NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 74 of 136

Dan aminiyata da nayi rainonsa to nayi Masa Alkawarin zuwa idan zan tafi". Ita dai Zahra tunda ta kwantar da kanta a cinyar Inna maimuna Bata Kara dagowa ba, jinta a jikin innar sai takejin wani sauki da nutsuwa suna saukar mata. Gashin Kanta innar ta Dan shafa inda gashin ya fito tana Fadin shi dai wannan gashin baisan kitso ba Kullum Yana Nan a nannade kamar gammo". Dan turo Baki tayi tana Fadin "Ya zanyi kinsan ba kitsuwa yake ba ko anyi idan ya Dade kwana biyu ne kawai ga zafi". "Allah ya kyauta kawai dai 'ya'yan zamani Amma har yaushe za'a yita Zama da Kai haka? Yau Wai uwar taku tace meya samu wayarki ko an Kira Bata shiga? tasan ba rashin caji bane tunda ance Kuna da wannan abar Mai amfani da hasken Rana" Dan Jim Zahra tayi tace ya karbe wayar ai hakan be dace ba, Sai kawai tace. "Nima bansan meye matsalar ba kawai rufewa tayi taqi kunnuwa". Magaji ne Wanda yaketa faman cakular waya dago Yana fadin dauko mugani ko abun minor ne". "Bata gurina tana gurinsa ban sani ba ko dubawa ze bada ayi". "Shu wa?" Ya fad'a da sigar zolaya, banza tayi masa kamar bataji ba. Tashi daga jikin innar Zahra tayi tana Fadin Bari na dawo wlh murnar ganinki ta mantar Dani ko ruwa ban kawo Miki ba". Tayi gaba innar na Fadin "dawo Zahra'u nida ba bakuwa ba". Gaba tayi abunta. Saida ta ciko tray babba da dangin Zaki da sanyi har sauran pepper chicken din ta zubo musu, tunda ta aje innar ke binta da kallo tana jinjina abin wannan cimakar bata mai Karamin kafin bace ko ance gida tallafin qungiya ya samu har abinci ci susuka dauki nauyin bashi?" Ita dai shiru tayi Bata tofa ba Amma a kasan zuciyarta da maganganu fal Wanda zasu tattaunawa da 'yarta. Ware ciki magaji yayi ya kwashi gara har Inna na Masa Dan biki. Wayarsa Zahra ta barba ta Kira Ammah ta gaisheta itama abinda ta fadawa innar ta fada Mata game da wayar lokacin data sauke wayar harda share 'yan hawayenta, magaji Yana Mata tsiyar shatwabarta tayi yawa ita Batasan ta kusa Zama uwa ba,Inna na Taya shi. Sai da Innar ta Gama sannan ta tambayi Zahra. "Wai Ina Mai gidan nawa ne banji motsinsa ba tunda nazo?" Kafin Zahra ta lalubo abin fad'a magaji ya rigata Yana fadin. "Ai kin baroshi can a unguwar mu gashi nan suna magana da Ya Abdul Hakeem a kusa da masallaci har suka daga Mana hannu". "Awoh to ai kasan ban waye dashi ba sai a hankali". Nasiha Sosai da ban baki Inna maimuna ta Kara yiwa Zahra tare da kara jaddada Mata mashinmancin biyayya ga miji. Kaya Zahra ta zubawa inna a wata babbar leda harda atamfa dasu turaruka taba Magajin ya rike mata. ****** Tafiya ce miqqqqiya daga Azare zuwa Babban mutum ta Babura jihar jigawa, direban daya dauko Mama da Asabe ya Dan juyo yana kallon Asabe wadda ta maida hankali gurin cin doyarta da kwai da suka saya a kanya babba yace ",munzo Babban mutum fa Ina zamuyi kinyi shiru alhalin kece idona tunda wannan ba yanyata bace". "To na manta wallahi kasan da Dan Habu muke zuwa na zata shine ita dai Mama Bata cewa komai Dan niqab nema a fuskarta badan ta matsu da son ganin malam na bande din ba da ba yanda za'ayi tayi wannan kasadar Dan yanda ta fadawa Abban Itas/gadau zasu wata dubiya Alhajin yaso Bala direba ya Kaita ta nuna Masa da kawarta matar tshon Ambassador zasuyi tafiyar abinda ya Hana Bala direba kaita kenan, hanyar tinkin ta nuna Masa alamar Niger zasu shiga. "Yanzu ke Asabe a she Niger zamu shiga shi ne kikace min kauyen Babban mutum wlh da bani da takardar ecowas da Saida na zubeku ku nemi wadda zata karasa daku kinsan kuwa yanda suke da doka da order?". Tafiya ce miqqqqiya daga Babban mutum zuwa bande, sun Sami tarba Mai kyau daga yaran malam na ciki suna fitowa su Asabe suka shiga malam din yana zaune akan buzu da wani zabgegen carbi a hannunsa ya amsa musu sallamar su suka zauna suna gaishe shi. Asabe ya dago kai kalla. "Baki fad'awa Hajiya sakona ba?" "Allah ya taimaki malam na fad'a Mata cewa tayi na kawota gurinka tazo taji Koda yanda za'ayi lamuran ne suke neman canza fasali". Carbinsa ya Fara ja yana girgiza Kai yayi hakan kusan say uku kafi ya sauke wani dogon numfashi yana Kara girgiza Kai. Mama cikin kidimewa ta furta. "Da matsala ko malam?". "To da matsalar Amma Abu mafi ban mamaki shi yaron har yanzu bana ganin komai akan Lamarinsa kwata-kwata sai yau Naga wasu mutane a Kan lamarinsa da Kuma itama yarinyar an tasa ta gaba da dafa'i shiri Kuma na gasken gaske sai dai naga wata tafiya a gaban mijin nata da alama Kuma tafiyar da Alkhairi q a cikinta sai dai idan dauke hankalinsa za'ayi daga garin kwata kwata, idan ya tafi ya kasa ko tunanin garin bare ya dawo, idan ba haka akayi musu ba ba makawa sai kin Zama 'yar kallo a gidan dan duk yaran gidan Mata ba wadda tauraruwarta ta kama kafar tata da gaske haka Allah ya yita da madaukakin Alkhairi". Zuru Mana tayi ta kasa magana, maganar dai ita kenan Zahra tafi nata 'ya'yan. "Malam ayi duk abinda ya Kanata inda hali ma ya rattaba Mata saki kafin yabar garin". ""Abinda ban gani ba kenan a cikin auren nasu Dan Idan shi ne z
🏠