NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 94 of 136

da sanyin tayis Bai Kama ki ba, tunda Naga gidan naku ko Ina sanyi Kamar gidajen larabawa". Sai Kuma ta rufe bakinta da hannu. "Kin jini ba wlh na manta Ashe gidan nasu ne". Dariya Zahra tayi "Kayya Ina wani balarabiya anan ai da uba ake ado Ni bafulatana ce kalarce dai na dauko tasu Amma idan masu abun suna yarawa wani abun sai kallo Dan ma Allah ya hadani da jarimin uba da yayi tsayin daka gurin ganin na iya yaren saboda na samu saukin mu'amala da dangin Mamana". "Wannan gaskiya ne Allah ya sakawa Alhaji da Alkhairi ya biya Masa bukatunsa na Alkhairi" "Allahumma Amin". Zahra ta fada. "Me za'a dafa miki? Mu dai nayi Mana nida bakon ku". "Wai bakon mu wato dai bazaki ce Mai gadin ba ko?. Dariya tayi. "Wlh baya Kama da masu gadi Kinga kuwa ai bana ce Masa ba". "Haka ne ki dafa min indo mie da cooker oat kawai". "To an gama sai kin fito". Ta fada tana juyawa zuwa main parlour din yayin da Zahra ta koma ciki. ************* DAMAGARAM NIGER REPUBLIC. Cikin takun ta na nutsatstsiya kuma wayayyar mace 'yar gayu ajin karshe ta shigo parlourn tana sanye da doguwar rigar madam gezber kalar peach sai gyalen kalar light yellow touching din flowers din dake jikin kayan sai takalmi plat Mai azabar kyau shima light yellow din tun kafin ta karaso kamshinta ya hade gurin. A hankali ya dago ya dubeta har ta karaso gurinsa, tattara aikin da yake yayi ya Maida hankali a kanta lokacin da take Zama a kujerar dake gefen da yake. "Sannu da aiki Yaya barka da Asuba". Ta fada tana sadda kanta kasa Bai amsa ba Jin shirun yayi yawa yasa ta dago kanta ta dube shi, ita yake kallo. "Yanzu abinda Kika zaba kenan Zainab da girmanki da hankalinki ki zazzage jiki ki baro dakin mijinki kizo ki nemi guri ki zauna mijinki yayi rarrashin duniyar Nan kinqi ki saurare shi daga karshen ma Kika zabi ki dawo Nan Damagaram saboda a Yamai uncle Yousoufu ya nuna Miki rashin kyautatawar abinda kikayi shine kikayo yajin Nan ko?.Ni tunda tubus ne Bari kizo ki zauna ki Mike kafa gashi nan har an Fara kawo Miki caffar ana son aurenki idan kin Gama idda wannan arzikin ki ne?". Ya fada Yana kureta da ido, da sauri ta cira Kai ta dube shi. "Ni Kuma Yaya ake jawo min zawarci kawai daga ganin mace sai ace zawara ce". "Kada kiga laifinsu sun ganki yau sun ganki gobe Baki da niyyar tafiya,idan Badi'a zata fita ki wanke jiki ku kama tafiya ba dole ace Miki haka ba". Idonta taf da hawaye ta dube shi "to Yaya ya akeso nayi kasan dai yanda abun Nan ya kasance duk yanda naso a saurareni idanuwa suka rufe ba Wanda ya kula da abinda nakeso su gane Saida suka rabani da Dana yabar gida cikin bacin Rai Wanda har gobe ba Wanda yasan inda yake, gaskiya Kuma tayi halinta yanzu za'a matsamin da zarya na fada musu niba yaji nayi ba duk ranar da yarona ya dawo Zan dawo". "Zainab a gabana kike fadar danki, Dan farin ba zakiyi min Kara ba". "Kayi hakuri Yaya na Bari d'anka to" ta fada. 'yar dariya yayi na nawa Kuma sai dai a koki gaba, yanzu Dan Allah Alfarma zakiyi min kiyi hakuri ki koma dakinki Suma sauran yaran suna bukatarki kusa dasu ko badan Babansu ba ki duba girman Hajiya Inna har Yamai Saida tasa aka kaita ko a jirgine dai ai tanayi dake ne amma Kika kasheta da dadin Baki akan kina tafe kikayi zaman ki karshe ma kikayo hijira daga can, duk laifin Hajja ne wlh ita an taba Mata dan 'yar so ba zaman lfy, gobe nace aje Abuja a daukeki tunda ba jirgin sokoto direct, kije kiyi ta yi masa addu'a bakin uwa Mai Albarka ne akan 'ya'yan ta muma muna tayaki nasan fushi yayi idan ya huce ze nemi gida". Har ranta bataso wannan hukuncin ba Amma yata iya da Yaya ishaq uba ne sak tun bayan rasuwar mahaifinsu bai barsu da kukan maraici ba, duk rintsi baya Bari su koka uwa uba yanda ya janyo gudan jininta ya nuna Masa hanyar nema tun a kananun shekaru duk abinda yaronta ya zama shine sila gashi Zuwa yanzu Allah yayi Masa karfin daya fi na Yayan. Hira sukaci gaba har Aunty Badi'a ta fito itama kamar me Zuwa gasar sarauniyar kyau ita Fara ce tas buzuwa kallonta Yaya ishaq din yayi "wato ta wata fuskar naji dadin zuwanki Zainab ko banza mutuniyar ta koyi gayu irin naki da dai sai a hankali". "Kai Yaya wlh bani na koya Mata gayu ba Daman Aunty na me class ce ko Aunty?". "Fada Masa dai,kawai nasan dai na koyi amfani da perfumes designers dani kowa ne ma saye nake Amma yanzu tunda ta bani naji dadinsu nake amfani dasu". Dariya yayin Yana fadin . "Ba cinya ba Wai 'yan magana sukace kafar baya, Wai yanzu Ina da kikace min zakuje? Bana son yawo har an Fara min sallama idan ta Gama idda". Ido Aunty Badi'a ta kwalalo "sallama Kuma?. "Wlh kuwa shi yasa nace ta tattara tayi hakuri zanyi Mata booking ta tafi kawai muci gaba da addu'ar Allah ya bayyana shi duk inda yake". "Gaskiya kam shi yasa kenan ranar da mukaje gidan sarki kingmakers sun fito daga meeting da Mai martaba Naga ana nuna ta har wani dogari Yana kokarin Zuwa gurin mu muka tafi". "Kinsan kuwa sakon daga fada yake". Baki Ammi ta rike "tab gara nasan inda dare yayi min kafin wannan labarin ya Isa k
🏠