NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 136

ha kyau kamar a dauke ba boye. Ga wani slow music da mc din ya saka na wakar Amarya da ango kowa ka gani cikin nishadi yake sabanin Amarya da Yayarta Banda ta Riga ta gayyato mutane harda wadanda sukayo Mata tafiyayya sukazo da ba abinda ze saka tayi wannan taron to Amma mutum Bai Tara Sani ga Allah ba. An raba kayayyaki na alfarma na bikin, sai magariba taron ya tashi, zuwa yanzu 'yan Qananan maganganu sun Fara fita a tsakanin kawayen Zahra tunda har zuwa lokacin ba wani duriyar Ango ko wani nasa, sai Dan kus-kus ake abinda yafi bada mamaki bai wuce ganin anata faman programs ba normal. Su Mahmud Basu samu kansu ban sai bayan sallar insha'i lokacin suka zauna Dan wuni guda suna ta faman sunturi daga can zuwa can abin dai ba sauki dan su sameer suna zuwa gidan suka babbago aikin da sai anyi sati ba'a Gama ba Dan sunce tsarin gidan gaba daya za'a sake, basunda ta cewa tunda oganninsu ne sai godiya suka dunga zubawa harda su Bashir. Gurin karfe goma malam ya Kira Mahmud a waya yace yazo cikin gida ya same shi. Saida ya leka falon iya Abu suka gaisa tana faman jansa tana ita ce ta karfen Dan haka ita zata koma sabon gidan a kawo Amarya nan. Da haka ya karasa turakar malam Yana zaune a falo Yana sauraren wa'azi a TV, yayi sallama Malam din ya bashi izinin shiga, Nan kasa ya zauna Yana gaishe da malam din.Wasu manyan ledoji malam din ya nunawa Mahmd Yana fadin. "Dauko wadan can kayan ka duba daya Wanda nasa a kawo maka ne biyun Kuma wadannan masu kungiyar ne ta taimakon tsangayu suka kawo ga lemuka can da ruwan roba sun kawo yafi catoon dari sunce kada ayi abinci ma duk za'a kawo, har na rasa da wane bakin zan gode musu, sai dai Ina rokon Ubangiji s.w.w yafi mu yabawa, naji su Habibu ma sun ce sun dauko aiki Mai yawa a wancan gidan ko?" "Eh wallahi munyi-munyi su Bari suka Kiya Wai haka aikin Qungiyar yake in dai kana musu aiki idan wani Abu ya sameka Mai Dadi ko marar dadi su zasu tsaya maka". "Alhaji yace min kun shiga dazu bayan sallar magariba har da bakin kunyi Masa godiya, kun kyauta haka ake so". Lokacin Mahmud ya koma dakinsu Habib baya Nan gurin da yake aje makullin lifan dinsa ya duba ya kuwa you sa'a yana nan, lodojin ya zube a kan gado ya dauki makullin ya rufe dakin ya hau mashin din yayi gaba. Bai dawo ba sai kusan Sha biyu da rabi har lokacin kuma Habib baya dakin yasan suna can suna kujuba kujuba. Yauma Zahra taso kwana a dakin Aunty Hasana saboda tana bukatar kadaicewa Amma Sajida ta matsa Mata da mita Saida suka tafi Amma fa zuciyarta Bata da nutsuwa gashi tana ankare da Aunty Hasana tun jiya da dare a taje can gida cikin gari Bata da nutsuwa ko alama Amma tana ta kokarin ta basar sai dai ko Yaya mutum ya shiga damuwa indai kayi Masa farin Sani zaka fahimta, ita Abu mafi Bata mamaki yanda aketa kwaramniyar bikin ba wani canji sai dai abunda baza'a rasa ba duk da Daman ba wata muguwar bidi'a ba ta had'a, walima ce kawai Bata Sami ba saboda tace ita malam Tijjani Ahmad zeyi Mata Kuma bayanan yana Umara. Tunda tayi sallah ta kasa tashi daga gurin tana kallon su Sajida sunata sabgarsu, Amma ita da wata irin faduwar gaba ta tashi ta rasa nutsuwarta kwata kwata da kyar ta tsahi sauko kasa gurin Aunty Hasana a fall ta sameta tana hadawa Abbansu Haidar break fast. Gurin dining din ta karasa tana gaishe shi sannan gaida Auntyn. Dakin Auntyn ta shiga kwanciya tayi tana ta faman sakawa da kwancewa zuwa yanzu dai tasan tabbas da matsala sai dai yanda ba Wanda ya fad'a Mata shi yasa itama ta zubawa sarautar Allah Ido taga iya karshen film din tasan ko menene yau dai za'a yita ta Kare tunda yau ne deadline duk wata kunbiya kunbiya za'a zazzageta. Tun karfe goma Mai yiwa Amarya make up tazo Amma kememe Zahra tace ita bataso a kyaleta aka dunga yiwa kawayenta, ganin guri ze kure ne Sajida take ta fadawa Aunty Hasana Saida tazo sannan akayi Mata light makeup Amma fa duk da hakan tayi karshen kyau, farin material ne ta sakata Mai touching din sky blue sai aka daura Mata head shima sky blue din takalman da pos din duk sky blue din ne. Wani san sanyan kyau tayi na ban mamaki, komai na Zahra Mai kyau lallai zaharar ce Dan duk cikin kawayen Bata da mahad'i. A babban masallacin juma'a za'a daura auren Masha Allah, ango ya fito Shar abokansa sai mamakinsa suke Basu taba sanin kyawunsa da cikar haibarsa ya Kai haka ba sai daya fito sun Sha mamakin kwarai har wasu suka Fara kokonto a kansa, Yana kallon yanda idanun sukayi Masa caa. Dan dakakkiyar getzener ta saka ga takalman da agogo ga hula, Sam bazaka taba cewa Wai alamajirin malam bane ba, ga wani irin kamshin tunda ta tumkaro taron abokanensa kamshin ya hade gurin. Daga gefe sameer ne da abokinsa Naraddeen suna tsaye lokacin da Mahmud ya fito Sameer ya kalli Naraddeen din yace "wallahi wannan guy kwallon Dan duniya ne na rasa Gane kan alkiblar daya kalla Wai aure zai daura shi kadai kamar marara gata, ni so nake Naga karshen wannan wasan kwaikwayon nasa. Daga inda yake tsaye ya kafe Sameer da Ido ko Bai fad'a ba yasan me yake
🏠