NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 79 of 136

ina da nasibi a cikin sana'ar, sannan Habib ma munyi magana zamu Fara siyar da spare parts na motoci a nan Muda lawal market din dai". "Allah ya bada sa'a, Kuma idan ka tafi sai yaushe zaka dawo? Ko kaima shike Nan abinda yake faruwa Dani ze faru a kanka kaima, kada ka tafi ka barni Dan Allah tunda nasan ba Sona kake ba baka ni akayi sadaka, Dan Allah ka taimaka ka kaini Jordan tunda Ina kudin flight kawai ka taimaka ka fitar Dani daga kasar da sunan Kai zaka tafi dani, bana son Ammah ta qara shiga cikin damuwa a kaina wlh Batasan tashin hankali ba Sai Dana isa aure Kullum idan kaga Ammah a cikin tashin hankali to a kan lamarina ne ni Kuma yanzu bana fatan na qara ganinta cikin bacin rai ta dalilina, kaje ka fada musu zaka tafi Dani ko Kano ne ka Kaini na zauna gidan su bestie kafin na samu visa, nagaji da Kasar nan wlh Ina da gata Amma sai walagigi rayuwa ta takeyi anan Dan Allah kayi min wannan alfarmar Koda ita kadai zakayi min ta karshe a zamana da Kai". Ta kifa kanta a jikin kafad'arsa ta saki wani kuka Mai tsuma zuciya. Bai hanata ba ya dai Kara matseta a jikinsa Yana shafa bayanta yasan abin Yana cin zuciyarta ne bata rasa komai ba amma an dabaibaye Mata Jin dadin rayuwa kamar yanda Baba malam ya fada masa. Sai da tayi Mai isarta ya dago kanta daga jikin kafadar tasa. "Kiyi hakuri kowa da irin tasa jarabawar ke taki a haka tazo, Kuma waya fad'a Miki zan tafi na barki bazan dawo ba? Waye kuma yace Miki bana sonki? Kinsan tun tsawon lokacin da nake dakon soyayyarki kuwa? Tun Baki san meye son bama yarinya share hawayen ki Mahmud naki ne har abada, dole kije Jordan ke me gida sukutum a can.Amma yanzu kiyi hakuri nema zani idan Kuma na zauna bakya son tafiyar saina fasa Sameer yayi komai kawai nace madam ta Hana". "Kaje kawai idan baka dawo ba nasan abinda zanyi". "Keh! kina da hankali kuwa me zakiyi wlh zan turaki gurin Hajiya Inna duk da ban shirya zuwa yanzu ba kawai ki Kira min ruwa, zaman Allah nakeyi zamanki nakeyi badan ke ba Dana Dade da barin garin Nan". " Ni Kuma?" "Off course" Ya fada da karfin gwiwa. "As how?" Share ta yayi kamar bai jita ba. "Tashi ki rakani kada dare yayi, dauko Mana key din motarki na dana kada na tafi ban Sanya albarka ba, ki canza shiga kada a kalle min kayana" fada Yana mikar da ita daga jikinsa. Duk kin haye min cinya kinsa sai ciwo take min". Ya fada Yana Mata wani smile. Bata kula shi ba tayi gaba abinta duk zuciyarta ba Dadi sannan tana jujjuya maganganunsa a zuciyarta, kinsan tun lokacin da nake sonki? Danke nake zaune a garin Nan gasu Nan dai da yawa. Saida ta sakarwa Kanta ruwa sannan ta shirya agurguje ta saka wata Riga da siket na atamfa super dinkin ya zauna das a jikinta ta saka mayafin da yayi matching da atamfar ba tayi amfani da turaren kaya ba body mist kawai tayi amfani dasu a jikinta kusan kala uku, sai ya bada wani sansanyan kanshi Mai dadi. Tana gyara gyalen ya shigo dakin tsayawa tayi tana kallonsa shida yace unguwa zata raka shi sai gashi da Riga armless da wandon ta farare tas na kamfanin Adidas sai taga kwata kwata ya canza Mata ya koma irin 'ya'yan hutu din Nan na gaske wadanda Jin Dadi ya gama ratsa su yayi wani irin fresh da shi. Matsowa yayi kusa da ita Yana Dan watsa hannu irin dai na isassun yaran. Mayafin ya kama ya ida rufa Mata a kanta. "Kallon fa na menene? Kona canza Miki ne?". Kai ta girgiza Masa. "Baba son body language fa ki bude Baki kiyi min magana". Yana janyo ta jikinsa. "A'a kawai dai da naji kace unguwa zan rakaka kuma na ganka da......" Sai tayi shiru. "Karasa Mana sai Kika ganni da shigar nigas ko?" Shirun dai tayi. "Idan Ina tare da iyalin dole na sake, kema da nace ki canza ai na Shan iska nake nufi ba Wai irin wannan ba, zo muje ki canza yawon Shan iska zamu ki min hira ki bani labarin ki tunda ke bakya bukatar nawa ki bani happiness a wannan Daren yanda duk inda nake na rinqa Tino da abubuwan su zamar min kamar kina kusa Dani". "Ni dai Dan Allah ka barni haka muje kawai" "Dauko key din to muje dare nayi Kuma Ina son ganin Baba malam da Abban mu, ko ba namu bane?" Ya fada Yana kallon ta, an samu cigaba, tunda ko banza tunda ya mamnatse ta take iya kallon idanunsa ba kamar da ba da Bata yarda ta kalleshi. "Namu ne". Ta fada a hankali, badan Yana very closer to her ba da ba lallai yaji me take fada ba. "Oya let's go". Ya fada Yana nufar kofa, saida ya kashe electronics na gidan sannan suka fito Yana time da karamar luggage a hannunsa,Kati ya curo daga cikin wallet dinsa ya saka a kofar ya rufe, daga nesa Mai gadi ya hangesu sun nufi parking lot din gidan inda motar daya take ajiye, a ransa yake fadar "duk inda wannan Dan ya fito Dan mafita ne ba irin yaran Nan bane lalatattu kamar yanda aketa surutun abun masu kushe da ganin rashin kyautatawar su Alhaji nayi masu gani kyautatawar nayi". Yana can Yana tunani Bai ankara ba yaji Karan Horn alamun har sun karaso Yana can Yana nashi zarafin. Da gudu ya tashi Yana fadin Ayi hakuri nayi zurfi gurin tunani ne, a dawo lfy Allah ya tsare". Horn y
🏠