biyayya ki duba yanda lamarin auren Nan ya kasance Amma tunda tayi 'yan koke-kokenta ta hakura ba Wanda ya Kara Jin kanta, duk da mijin nata Mai Karamin karfi ne akan wadanda suka nemi aurenta Allah be nufa ba da Kuna duba da inda ta fito da Kuma uwa uba dangin mahaifiyar ta Amma tayi zaman ta Ni kuwa ba abinda bazan yi Mata ba matukar baifi karfin arzikina ba". "Wannan gaskiya ne duba da yanda ta waye tayi karatu Mai zurfi ai ba wata ce bijirewa zatayi ayi ta Kai ruwa Rana" Mama ta fada. Yar dariya kawai Ammah tayi duk Dadi ya cikata Bata taba tunanin Zahra nada wayo haka ba tasan dai abun duniya Bai rufe Mata ido ba. ✨✨✨ ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI ✨✨✨ ✨✨✨ Maman Fateemah. Page 32 _______Qaran alarm din daya saita ne ya tashe Shi sallar Asuba, duk da bai kwanta da wuri ba Dan sai Kusan karfe biyu na dare suka shigo gidan, meeting din nasu sun jima suna tattaunawa akan sabon kafanin da zasu bude a jihar kebbi na shinkafa, masallacin da suke sallah da gidansu akwai tazara sosai shiyasa ya saita kafin sallar Asuba da kamar hour daya, sai da yayi yaqi da Shaidan sannan ya samu ya sauko daga gado Bai jima a toilet ba ya fito sanye da bathrobe Fara tas Mai jikin towel. Jallabiya ya saka yayi raka'atanul fajri sannan yayi waje a Yana niyyar yiwa Sameer knocking ya bude ya fito. "Barka da Asuba" Sameer ya fada yana mikiwa Mahmud hannu sukayi musabaha, "Ashe ka tashi ai nayi tunanin saina shafa maka ruwa sannan ka mitsa". 'yar dariya Sameer yayi Yana fadin "irinku da kuka San inda kuka dosa Kuna dagewa da mujahada to mu ta Yaya zamuy
🏠