NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 76 of 136

unani kala-kala Sam na kasa samun nutsuwa". Tashi Zahra tayi ta shige ciki tana Fadin "Bari kawai bestie guy din nan ya fa karbe wayar tun ranar da Kika tafi ya dauketa da safe daya shigo, shine fa daya shigo ya tarar duk na hargitse gado ina neman ta yace tana gurinsa, ya kama min wasu zantika akan Kiran da Musbahu yayi ranar ni kuma na kasa hakuri shine yayi min Rashin mutunci Kuma ya hanani wayar". Ta fada kamar zata fashe Mata da kuka, tambayar ta tayi yanda abun ya faru Bata rufe Mata komai ba ta fada Mata. Bata katse Mata hanzari ba har ta gama. "Amma ban taba sanin Baki da wayo ba sai yau, Gaskiya Baki kyauta ba ko alama Ina hankalinki ya tafi kada ki Kara Koda Wasa saboda wani ki ciwa mijin aurenki fuska ai wallahi jarimi ne daya iya hadiye fushinsa bakiji a jikinki ba". Ta fada a kufule, kit ta kashe Kiran. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana kallon wayar a zuciyarta tana fadin ji a jiki na nawa Kuma ba ze fadu bane shi yasa. Lokacin da zahrar ta fito wasu bakin ta tarar sun shigo su biyu har Amatu ta kawo musu ruwa da drinks suna hira dasu Aunty safiyya, sallama tayi musu sannan suka gaisa Nan Amatu tace musu "ga matar gidan nan". "Masha Allah" Suka fada a tare sannan babbar wadda zatayi kamar sa'ar Aunty safiyya tace "mune makotanki da hannun dama sunana Hafsat Amma ana kirana maman junior, wannan Kuma kanwata ce Nuratu da take karatu a Nan Abubakar Tatari Ali polytechnic (ATAP) aiki ne ya kawo Mai gidana mu 'yan Taraba ne". "Masha Allah! Allah ya taimaka ya bada sa'a". Suka fada. Sun Dan jima ana hira dasu sannan suka tafi har gate Amatu ta rakasu da ledar kayan garar biki. Suma mikewa Aunty safiyya tana goya Shureem da yayi barci, Dan langabar da Kai Zahra. "Wai har zaku wuce ne Kuma Aunty?". "Eh mana zan shiga gidan fachalata data haihu bana Nan". "Amman Banda ke dai Amah gaskiya tunda nasan kina garin Nan sai karshen wata keda jama'are". Aunty safiyya ce ta tari numfashin zahra "Ai ita ke driving dinmu ya zan barta a Nan ta dawo Miki special ko weekend ne". Alamar bude kofar da akayi ne yaja hankalinsu, Mahmud ne ya shigo Yana musu sallama da katuwar leda a hannunsa, tunda ya shigo Aunty safiyya ke kallonsa ita dai tasan wannan fuskar amma ta Yaya za'ayi haka ko Kuma kama ce kawai. A cikin takunsa na cikakken namiji ya shigo, da sauri Zahra ta nufo gurinsa tana Fadin. "Sannu da zuwa". Tana Mika hannu zata karbi ledar. "Da nauyi bazaki iya dauka ba". Ya fada Yana kallon ta. Har cikin kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce bedroom. Amatu ce ta zunguri zahra. "Ke! meye hakan Kuma? Kika wani sharesa Kada dai kice min sokoncin da kike bazawa a gidan kenan ko Kuma Dan kin gammu ne kikayi wani biris dashi". "Gaskiya Kam ki dage ki Kama mijinki irinsu tsada suke". Aunty safiyya ta fada tana nunawa Zahra hanyar daya bi. "Kai! Aunty Kuma ......" Bata karasa ba Amatu ta Kama hannunta ta nufi steps din tana Fadin "kije kawai tunda daman tafiya zamuyi saina shigo Saturday in Sha Allah". Dan raurau tayi tana kallon Aunty safiyyar. "Na gode Aunty ku gaida gida saina zo har gida ban gajiya". Dariya Auntyn tayi. 'Haba dai sai dai mun dawo, wannan turaren kada kiyi Wasa dashi tun daga besse na taho Miki dashi kakata ta wurin Babana take haduwa da Kanta Yana da matukar kyau sosai ba sai fada Miki ba da kanki Zaki nema". Dawowa tayi Saida ta rakasu har gurin mota duk da mitar da Amatu ke mata, ta hadasu da kayan garar fal ledoji biyu dasu bokitan roba da mug masu kyau da plates Wanda Aunty Hasana ta bada aka kawo mata saboda Baki masu zuwa. Saida suka fice daga gidan sannan ta dawo ciki. Bata shiga ciki ba a parlourn ta zauna tana mitar. "Idan na shiga me zan Masa wanda yake ganina a wata Mai neman rayuwarsa". *** Saida Amatu ta dai daita a titi sannan da Dan dubi gurin da Aunty safiyyar ke zaune tana rungume da Shureem. "Aunty nifa wani Abu ya bani mamaki da daure Kai" "Kamar me fa?". "Duk gari ya dauka an aurawa zahra Almajiri k'olo saboda ita ba 'yar Alhajin bace, surutu dai gashi nan, ni Kuma yanzu Naga sabanin abinda ake fada, yaushe Zaki kalli wannan kice Yana Qasqantacciyar rayuwa irin wadda ake fada?". "Ni Nama fiki mamaki Dan ni dai Idan ba gizo idona yayi min ba ko Kuma kama ce ta halitta tunda ance kowa Yana da Mai Kama dashi a wani gurin, da sai nace Miki M.M DANGE na gani". "Waye hakan?". Amatu ta tambaya. "Bazaki gane ba Amatu wasu Family ne a sokoto masu mahaukanta kudi Nima fa sau daya na taba ganin M.M DANGEN a bikin wata cussing Dina zainab data auri Dan Family din, Kai gaskiya bashi bane inaga Kama ce kawai, amma Kuma kamar harta baci sai dai ba yanda za'ayi DANGE ya iya rayuwa a nan". "Kamar Yaya Aunty?" "Tab kinsan kuwa waye shi? ai inaga kaf ba Wanda ya mallaki abunda ya mallaka a duk Family din, gashi yaro matashi Kinga gidansa na sokoto ma kuwa? Banda na Abuja da sauran garuruwa, to in kuwa shine me zeyi da Dan wannan gidan ai ji zeyi kamar Yana rayuwa a kurkuku ne, bama shi bane shifa ko bodyguard dinsa abin kallon ne Suma su
🏠