NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 75 of 136

e saketa to inaga sai dai ta mutu da auren Dan Banga hakan ba a tare dashi,ni a yanda na gani a istiharata ma ya Santa batun a Nan garin naku ba Kuma da soyayyar ta Mai karfi a zuciyarsa wadda har abada baze iya rabuwa da ita ba, ayi dai hakan yanda Idan iyayenta suka gaji da jiran dawowarsa Bai dawo ba su raba auren da Kansu". Bayanin ya kwantawa da Mama hankali, ya kawo abubuwa ya bata har Wanda za'a hada da tuaren wuta a bawa zahrar Idan harta turara Mahmud ya shaqa shida Azare har abada. Kudi masu kauri Mama t✨✨ ✨✨ 💎 AUREN HUCE HAUSHI 💎 ✨✨ ✨✨ MAMAN FATEEMAH PAGE TWENTY FOUR (24) _____ Tun bayan tafiyarsu Inna da magaji sai gidan ya zamar Mata shiru Bata Dade a parlourn ba ta koma ciki, da taga tunani yana neman ya dameta saita dauko qur'an dinta ta Fara karatu Saida taji Kiran sallah ta aje taje tayo alwala. Bayan ta gama sallar ta Haye gado ta Kara A/C tayi kwanciyar ta ba tafi minti talatin da kewnciya ba taji alamar Baki ana Danna bell, tashi tayi ta nufi kofar da gaske dai bazata samu barcin na kirki ba,Kofar ta bude a hankali su Amatu ita da Aunty safiyya ne guri daya suka zauna a Dr sulaimanu Adamu model school of Hygiene inda tayi service, su Kuma permanent lecturers, rabon ta da Amatu tun ranar daurin aurenta dan lokacin da zata wuce jama'are garinsu Bata biyo ta gidan Ammah ba daga gidan Aunty Hasana ta wuce kawai. Cikin nuna tsantsar farin ciki Zahra ta rike hannun Amatu tana fadin "wlh nayi fushi Amah Ina nan Ina jama'are? Amma kikaqi dawowa ni Aunty safiyya zanyi welcoming kawai Amma ke kam dai sai a hankali kawai, Aunty sannu da zuwa". Ta fad'a Tana Basu hanya tare da karbar yaron Aunty safiyya dake hannun Amatun. "Hakan ma na gode tunda an karbi Auntyn ai shike nan tunda ita ta gari batayi laifi ba saini da nake can kauyen mu". Ta fad'a Tana Zama a cikin one seat dake kusa da ita. "Eh wlh Aunty tana da excuse a gurina tunda nasan Bata Nan taje gida sokoto Amma ke kuwa ko waya fa Baki Kira kinji ya ake ciki ba". "Kice dai ban Kira ba. Amma tambayi Sajida kiji na kirata yafi sau ashirin ma ke dince lokacin Kiran baze yuwu ba Sai ki qara narkewa". Dariya suka saka su duka harda Aunty safiyyar. "Wlh Amah saina rama kinci bashi, Wai na narke kamar wani danyan tuwo". "To da mecece? mutuniyar dake somewa Kikayi fa dif kika dauke wuta". Kyale Amatu Zahra tayi ta karasa kusa da Aunty safiyya ta zauna ta Dora Shureem a Kan cinyarta tana Fadin. "Aunty sannu da zuwa Ina yini?" "Lafiya kalau Amarya ya Amarcin Naga ya barbeki kanwata Masha Allah". Dan sinne Kai tayi tana Fadin "Kai Aunty Ina wani Amarci a Nan kawai dai". "Gulmammiya Kinga yanda kikayi wani mahaukacin kyau kuwa? Ai da gani Amarci ya tabbata a gare ki,wa Zaki kife a baibai yarinya Kar nake kallonki fa". "Allah ya shiryeki tunda haka Kika zama, Bari ki gani". Ta Mike da Shureem a hannunta ta nufi kitchen, saida ta Zuba musu kayan garar a plate ta dauko musu ruwa da drinks ta dauko plate ta fito tana Fadin "Amah shiga ki dauko dayan Dan Allah". Sai da suka Gama sannan Zahra tace su shiga suga gidan, ko Ina suka shiga Fadi suke Masha Allah! a gurin fridge din dake cikin Dan Arc din dake tsakanin kitchen da dining area ne Aunty safiyya ta kasa hakuri Saida ta magantu lokacin data Kai hannu ta bude tana fadar. "Yau ne ganina na biyu da fridge din nan naso shi kamar qaddara Amma da aka fad'a Mana kudinsa Saida na Raina kaina" "Kai haba Aunty bakiyi niyyar saye bane". Zahra ta fada. 'yar dariya Auntyn tayi. "Bazaki gane ba Idan ci baizo daya ba ai koshi ma baya zuwa daya". "Haka ne kam Aunty". Amatu ta fada, suka nufi bedrooms dinta ko Ina dai maganar daya ce Masha. Amatu ce ke fadar "Allah ya mayar damu danshinki". "Amin. Amma Banda kalubale irin nawa, ba Dadi Amah har gobe abun Yana damuna bani da nutsuwa ko Kankani wlh duk lamurana sun tsaya cak bani da wani karsashi irin na amarya a gidanta, komai ganinsa nake Wai banbarakwai kamar a mafarki haka". Sai Kuma idanunta ya ciko da hawayen da taketa kokarin kada su zubo. "Ayya haba Zahra kiyi hakuri Mana, ai zuwa yanzu yaci ace kin hakura da koke-koken Nan tunda Mai abkuwa ta abku ai sai hakuri ki rungumi abinda Allah ya Baki ki dangana wata Rana sai labari". Aunty safiyya ta fad'a. Parlour suka dawo sukaci gaba da Hira, rabi duk ban Baki ne Aunty safiyyar kewa Zahra da nuna Mata ribar hakuri a cikin hirar ne Amatu take fadawa Zahra sakon Sajida na tana kiran wayata Amma Koda yaushe switch off. Dan lumshe ido tayi sannan ta bude tana kallon Amatun. "Matsala wayar ta samu shi yasa ba'a samuna Amma in Sha Allah soon zan sayi wata, yanzu bani taki na kirata". Wayar Amah ta Mika Mata tana dialing din number ta. Tana dauka ta Fara mata tsugudidi. "Yau wacce Rana Amatu ta kirani". "Assalamu Alaikum ayi sallama Mana bestie". Ta fad'a tana murmushi. "Kai!!! wa nakeji haka bestie, haba Dan Allah kin kyauta kenan ba waya ba wasika kin barni a t
🏠