NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 92 of 136

fada tana cire hijabinta daga jikinta vest ce Fara Kal sai wando shima fari ai pink din kananun flowers gashin tayi parking a tsakiyar Kan ta kashe da band shima pink, sai fito baby sak. Gyara kwanciya tayi, tayi ringinnine da wayar a kunnenta Hira sukaci gaba da sajida yawanci duk akan auren zahrar ne. Sun dauki lokaci Mai Dan tsawo suna tattaunawa akan bututuwa da dama kafin suyi sallama, ta nufi toilet wanka take son yi kafin ta fita cin abinci. ******** Jirginsu Mahmud a Addis Ababa Bole international airport yayi landing, daki biyu Sameer ya kama musu Nan kusa da airport din tunda a kalla zasuyi Kusan three hours. Saida ya kaiwa Mahmud jakar laptop dinsa sannan ya nufi nasa dakin, bayan fitar Sameer Mahmud wanka yayi sannan yayi sallah maimakon ya kwanta ya Dan huta sai kawai ya bude wayarsa so yake ya ganta duk wani matsi da yayi tana manne da zuciyarsa so yake ya ganta kafin ya kirata. CCTV ya shiga ta wayarsa duk abinda akeyi ya rinka bi Yana gani yasha dariyar karon Zayyan da wannan matar wadda ko sunanta Bai sani ba, shi yasa ya dauko shi yasan shi kadai ne cikin amuntattunsa Wanda ze Masa wanna aikin ba tare da an samu matsala ba. Saida ya gama kallon ko ina na gidan yaga ba wata matsala, sannan yayi zooming din cikin bed room dinta daga ita sai vest purple da wando skintight kanta tayi parking da purple din band sai tayi wani irin kyau na musamman, kura Mata ido yayi Kamar ya warto ta yakeji, turare ta dauko tana fesawa a jikinta. Nan ya shiriri ce Yana kallonta knocking din da akayi Masa ya katse Masa abinda yakeyi, umarni ya bada a shigo Sameer ne sai ma'aikaciyar hotel din dauke da tray na abinci sai karairaya take shi har dariya abin nata ya bashi, me Kamar zahra yaushe irin wadannan zasu burge shi, bayan ta wuce ne ya dago ya dubi Sameer "kada ka qara zuwar min da irin wannan a rinqa bawa maza suna kawo min kawai". "Noted sir" Ledar dake hannunsa ya Mika Masa Mai tambarin wani boutique ne, sannan ya aje Laptop dinsa a kusa dashi Yana nuna masa wasu ayyukan da ya Gama yanzu, sun jima suna aikin kafin sameer ya fita saboda lokacin tashinsu ya kusa cika shi kuma Mahmud ya ciro kayan da nufin sakawa. Saida Zahra ta Gama feffesa turarenta sannan ta dauko after dress ta zura ta yane kanta da gyalen sannan ta nufo parlour, zalai ta samu tana 'yan goge goge duk da ba wani datti a gurin, gaishe da zilan tayi tana Mata sannu, ajiye mofar tayi "Allah ya taimaki uwar dakina ga abincin can nayi Miki abinda kikeso faten dankalin turawa da pepper soup din kifi" Zama Zahra tayi tana fadin "Kai Amma wlh na gode kwarai da gaske shi yasa nake yinki kinsa favorite Dina wlh". "Ai shi yasa na cewa Ammah kada a wani dauko yarinya tun daga Mubi Nima na isa na zauna dake saina kirawo Kanwata Alawiyya ta cigaba da yiwa Ammar kafin Allah yasa yallaban ya dawo, ai ni har zaman wanka ni zanyi Miki Koda kuwa bakwa garin Nan ne". Dan smile tayi kawai bata ce komai ba saima ta canza akalar zancen. "Ni Kuma Aunty zilai kin mikawa mutumin Nan abinci kuwa?". "Ai tunda na Gama na zuba na hada harda ruwa da lemo na mika Masa. Naga Dan gayu ne beyi kalar masu gadi ba". Dariya zahra tayi tana fadin "Aunty zilai kenan shi Mai gadi har Kama gareshi". Yana da kama Mana Wai Kinga wannan din?" Na ga wani dai dazu ban sani ko shine Wanda aka Kira jiya cikin dare". " Cikin dare Kuma?" Kai ta gyada "Mata kusan Hakan tunda Sha biyu ta wuce ya kirawo wani kawai umarni ya bashi yazo garin Nan da safe kinsan bakwai a Nan tayi mass nifa mutumin Nan wlh tsoro yake bani na kasa gane kansa". Dan murmushi zilan tayi tana kallon Zahra "kiyi hakuri uwar dakina a hankali Zaki San komai a kansa badai Kuna tare ba da sannu Zaki gane shi din waye, kici abincin sai muci gaba da hirar idan kin gwma". Bata k'i Shawarar zilan ba ta tashi ta nufi dining ita Kuma zilan ta nufi dauko Mata ruwa da mutuniyarta farm fresh, sai da ta Gama cin abincin sannan ta dawo parlourn gurin da tabar Aunty zilan sukaci gaba da hirar su, amma Kusan hankalin Zahra yana Kan Mahmud haka Nan sai taji ya fado Mata ta yarda da ake cewa sabo turken Wawa, yanzu da baya Nan sai taji duk kewarsa ta kamata, tun dazu take duba waya ko zataga kiransa Amma shiru tasan tsakanin Nigeria da inda zasu indai da gaske chinan zasu da nisa a kalla jirgin zeyi landing a Ethiopia da India yaci ace ya kirata Amma shiru har Yanzu ko lfy? ta ayyana a cikin zuciyar ta. Ganin tunanin Zahra yayi zurfi yasa zilan ta tashi tana fadin Bari nayi wanke wanke tunda kin Gama da kwanukan" Tayi hanyar kitchen, ita kuma ganin tunanin ze dameta yasa ta kunna tv ta kamo MBC MAX tana son finafinan su sosai,Aunty zilan ma data Gama Zama tayi sukaci gaba da hirar jefi jefi har aka Kira magariba suka shiga sallah. Tana addu'oin yaumiyya na cikin du'aul mustajaba ne kira ya shigo wayarta da sauri ta dauko tana duba Mai Kiran Ummee ta gani da sauri ta daga tana fadin "Ummeena" Amsawa tayi suka gaisa Ummeen ke fadar an fada Mata ta kirane nan tayi Mata fadan rufe layi da tayi,nan Zah
🏠