shiga ku gaisa, a waya ya kirata ya fada Mata sannan yace su karasa ciki.
A kofar gate na shiga ciki suka samu Musaddiq Yana jiran su, cikin ladabi ya gaishe su Yana tambayar Mahmud Aunty Zahra, hannunsa Mahmud din ya Kama Yana bashi amsa har suka shiga part din Ammar.
Sallama sukayi tana zaune a parlourn, sallamar ta amsa tana fadin. "Su Habib ne sannunku Bismillah".
Ta fada tana nuna musu gurin Zama.
Basu zauna a kujerar ba sai suka zauna a Kan carpet.
"Ina yini?"
Suka fada a tare, "lafiya kalau ya wajen malam?"
"Lafiya kalau yace a gaisheku".
"Masha Allah muna amsawa, Allah yayi Albarka, yayi muku jagoranci cikin dukkan lamuranku, ayi ta hakurin Zama da yara".
Ta fada a kunyace Dan har ga Allah tana Jin nauyin yaron da kaunarsa saboda karamcinsa da halin fattako daya nuna lokacin da aka bashi Auren zahra da Rana tsaka ya Kuma sa hannu biyu ya karba.
"Amin na gode ba komai, zahrar tace ma a gaisheku, kuma nazo ne nayi muku sallama zanyi tafiya ne amma in Sha Allah bazan jima ba, na fadawa Abba a samu wadda zasu zauna tare kafin Allah yasa na dawo".
"Masha Allah. Allah yayi taimako hakan baze gagara ba ko can gida Mubi Sai a samu wadda zatazo su zauna tunda akwai yaran sosai ba sai an dauko bare ba tunda yau din ta Zama wata iri Amma kafin tazo sai su Fara Zama da zulai tunda Bata da matsala"
"Godiya muke Allah ya kara sutura" Habib ya fada, suna mikewa har lokacin Autan Ammah Yana jikin Mahmud a zaune. Addu'a Ammah take musu har suka fito Nan da nan wani rauni ya shigi Mahmud haka tasa Umman take Masa a duk lokacin da ze shiga wurinta bakinta baya gajiyawa da Yi Masa addu'a, duk kewarta sai ta rufe shi, "kaimu gurin Mama mu gaisa".
Mahmud ya cewa autan Ammah.
Part din Mamar suka nufa, Musaddiq ne yayi knocking har sau biyu ba'a bude ba Kuma suna jiyo maganganu da sound din tv.
Habib ne yace "mu tafi Dan Allah yaushe zamu tsaya kamar wasu 'yan maula". Har sun sauka daga steps din balcony din sannan aka bude kofar, Asabe ce ganin Autan Ammah da mutane yasa ta fito tana fadin ku shigo Dan Allah wlh bamuji ba sai daga baya Salma ke fadin Kamar taji bugun kofa".
Habib ne yayi farat yayi magana "ai ba komai a gaishe da Hajiyar Daman mujin Zahra ne ya shigo ya gaishe ta".
Sukayi gaba suka barta a tsaye.
Ciki ta koma jiki ba kwari.
Mama ce ta kalleta.
"Wai su waye Naga kin fita Kuna magana dasu ne Kuma Basu shigo ba?"
Zama tayi kusa da mamar, "sirikin ku ne inda mukaje basa Nan yazo gaishe ki da alama Kuma sauri suke tunda sun jima a tsaye ba'a bude ba".
"Wai kina nufin Mahmud mijin Zahra?"
"Shifa sunce a gaishe ki, da alama sauri suke Dan har sun fice.
Baki Salma ta tab'e tana fadin. "saura kiris dai uban kowa ma ya rasa, ba dai kunce kun Kai turaren wutar ba, yanda aka wayi gari aka ganshi da hakoransa talatin da shida haka za'a wayi gari yayi layar zana inga ta qafafar da ake anyi aure, auren ma Dan jeka nayi ka da ba wani armashi yayi ba, Shima Abba Dan ya ganshi handsome ne ya bashi ai ko banza ance mijin agolar gidansa ne".
Dakuwa Mama tayo Mata "Abban naki kike fadawa haka? Nima da farko nayi tunanin ko wani lashi yaga yaron Yana dashi sai da na saka akayi min bincike aka tabbatar min da gidan da kayan da yake sakawa duk Wanda yakewa aiki ne suka kawo Masa Dan wasu ma ance min wannan yaron shugaban aikin nasu ne ya kawo Masa kwancensu Dan ya rinka fita kunya tunda matar tasa 'yar boko ce, shi Kuma almajiran soro ance min ma iyakarsa secondary ya Dan iya rubutu da karatu ne yasa suka dauke shi aikin nasu, har kike wani zaqewa kina sonsa ai da naji haka saina fad'i ba nauyi yo Dan kyau me ake da kyau bako sisi Allah Banda nayi Alkawarin saina Maida Zahra karamar bazawara ba, da barinsa zanyi a garin to idan nayi wannan saken kakanninta zasu iya bashi mahaukatan kudi ya nemi sana'ar da ze rike musu jika gara dai yayi gaba tazo ta zauna na Dora daga inda na tsaya".
Dariya Salma da Asabe suka kwasa Asaben ce ke fadar "Aikinki Yana kyau uwar dakina ba Wanda ze taba hasaso hakan daga bangaren ki kin kasa kin tsare duk wata kafa da wani ze fahimci da saka hannunki a lamarin yarinyar nan".
Dariya mamar tayi itama "Au da sokike na ringa nuna adawata a fill ai Ni duk ranar da tazo gidan Nan da bayanin mijin ya gudu sai nafi kowa kuka da tsine masa".
"Sai Maman mu". Salma ta fada tana kyalkyalewa da dariyar mugunta.
*********
A harabar gidan suka samu Abba Yana yiwa malam Bala direba magana, gurin suka nufa Abban na ganinsu ya nufo inda suke.
"Har kun fito"
"Eh Abba zamu koma"
Suka fada tare, takarda Abban ya mikowa Mahmud.
Hannu yasa ya karba.
"Gashi Nan ka Kara guzuri Allah ya kaiku lfy ya bada sa'a".
Godiya sukayi Masa sosai har Saida yayi fada.
Tare suka fita da Auta har gurin mota ledoji biyu Mahmud ya dauko daga seat din baya ya mikawa Musaddiq.
"Gashi naka daya na Faruq daya tukwaicin ku ne na kawo abinci".
Da murna Auta ya nufi gida Yana fadin "mun gode Uncle".
Cheque din kudi ne masu nauyi Abban ya bawa Mahmud saida abun ya Basu matukar mamaki.
Habib ya mikawa