NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 81 of 136

ad'a yana saka wayar a handsfree. "Ya akayi Hayatu". Dariya ce ta kwacewa Sameer Wadda Bai shirya Mata ba. "Wlh zan kashe, wato abin dariyarka na Zama ko?". "Sorry sir wlh ji nayi gaba daya tazo min, Kuma ko sallamar da nayi baka amsa min ba". "Ka Fadi abinda zaka Fadi Kona kashe da gaske Kuma sallama na amsa Kaine dai bakaji ba, duk safiyar Allah baka tashi kirana ba sai yanzu da tsohon dare salon ka Hana mutum rawar gaban hantsi, na fada maka idan Ina bukatar Abu ni zan nemeka Amma tsabar saka ido sai ka kirani ni, to fad'i meya faru? Ina jinka". Ya fada Yana maido ta jikinsa. "Game da maganar tafiyar Nan ce anya zanje kuwa wlh jiya danaje sokoto daukar wadannan hardcopy din na shiga gurin Hajiya Inna muna cikin magana saiga uncle Mustapha ya shigo a sukwane bansan wane minafikin bane ya fada Masa nazo garin ba tunda bana zuwa lokacin da suke gida, ya tasani gaba da sababin nasan inda kake ina kallon su suna walaqiqin nemanka Amma nayi mirsisi naki fad'a musu komai, Ni Ina ta faman lallaba mutuniyar taka amma Saida Uncle mustapha ya Bata lamarin Dan wlh kuka take da hawayen ta bibiyu tana fadin Dan Allah na fada Mata idan mutuwa kayi saita hakurw tasan ita kadai zata nesanta ka da ita, wlh yanda ta bani tausayi da bude aiki kawai zanyi sai Kuma na tuna da warning dinka kawai na fasa, Kuma wlh yanda uncle yayi ba abinda ze Hana shi bibiyata ta karkashin kasa ban sani ba a gida da waje amma ya kake ganin za'ayi? Numfashi ya sauke me karfi yana Kare matse zahrar a jikinsa har Saida tayi 'yar karar Jin zafi. "Karar me nakeji a kusa da Kai ne?". "Ina ruwanka tsabar saka ido, to madam ce a kusa Kona baka ita kaji for confirmation, a'a Barta a gaisheta". Tana jinka a speaker wayar take, ka Bari kawai Zancen baze yuwu ta waya ba idan Allah yasa na shigo sai mu tattaunawa Kuma ka tabbata komai ya kammala kafin na shigo goben in Sha Allah" "Noted, in Sha Allah a gashe min da ita sosai a fada mata Batool tayi ta kiranta dazu ba'a dauka ba". "Ina ga a gida ta baro wayar ka ganta Nan sai rigima take zabga min irin tasu ta shagwababbun 'ya'yan larabawan" ya fada yana dan matse dantsen Hannunta kadan. "Wash Allah na da zafi fa". Ta fada tana Masa wani kallo Mai ma'anoni kala kala. "Allah ya bamu Alkhairi" Sameer ya fada Yana kashe wayar Bai jira yaji abinda Mahmud din ze fada ba. "Kinga kinja ya katse Kiran bamu gama bayani ba irin wannan Abu haka ai sai ayi zaton muna hanyar shuga wata nahiyar ne". Sunne Kai tayi a jikin kirjinsa, "Dan Allah ka Bari ni me nayi,". "Ba komai". "Bayani zakiyi da yaren garinku yarinya". Gurin zamanta ya maida ta sannan ta tada motar suka koma kan titi, tunda zahra ta koma gurin zamanta take Masa kallon tukuma da neman Karin bayani. Amma saiya fuske abunsa kamar be gane ba, Yana ta faman tukinsa ko a jikinsa. Zaranda hotel taga sun shigo, kallon mamaki tayi Masa a kasan zuciyarta tana tunanin me kuma za'ayi a Nan shida yace unguwa zata raka shi to Wai mema ya hada shi da hotel ne? Gurin da aka tanada don parking ya nufa ya kashe motar. Fitowa yayi ya zagayo kofar da tare zaune ya bude ya Mika Mata hannunsa ta Kama ta fito. Kulke motar yayi ya jata suka nufi ciki, a Hanya suka hadu da wani security da gani akwai sabo sosai a tsakaninsu. "Ranka ya Dade an shigo lfy? Ya fad'a Yana kallon Zahra a kaikaice. "Lafiya kalau Ibrahim ya aikin?" "Lafiya kalau yallabai". Ya fada Yana niyyar wucewa yana Kara kallon Hannunsu dake sarke Dana juna. " Ibrahim gafa madam Dina Yau na kawota taga mafakata". Ya fada Yana Dan murmushi. Dawowa yayi Yana fadin. "Masha Allah yallabai Allah ya bada zaman lfy, ai Dani aka daura Auren babban masallacin juma'a, madam sannu da zuwa gurin namu". Ta amsa ta gaishe shi ya amsa yana Mata Allah Sanya Alkhairi sannan sukayi gaba, dakin da yake kusan mallakinsa ya bude musu suka shiga lumshe ido Zahra tayi Dan wani special kamshi da sanyi A/c ne ya bugeta, yanayin ba Karamin Dadi yayi Mata ba, direct kan sofa ya nufa da ita tare suka zauna har lokacin Bai sakar Mata hannu ba. Falon tabi da kallo ba karya komai yaji Dan an kawata shi sosai. "Wai me zakayi a nan?" Ta fada tana masa kallon ido cikin ido. "Me kikeci na baka na Zuba? ai dai muna tare dake ko! zakiga abinda zanyi yanzu ki zauna ki dan tayani aiki kafin naje unguwar ku gurin iyayena sallama". "Dan Allah kaje Dani " "Kai ! Naje dake Ina? Lallai kina so na amsa tambayoyi kenan kwanan ki nawa rabonki da gidan? Kawai na kawoki Nan ne kisan dakin yana cikin abubuwan da suka zamar min abin tunawa a zamana na garin Nan kinsan saboda ke na kama shi ya Zama permanent dakina tsawon shekara kusan biyu da nayi a garin nan?". Galala take kallonsa. "Saboda Ni kamar Yaya?". Wani kallo yayi Mata Yana Dan taune gefen lips dinsa na kasa. "Naki Wasa ne yarinya,Wai kin zata daga cewa an bani Mata saina karba kawai? Niga sarkin tausayi ko to Daman Nima Ina son kayana kawai dai kinfi karfina ne na mikawa Allah kukana Ina zaune Kuma ya juya lamarin gareni tunda shiya hadani da
🏠