NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 87 of 136

Hygiene inda nayi service na ringa yin lectures ko sau biyu ne a sati". Wani kallo yayi Mata na Amma Baki da lissafi. "Ni matata da yawon aiki? Gaskiya A'a! Wannan bukatar Bata karbu ba, me kikeci na baka na Zuba indai aiki ne wlh sai kin gaji da yinsa, tashi daga jikina kin wani samu cinya kin dane,kada na makara nayi missing flight mu tsuguna duk dan burin bawa ya rushe". "Yanzu Allah bazaka Bari na rinka Zuwa ba". Ta fada a marairaice. "Kinsan Allah wlh Zan hadaki da zayyan Dan nasan Yana daf da shigowa garin Nan ya juya min dake can kauye gurin Hajiya Inna ko banza kin tuka mata tuwon dawa kin mata shara, kinga ita gaba ta kaita balarabiya na mata aikatau ita kuwa bakar fata Kinga sai mu Dora a media muma 9ja munci gaba ana zuwa daga middle East ana Mana aikatau". Ya karasa fada Yana Jan Dan tsinin Karan hancinta. Tana kokarin magana wayarsa dake Kan bedside ta dauki wani kidan larabawa Mai dadi. "Dauko min wayata Dan tsabar na Zama mijin ......, Gashi Nan ringtone din ma kidan kune na saka". Wayar ta dauko, Zayyan ta gani kwalalo idanu tayi Ashe da gaske yake da yace Shi wannan din zezo yanzu ko waye shi kuma "oho" ta fada a zuciyarta. Wayar ta Mika masa. "Ka karaso?" Abinda taji ya fada kenan Bata San me yace Masa ba taji yace "ok, ka shigo ciki akwai securities a kofa zasu zasu rakoka gurin da Zan ganka". Ya kashe Kiran Yana nufar kofa, ki shirya kafin na dawo yanzu zamu wuce". Yayi Gaga abinsa ya barta da Baki a sake "ikon Allah shi Kuma ko waye yake bada umarni cikin dare ya wayi gari da abinda ya bukata tasan ko waye daga nesa yake Dan jiya tanaji Yana fadin kada a biyo ta jos a biyo ta kano, ita duk ya Gama Dame Mata lissafi wlh. ****** A hankali yake tafiyar cikin nutsuwa Amma da gani kasan tafiyar ta ingarman namiji ce, tunda ya doso gurin Zayyan ya kafe shi da ido, take ya shiga jinjina lamarin ogan nasa wato ana zaton wuta a maqera said gata a masaqa, waze tab'a tunanin sa a irin nan yayi masifar bada kafa. Bai Farga ya kureshi da ido ba Saida yazo daf dashi, "sorry sir" ya fada Yana sadda kai, baiyi magana ba ya mika Masa hannu wannan d'abi'ar sa ce baka Masa irin gaisawar Nan sai dai kuyi musabihwa. "Barka da Asuba ya Hanya?". "Alhamdulillahi." Ya fada sai da Mahmud ya zauna kafin Zayyan Shima ya koma ya zauna. Kamar bazece komai ba gurin ya dauki shiru. Saida yaja fasali sannan yace. "I hope ba Wanda ka fadawa munyi waya ga Kuma inda zaka sameni?" Kai ya girgaiza "ko daya oga ba Wanda yasan inda na tafi kawai nace musu zanje gida ne na samu Kiran gaggawa". "Good, na kiraka ne zaka zauna gidan da wife Dina take zanyi tafiya, Wanda na saka gadin Naga alamar gaskiya Bata isheshi ba, ko Kuma ze iya komai saboda kudi, zan turo maka pictures na wasu Mata koda Wasa kada kabar kafarsu ta shigar min gida shi yasa na taso ka da tsohon dare ". Zayyan jin magwnar yayi wani banbarakwai "wife Kuma? To ta ina Hakan ta faru? mutumin da ake tunanin baya kasa sai Kuma ya ganshi a nan Yana wata irin rayuwa hankalinsa kwance, ga abubuwan tambaya Amma ba Halin yinta. "To in Sha Allah baza'a samu matsala ba". "Yanzu zaka shiga cikin Ibrahim ze nuna maka dakin da zaka huta daga Nan zuwa sha daya Binyaminu ze shigo kuje gidan". Ya fada Yana mikewa. Da kallo zayyan ya bishi har ya b'acewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke Yana jinjina Lamarin ogan nasu wato duk yanda kasan Shi idan yayi wata bada Qafar saika rasa gane wace alkiblar ya kalla. "Wife Dina". Yanda yayi maganar kasan ba wasa cikin Yana wannan tunanin Ibrahim ya karaso Bai sani ba. Da azama ya shiga falon a zaune ya sameta da luggage dinsa a kusa da ita tayi rolling da Veil din rigar sai tayi masa wani irin kyau, a slow ya karasa inda take zaune ya saka hannu ya dagota tsaye ya sumbaci saman goshinta. "Nayi Miki irin gaisawar ku, Ina key din lokaci Yana ja kada da gaske nayi sakaci kija Mana, muna lallabawa, kin hakura da Zuwa makarantar naji Baki ce komai ba?" "Bani da say, sai yanda kace haka za'ayi". "Nace A'a! in dai Ina raye da lafiya ta bazaki nemi komai ki rasa ba Koda kuwa faskare zanyi to zanyi na samu abinda zankula dake".ya fada Yana daukar luggage din ita Kuma ta nufi kan fridge inda ya ajiye key din jiya. A jere suke tafiya sunyi wani irin dacewa wadda dole idan ka kallesu ka qara suna kokarin fita daga reception su Zayyan suna kokarin shiga, Mahmud ya kalla da jakar matafiya a hannu Yana rike da Hannun Zahra,. "Kam bala'i" Yaji Bakinsa ya subuce ya fada Yana matsawa baya Kamar yanda Ibrahim yayi. "A sauka lfy" Ibrahim din ya fada shi kuwa Zayyan kamar an saka makulli an datse Masa baki. "Ka bashi key din dakin ka biyoni mota Zan baka sako". Ya fada Yana duban Ibrahim, mota Zahra ta shige ta barsu suna tattaunawa kafin ya shigo ya tada motar ya nufi get din fita har yabar harabar hotel din, Zayyan na lekensa ta window sai dai yasan idan yayi magqnar Nan da wani kwabarsa ce zatayi ruwa daya fesa labari, oga da rije jikar mace uwa uba yana tukata da kansa Kai wannan abin surprised da yawa yake"Ga bik
🏠