NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 9 of 136

nufi tun jiya yake tuhumarsa aka zuwa da abokinsa da yayi duk da ya nuna Masa wannan ba wata matsala bace Amma har yanzu Yana hukunta shida idanunsa. Masha Allah dubban mutane ne suka shaida daurin Auren FATIMAH ZAHRA AHMAD SANI da Angonta MAHMUD MUHAMMAD DANGE akan sadaki dubu dari uku lakadan ba ajalan ba. Daurin aure daya bawa dubun mutane mamaki bare wadanda sukazo daga bangaren Mushahu sunyi mamaki kwarai sunan Amarya dai shine Amma ba mijin daya gayyato su bane yayin da yan unguwa ya Zama abin kasawa a faifai ana yawo dashi, da yawa na ganin beken Alhaji Jafar na aurawa bakon da ba'asan asalinsa ba yarinya kamar Zahra yayin da wasu ke fadar ai Dan ba 'yarsa bace shi yasa yayin wannan danyan aikin. ....... 💋❤️AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️ Page four🔷 ___________''📖🖋️ Wata marokiya ce irin dattawan Nan da suke bin manyan marok'a ta biyo tawagar masu dawowa zuwa gida kasancewar gidan ba nisa daga masallacin juma'ar, itace ta rangad'a guda har sau uku ta Kara da fadin "Alkawarin Allah ya tabbata an daura auren Fatima Zahara'u da zukeken Angonta Mahmud Ubangiji Allah ya bada zaman lafiya da kazantar daki Bata shara ba, munzo much arziki mubar arziki a gurinsa. Kamar saukar aradu haka maganar ta shiga kunnen Hajiya mama, batasan lokacin data tsallake mutanen falonta ta fito ba dankwalinta a hannu, tana fadin "me naji ana fad'a wa aka daurawa aure da Mahmud naji kowa". "Eh haka ne Kam Alkawarin Allah ya ciki Zahara'u ta Zama matar Mahamuda" Ta debo wata gudar ta Kara rabsawa. Dai dai lokacin Hajiya kaltume aminiyar Ammah ta fito ta dukulawa wannan marokiyar kudi sannan ta Mika Mata babbar leda Mai abincin biki har da ruwa da lemo. Cikin rashin nutsuwa Hajiya mama ta nufi dakin Amma ko sallama Babu ta Fara fadar "Hajiya kinji abinda naji ko kunnena ne ya jiyo min ba dai dai ba?". Kallonta duk 'yan dakin suke kafin Ammar tace Mata "nima haka naji kamar yanda kikaji sai dai ko shirme takeyi ita Mai rokon tunda ba sanin su tayi ba". "Eh gaskiya Kam sai dai hakan". Ta juya ta koma daki. Bata zauna a falon ba uwar daki ta wuce, Asabe ce ta rufa Mata baya, a tsaye ta sameta ta Goya hannu a baya tana Dan Kai kawo a tsakanin gado da madubi. Waiwayowa tayi tana kallon Asaben kafin ta zauna a bakin gado, kusa da ita Asaben itama ta zauna. Tana fadar "Haba Hajiya Dan Allah ki nutsu bana son ki bada wata baraka a sabgar Nan keda na fad'a Miki Daman malam na BANDE yace wannan karon aure sai anyi Amma ba da Mushahun ba, Amma abinda yake daure min Kai malam na banden yace Wanda zata aura a nesa yake Kuma yaga haske so sai akan lamarin duk yanda yaso ya Bata lamarin abin Bai yuwu ba shine nace kawai a kyale tunda dai Wanda muke son a fasa da shin din aikin ya yuwu, nasan dai da wuya ta Sami irin Wanda ta rasa a bay". "Haka ne Amma abin dubawar waye wannan din sanan me yasa aka kudundune zance? Wai fa Dan munafurci Hajiya Asma'u cewa tayi Bata Sani ba ke kin yarda Alhaji ze aurar da Zahra Bata da masaniya, ko meye ma dai kyawaun ya kare a auren Hadi tunda nasan ba wani sai Mushahun shi Kuma ya Kara gaba kamar sauran". Ta fad'a tana kwafa, mikewa tayi tana gafar "Bari na fita sai Naga kul uwar daka". "Allah ya taimaki uwar dakina, aikinki Yana kyau". Asabe ta fad'a tana mikewa itama. ********** Daga gurin daurin aure Kai tsaye gidan gonar Alhaji Jafar suka wuce har tawagar angon bisa umarnin Alhajin tun safe ya turo Mai sunasa (magaji) yaje ya fadawa Baba malam. Anci an Sha kamar ba gobe mutane sunyi mamakin irin wannan karamar arzikin dan duk zarin mutum sai dai yaci ya Bari ruwa da lemo kuwa kamar banza. Abokan Mahmud kuwa sai Dan biki suke Masa. A gidan malam ma Masha Allah anci an Sha Yara sun san ana biki a gidansu, Iya Abu ma tayi nata taron komai baja baja makotanta ma sunsan ana hidimar arzki a gidan Kuma Suma sunzo Mata harda masu riko abin arzikinsu su kawo Mata. ******** A guje Faruq ya Fado falon Aunty Hasana,danta ne na uku Yana rungume da babbar rigarsa ta daurin aure daya saka Yana Fadi "Aunty Zahra wallahi Naga mijinki ba wannan Uncle din bane na kano wallahi wanna yafi shi kyau Baki gani ba yanda yake rabawa marok'a kudi ba, Kuma Dan gayu ne sosai Naga Uncle Abdul Hakeem ma ya rugume shi Yana ta dariya, Dana tambayi Auncle Imam yace min sunansa uncle Mahmud". Tunda ya shigo Yana karadin Nan ta zuba masa Ido tana sauraren abinda yake fad'a, kana ganinsa kasan har zuciyarsa abinda yake fad'a din gaskiya ne, wani irin gingirin taji kanta yayi mata, nan ta sulale ta kwanta kan kujerar ta saka hannunta ta rufe fuskarta wasu hawaye na zubo Mata masu zafi. Sajida da Amatu suka nufi gurin Faruq din suna neman Karin bayani. Yayin da wasu da yawa suke ta sabgar ciye ciyensu Dan Suma Kam an kawo koma enough. Kamar yanda ya fad'a haka Suma ya mayar musu Dan su harda Karin bayanin yayi musu kasancewarsa Mai surutun tsiya. A hankali Sajida ta kamo hannun Zahra Dan Bata fatan wani daga cikin bakinsu su fuskanci an samu matsala gaskiya, kamar masu
🏠