NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 78 of 136

abinda ya fuskanta kawai dai Bata daukar raini. Tana karasowa saita zauna kusa da kafafunsa a kasa taki zuwa gurin hannunsa da yake Miko Mata. Dan murmushi yayi Shima ya sauku Yana facing dinta da karamar ledar dake hannunsa, Mika mata yayi."Gata Nan ayi hakuri ki hada ta batirin ma yana da full charge da sim a ciki, duk numbers dinki important suna ciki. Wayar ta bude sabuwa ce Kar jujjuyata ta Fara tafi wadda ya Fara Bata tsada nesa ba kusa ba kallon tuhuma ta Farayi Masa tana girgiza Kai tare da Mika masa wayar tana Fadin. "A Ina kake samun irin wadan Nan wayoyin na mahaukatan kudi wlh ba ruwa na ka rike kayanka bana so ka maido min tawa ta asali kawai". ✨✨ ✨✨ ✨💎AUREN HUCE HAUSHI💎✨ Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah s.w.a, salati da daukaka da Aminci su tabbata ga Annabin Rahama Muhammad s.a w.w. Page 25 📖🖋️ ________Dariya ya kama harda hawaye abinda bata taba gani ba. Sororo tayi tana kallonsa, ita bataga wani abin dariya ba a maganarta, hannu ya Mika ya karbi wayar kunnawa yayi ya Mika mata Yana kashe Mata ido tare da d'age gira. "Kina son kisan inda nake samun mahaukanta kudaden Nan ne?". Kai ta gyada Masa. "Good ki Bari sai ranar da Kika Zama ni na zama ke na mallaki kayana, a ranar nayi Miki Alkawarin sanin komai nawa na duniyar Nan, Idan Kuma yanzu you are ready za'a taimaki Dan Malam a lullubeshi da bargon ni'ima to? yanzu kuwa kisha labari har wanda Baki nema bama zan fad'a Miki, tunda ke inda nake samun kudi kawai Kika bukata baki son sanin waye ni?daga Ina nake?meya kawoni garinku? Gasu nan rab'ab'a da yawa, to ki rubuta ki aje har abada ni Mahmud bazan tab'a ciyar dake ko shayar dake ko wani Abu na jindadin rayuwa da haramun ba, duk abinda na Baki ki tabbata da gumin halalina na nema, kinga wannan wayar da kudina na saka na saya Miki,wato kina tsoron kada na Sato kayan mutane na kawo Miki ko?" Kai shiga gigizawa. "Ni ba cewa nayi kayi sata ba, gani nayi kana ta abubuwan da sai Mai wadata ne ze iya yinsu Kai Kuma Naga...." Sai kuma tayi shiru tana kallonsa. "Oya continue Mana,kinyi shiru wato Kinga bana aikin komai ko?". Shirun tayi Bata Kara cewa komai ba. "Tashi ni ki bani abinda zanci idan na biye Miki da wannan yarintar taki sai yunwa tayi min illah kisa a Fara gulmarki ace kina barina da yunwa, ganshi kin sani azumin da Babu lada". "Ba Kaine kayi zuciya ba ka tafi kabar abincin" Ta fada a shagwabe. "Ki tashi ki bani kada lissafin ya canza fa" Ya fada yana matsowa jikinta sosai, da sauri ta Mike ta nufi dining inda ta jera abinci. Table mat ta shimfida a Kan carpet din sannan ta dauko abincin ta aje. Plate biyu ta dauko dayan ya janye. "Ki Zuba Mana a plate daya ya Isa ai Kuma indai Ina gida plate din mu daya tunda Kika yimin horon yunwa yau daga Wasa Dan kawai kewar Hajiya ta ta kamani shine Kika horani duk ranar dana kaiki gabanta saina fada Mata tasan irin zaman da zatayi dake, ni Dan gata ne a gurinta bana laifi zakiga yanda take sona". "Ko?" Ta fada tana zuba abincin a plate, Dan tura Masa plate din tayi kusa dashi "Gashi Nan ni bana Jin yunwa". "Ashe zan Miki dura wlh, sai kinci kuji min yarinya da kinibibi Wai so kike da karfi sai kin koya min surutu ne? Kin iya kalato abin magana da wani bakinki chut". Ya fada yana shafo pink din lips dinta. Taci Amman ba wani na kirki ba da gaske abinci Bai dameta ba barta dai da 'yan ciye-ciye. Bayan sun gama ne ta kwshe kayan ta gyara gurin duk Yana kallonta komai tayi kyau yake mata gata ba wata babba ba sai dai akwai Sama da kasa masha Allah. Lokacin data gama ne ya yafito ta da hannu,a hankali ta nufo shi kamar me counting steps sai rausaya take, wani yawu ya hadiye, Dan risinawa tayi a gabansa duka hannuwanta ya kamo ya zaunar da it kusa dashi. "Zaki rakani unguwa?" Ya fada Yana zame Mata veil din da tayi rolling gashinta ne ya bayyana biki sidik dashi sai walqiya yake yasha gyara ga kamshin hair spray Yana tashi. "Eh zani Bari naje na shirya". ta fada Tana kokarin zare jikinta daga nasa. Duka hannuwansa yasa ya riko kugunta ya hade ta da jikinsa. "Ina zaki?wane irin Shiri zakiyi kinsan inda zamu ne kike sauri?". Lakwas tayi a jikinsa da karfi da yaji so yake ya Saba mata da Zama a jikinsa gashi baya ko Jin jauyin taba Mata jikin sai dai idan Bai soba. "Bazaki tambayi inda zamu ba, kina Neman sake canza Kaya". "Nasan gida zamuje Mana". "Ai kece gidan, kinaji da so nake muje gidan da gaske mu roki alfarmar a bamu aron me aiki daya Wadda zata zauna min dake kafin na dawo". "Kafin ka dawo? Ina zakuje?". "Au Ashe ban fada Miki ba, aikin NGOS din Nan ne ya taso suka gayyace mu zuwa meeting da zasuyi a UK Kinga ai bazan zauna ba da dollars ko stalling founds suke biyan mu, idan Allah yasa na samu da Dan auki Kinga na Kara jarina tunda Naga Nima Ina sha'awar siyar da materials har munyi magana da Abba yace ze bani rumfa daya a Muda lawal market na gwada ko
🏠