NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 93 of 136

ra taji kuka yazo Mata, Nan da Nan Ummeen ta rude tana tambayar ta ko tana da damuwa ne ta fada Mata cikin kukan tace "Ummee Shima fa wannan daga kawo ni gidansa ko sati daya ban rufa ba ya tafi ya barni Wai aiki zejeyi uk" shiru Ummee tayi kafin ta shiga rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali da nuna Mata ba lallai ne hasashenta ya kasance gaskiya ba, kada ta damu saboda ita har Umara tayi bayan auren tayi mata addu'oin samun nasara akan dukkan lamuranta, sannan ta yi mata fadan ta kiyayi yawan kukan Nan bashi da ma"ana, daga karshe tayi Mata albishir zawan su next week harda Mama Hanifa da Aunty Nawwara duk suna hanya Daman ko Bata sameta a waya ba zata kira Hajiya Asma'u tasa a fada Mata. Murna ta shigayi Kamar tayi me har Ummee na Mata dariya Nan da Nan ta ware ta shiga lissafo abinda takeso Wanda za"a taho Mata dashi. Bayan maga wayarsu da Ummeen Ammah ta Kara kira lokacin tana tare da Abba. Tana zubawa Abba Dan fruit salad wayar ta dauki ringing Abban ne ya dauko ya duba 'yar dariya yayi Yana mikawa Ammar wayar tare da fadin. "Uwata ce ke kira". Ganin Kiran ze yanke yasa Abban karbar fruit salad din yaci gaba da zubawa Yana fadin "A dauki Kiran uwata kada ya yanke". Daukar tayi tana amsa sallamarta da gaisuwar da take mata. "Ammah yanzu Dan Allah bazakizo ba Kuma Aunty Hasana ma fa batazo ba fa Kuma Ni sonake na ganki". "Ikon Allah yanzu ke saboda Allah sai a ganni a gidanki a irin wannan kwanakin ai sai a dauka ba lafiya Auntyn taku dai zatazo Daman jiya take fad'a zata shigo ta ganki tunda mijin naki baya Nan, ai Mahmud din ma ya turowa Abban ku da sako ba dadewa ta whatapp yace sun sauka lafiya, ke dai abinda nakeso ki kwantar da kiyi Masa biyyayya kinji". Ta fad'a tana rarrashinta. "To Ammah, daman kira nayi na fada Miki Ummee tace next week zasu shigo Nigeria nasan zata fada Miki". "To Allah ya kaimu Daman munyi maganar shekaran jiya har take tambayar meya faru da taki wayar? Nace ta Dan samu matsala ne, ga Abbanku yace a gaishe ki" "Lah! Ammah Daman yana Nan amma ba'a fada min ba Bashi na gaishe shi" Sun gaisa da Abban har Yana Dan tsokanar ta, tunda a wani bangaren kakace a gurinsa, Nan yake fada Mata mijinta yace ya tafi da motarta Kano tana airport Dan haka daga nan Zuwa jibi za'a kawo Mata daya motar ta gurin Muttaka, godiya ta yiwa Abban sannan sukayi sallama. Ta jima Bata aje wayar ba, tana juya maganarsu da Ammah Wai ya fadawa Abba sun sauka wato ita da bayaso Bata da matsayin da ze kirata ko sako ya fada Mata sun sauka, kenan Daman duk abinda yake Mata a 'yan kwanakin Nan yaudara ce Dan ya lasa Mata Zuma a baki ya gudu ya barta da kewarsa inda ta godewa Allah be lalata mata rayuwa ta gudu ya barta ba wlh duk rintsi sai ta bar Kasar Nan ta koma Jordan, Dan tasan Allah kadai yasan halin da Ammah zata shiga idan bawan Allahn Nan yaqi dawowa.... ✨✨✨ ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI. ✨✨✨ ✨✨✨ Story & Written by Naman Fateemah. page 31 ______________Har aka Fara Kiran sallar insha'i tana zaune tana faman tunanin makomarta, tashi tayi tayi sallah, nan Kan sallayar ta kwanta tana lazimi a haka har barci yayi awon gaba da ita. Tun zilai na saka ran fitowa Zahra har ta hakura ta shige ciki duk da ba barci take ji ba, tun yamma take ganin zahrar wani sukuku Kamar marar lfy. Zahra ba ita ta farka ba sai Kusan daya da kwata, tashi tayi tana mik'a tare da salatin Annabi, duk jikinta ciwo yake Mata hijabin ta cire tare da after dress din ya Zama daga ita sai vest da wandon toilet ta shiga Bata Dade ba ta fito canja kayan jikinta tayi da rigar barci ta Kashe wutar Mai haske ta kunna bed side camp tayi shiru tana istigifari ga Allah s.w.a da Salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama duk yanda tunani yaso ya bijiro Mata saida ta kawar dashi kawai ta fawwalawa Allah lamarinta tasan duk rintsi Yana tare da ita, a haka har barci yaci karfinta. Da safe har zulai ta Gama share share da mofin Zahra bata fito ba ganin shirun tayi yawa yasa tayi tunanin buga Mata kofa kada ta Zama babbar banza zuwanta ya Zama marar amfani rabonta da yarinyar nan tun magaribar jiya Bata Kara sakata a idonta ba, kofar bedroom din ta nufa tayi knocking taji shiru lokacin Zahra na Wanka, Kara bugawa tayi still dai shiru taji Nan da Nan hankalinta ya tashi kada fa wani abu ya Sami yarinyar Nan ta shiga uku. Tana Nan tana shawarwarin ta bude ta gani ko lafiya? taji alamun motsin tafiya daga ciki da sauri ta Kara knocking din, Zahra da towel a jikinta ta nufo kofar ta bude. "A'a Aunty zilai kece? Ina kwana?" Ta fada tana goge gashinta daya jike gurin wanka. "Lafiya kalau, naji ki shiru ne tun daga shiga sallah jiya harna gaji da zama Baki fito ba, gashi yanzu ma naji shiru har Ina kokarin Kiran Ammah na sani koba lfy ba". Ta fada tana kokarin barin gurin "na gode da kulawar ki Aunty zilai wlh jiya barci ne ya daukeni a nan Kan sallaya bani na farka ba sai Kusan karfe biyu na dare". "Ikon Allah kice kwanan kasa kikayi
🏠