ke a inda ban zata ba ya cusa min soyayarki lokaci daya nasan baze Bari na shiga gararin rayuwa ba, duk rintsi ze kawo min mafita sai gashi ya kawo min lokacin da har nayi given up Ina kokarin barin garin idan na shaida dauri Aurenku, amma fa da Allah kadai yasan meya faru yanzu to Sai ya taqaita cikin shikimarsa".
Agogon hannunsa ya duba, Zahra tana kokarin magana ya katseta.
"Adana tambayar saina dawo Kinga idan na biye Miki ba inda zan fita, a 'yan kwanakin nan kin mayar Dani wani parrot sai magana nakeyi ba comma ba full stop, wlh kin canzani kwata-kwata da Hajiya Inna zata ganni Ina zuba haka hum..".
Ya fada Yana daukar luggage din daya shigo da ita da dayan hannun dayan Kuma ya mikar da ita tsaye.
"Zo muje ki tayani shiryawa".
Nokewa tayi tana Dan ware idanunta. Shiryawa kuma? Kaje kawai Ni ina nan".
Gaba yayi yaga alama da gasken ze iya shashancewa a gurinta.
Komawa tayi ta zauna tana jujjuya lamarin bawan Allahn nan sai wasu maganganu yake fada Mata ba tare da fashin baqinsu ba.
Kamshinsa shiya fada Mata wanzuwarsa a falon, a hankali ta dago Kai ta kalleshi "Masha Allah" ta fada a hankali Dan ba lallai yaji ba.
Gurin da take zaune ya Dan tsuguna a gabanta ya Dora Mata laptop din dake hannunsa da wasu takardu da list na sunan mutane kusan dari da ashirin da biyar daga local government hudu Alkakeri, Jama'are, Zaki da Dass, karkashin makarantun Allo zasuyi step down training a Nan Azaren schedule ne na aikin da payment dinsu.
Ta dago zatayi magana ya Dora Mata yatsa a biki "kiyi kawai idan na dawo kin tambayeni duk abinda kike bukatar sani bana son nabar garin Nan aikin Nan Bai kammala ba".
Ya Mike fuskarsa ya kawo dad da tata ya Bata light kiss a gefen kumatunta, saina dawo take care". Ya nufi kofar da sauri da key din motar a hannunsa.
Harya rufe kofar Bata dauke idonta daga gurin ba, ita fa mutumin Nan ya Fara Bata tsoro mutane suna daukarsa wani Abu daban ita Kuma tana ganinsa wani Abu daban.
Ta Dan jima Tana sakawa da kwancewa daga karshe ta watsar da komai ta dauki laptop din ta shige cikinki bedroom din ta Haye lafiyayyan gadon ta bude ta shiga aikin inda Allah ya taimaketa yaci karfin aikin karasa Masa zatayi.
*******
Lokacin da Mahmud ya fito Ibrahim da wani sulaiman ya Kira ya Basu aikin kula da dakin da Zahra ke ciki duk da yasan suna da matakan tsaro sosai Amma hankalinsa Bai kwanta ba sai da ya Kara Mata da nasa, gurin motar ya nufa bayan ya zauna ne ya Ciro wayarsa ya bude ta haka Nan ya shiga CCTV da akayi connecting da wayarsa.
Hotunan ne suka fito rababa na dakinta yayi zooming qura Mata Ido yayi lokacin data fito daga wanka tana daure da Karamin towel fararen cinyoyinta sunyi wani sambal dasu ta Kai ta kawo Yana kallonta harta gama, tunda ya Fara kallon yake sakin wani Nishi kadan kadan Dan da gaske ta yamutsa Masa tunani ji yake kamar ya zubar da Alkawarin daya daukarwa kansa a kanta, komawa yayi baya na kofar gate ya dauki hankalinsa ganin wata mota mata sun fito sun dauko wani Abu a Leda sun nufi gate din gidan full screen yayi da gurin da suke ya waye da mama amma Asaben çe bai ganeta ba yana kallon duk abinda sukayi har Zuwa lokacin da Asabe tayiwa Mama rad'a a kunne ta Kira Mai gadin ta bashi kudi suka juya
da yanda suke kwasar dariya har da tabawa kamar yara sai abin ya bashi mamaki, meya kawo su gidan su kadai ga Kuma motar da gani ta commercial ce, girgaiza Kai kawai yana tunanin abinyi.
Da gurin malam ya fara zuwa ya Dan jima tare dashi kafin ya aje Masa Alkhairi yayi Masa sallama, Yana Kara yi Masa addu'ar samun nasara a tafiyar da godiyar Alkhairnin daya bashi, Habib ne ya Dan kalli Mahmud din bayan sun fito Yana tambayarsa..
"Da gaske baka fad'awa Baba malam ba inda zakun kada fa yaji daga baya yayi fada yace ka tsallake kasa baka fada Masa ba.
Kafadarsa ya dafa.
"Kada ka damu da kaina Zan fada Masa in sha Alllah".
Tare sukaje gidansu Zahra inda suka Dace suna kokarin yin knocking sai magaji ya fito, daga gani wani gurin zaya yanda yayi Shar dashi.
Gaggaisawa sukayi kafin Magajin yayi musu jagora zuwan gurin Abban nasu. Anan falon ganawa da bak'insa suka sameshi, sun gaisa Sosai a Nan Mahmud ya fada masa tafiyar da zeyi, Abban yasa Albarka soshi.
.
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH
Page 27
_____Dan Jim Mahmud yayi kafin ya Dan muskuta kadan ya Kara sadda kansa kasa.
"Abba Dan Allah ko za'a taimaka a bamu Aron daya daga cikin masu aikin Nan Mata su tayata Zama kafin Allah ya dawo damu". Ya fada a ladabce
Dan gyaran murya Abban yayi Yana fadin "Hakan babu laifi kayi tunani Mai kyau baza'a bar yarinya ita kadai ba gara da babba, ba komai kome kenan da safe za'a turo wadda zata zauna da ita, Allah yayi Albarka ya bada sa'a"
Sun jima suna Hira da Abban har suke fada Masa harkar kayan spares na kayan motocin da zasu ringa saidawa, Albarka ya sanye musu sannan sukayi Masa sallama, har sun Kai kofa Abban yace Bari ya fadawa Ammah ku