NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 91 of 136

i shiga Bismillah tsuntsu daga sama gasashshe, Dan muna da kudajen da basa haram akan duk Mai tsautsayi, idan na Kara ganin giccinki a wurin Nan saina hadaki da karena yayi min fata-fata dake, wuceeee min daga nan" yayo kanta,da gudu ta kwasa ko waiwaye babu. "Stupid! Da gani wannan tsohuwar kwarkwar ce wlh Banda oga ya hana da kinci na jaki banza wato kin samu oga a araha shine kuka Neman zaku masa shegantaka akan matarsa ni na rasa yanda akayi ma oga ya Fado garin Nan,? Kuma har ya iya Zama a haka ba wani damuwa, ko Dan meze dameshi Yana tare da wannan danyan gold din". Ya fada Yana komawa bakin aikinsa Amma zuciyarsa fal tunanin abinda ogan nasa ya sani game da wannan matan daya turo Masa hutunan su ya Kuma shata musu dogon layi. Asabe Bata samu zarafin tsayawa ba Saida ta dangana da wani gurin me suyar kifi a bakin titi shima gani tayi gurin da jama'a ko cimmata yayi za'a ceceta, gefe ta koma tana mayar da numfashi sai lokacin ta dubi hanyar data fito ko Mai Kama dashi Babu. Gefen wani dutse ta zauna tana tunanin to koba gidan da sukaje jiyan bane tunda ba wannan basamuden suka tarar ba Amma daga Daren jiya Zuwa yau har lamarin ya canza ita damuwarta daya shin sakon da suka bayar ya sameta ko kuma na jiyan ba shine asalin Mai gadin ba yayi musu ta 'yan duniya ya barbe kayan da kudin ya wuce nasa gurin. Tashi tayi Kamar wadda aka tsikara ta dauki 'yar ledar data sawowa Mai gadin Dan abun tohiyyar Baki sai Kuma labarin ya canza salo. Harta dauko wayar ta Sai ta mayar idan tayi gigin fadawa Mama kwabarta zatayi ruwa Dan a yauma Saida Mana ta karo kudi masu nauyi tace a bawa Mai gadin yanda duk abinda za'a saka shi yaji baze iya gardama ba, to idan ta koma Mata da wannan labarin amshe kudin zatayi tasan halinta kayan ta, data Bata naira dubu gara ta bawa Dan tsubbu dubu hamsin, Sam Bata karuwa da ita saita wadannan hanyoyin idan ta aiketa tunda itace amintacciyarta ta Nan takeyin nata duk rintsi bazata so ta rasa wannan mafakar ba Dan Kusan da ita ta dogara gurin kwaramniyar yau da Kullum nata. ******* Saida Zahra tayi barci Mai isarta sannan ta farka lokacin biyu har da minti ashirin da hudu, da sauri ta Mike tana addu'ar tashi daga barci tayi mamaki ita fa gani tayi kamar barcin minti goma Sha biyar tayi Ashe lokacin ya ja haka, alwala tayi tazo ta Fara sallah bayan ta idar wayar ta da dauko Ummee ta Kira cikin shauki tun dazu ta nemeta network din na garin ba kyau sai hakura tayi, Bata jima ba tana ringing aka daga ba Ummeen bace wata ce ta daga tana ta yi Mata larabcin gargal ita kuwa zahrar na language yafi kwarewa a Dan daburce tayi Mata bayini ta gane Ummeen ta fita masallacin Annabi sallah tunda har lokacin suna Madina basu tafi ba Kuma a yanda sukayi daga Saudi Arabia Nigeria zasuyo gurinta, sallama tayi wa matar ta kashe. Number sajida ta lalubo ta syprus tasan zata Sha mita tun ranar da sukayi ways da wayar Amatu tayi Mata buyagi ta kashe Basu Kara waya ba, har tayi ringing ta katse Bata dauka ba, Bata hakura ba wani Kiran ta karayi shima Yana daf da ze katse aka daga. "Haba bestie Ina ta kira kin shareni ko har yanzu fishin ne?" Mai makon taji bestien sai muryar Fatima taji tana kwallawa Sajidar kira tana fadin "ku taho ga Amarya Zahra! Zahra" ta kirata da karfi tana murna kamar zata tsaga wayar, daya bayan daya suka dunga gaisawa suna ta korafin amarci Dadi ta Kama waya ta rufe wato Bata so a shigar musu rayuwa ko? Hakuri ta Basu tare da fada musu tayi missing din waccen wayar ne har sim din, sai daga karshe sajida ta karbi wayar. "'yar duniya wato kinji dadin lamarin ko Kika wani shareni, ni yanzu ai yallabai Mahmud ya fiki kirki kinsan ya kirani Kusan sau uku? Daman ko Baki kirani ba Zan kiraki dazu wurin Sha daya ya kirani Wai na kiraki na lallasheki yayi tafiya ya baroki kina kuka?". Ya fada tana kunshe dariyar ta. "Malama ki fito kiyi dariyar ki sosai kada ta kume Miki a ciki,da kike wani kunsheta". Dariyar tayi da gasken sai tayi Mai isarta tace. "Dan Allah bestie mekika bawa wannan guy din Kinga yanda yayi masifar macewa a Kanki? Wlh har tausayi yake bani Ni har mamaki nake idan ya kirani Yana min maganarki ranar Nan fa cewa yayi na bashi labarin zamanki a Nan syprus din wlh nayi zaton da Wasa yaki tunda nasan ba Karamin cajin kudi za'ayi ba. Amma haka na ware na rinka bashi labarin har na Gama ko a jikinsa, yanzu Ina aka tsaya da fatan komai ya dai daita? Dan nafi son dai dai lokacin ganawarmu muyi murna biyu graduation da naming ceremony". "Wlh Zan kashe yaushe Kika zama haka Mai bin kwakwkwafin jama'a? to bazakiji ba an fada Miki kowa ma irinki ne ai wlh ya Abdul Hakeem ya debo ruwan dafa kansa Dan nasan Dan bawan Allah saiya rinqa guduwa daga gidan" Wata irin dariya ta saki tana fadin "billahil Azeem gara wata wainar data wake yarinya gyara zancen ki idan ana cin baure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana sallah ba'a magana". "Wlh sharri zakiyi Masa Amma shi dai salihi ne". "A inda salihai sukayi karanci ba". "Mubar zance kawai tunda abun ya Zama haka". Zahra ta
🏠