NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 72 of 136

lleta yanda yakeso ko? Matata take kaiwa Mai gadi abinci wannan wane irin zubewar aji ne a gurina? Dubi fa yanda ta fito? Ko baka gani ba?" Ya fada yana kallon Sameer. "Ni banga wani Abu na rashin kyautatawa ba a shigarta, kawai dai idonka wani Abu ya nuna maka na daban gaskiya". Hannunsa ya zare daga cikin na Sameer din ya bude kofar a hankali ba Kamar dazu ba zagayowa Sameer yayi ya rufe motar yabi bayansa Dan Idan ya Bari ya shige irin na jiya ze masa ya ajeshi a waje, kofar ya bude wani sanyi da kanshin girki Dana turarikan daki sukayiwa Sameer sallama Bata Nan sai tv a kunne ana karatun har lokacin. Direct gurin dining Sameer ya wuce yana fadin Bari na Fara da Nan Idan na gama ma gaisa tunda ba bako nake ba ya Fara budewa Yana kallon Mahmud Yana fadin. "Tab da alama Allah ya tarfawa garinki nono irin wannan delicious". Gaba Mahmud yayi Bai tanka Masa ba ya shige ciki. Kofar bedroom dinta ya kalla har dariya take bashi bilhaqqi da gaske tsoransa takeji bare Kuma da jiya ya Dan motsa mata Jamiyya. Ta Dan Dade a bedroom din nata daga baya ta bawa kanta kwarin Gwiwar ta fita ko banza bazata bada kofar da wani na waje ze gane da 'yar tsama a tsakaninsu ba Kar a Raina Mata wayo, fuskarta ta Dan Kara shafawa powder kadan ta Dan Kara fesa mouth freshner Mai kamshi apricot ta nufi kofa tana budewa saura kadan yau ma suyi karon, da sauri taja Baya. Shigar kananun Kaya yayi as usual dan zaman da sukayi ta fashimci kamat ya samu wani freedom ne na sakewa, trouser black da milk T-shirt ne a jikinsa hannunsa daure da agogo sai waya a hannunsa. Baya tayi da sauri tana Dan zare idanu Dan ba Karamin tsoro taji ba, Shima kallon ta yake Kamar ya rungumota ko yaji relief na abinda yakeji a zuciyarsa, amma sai ya share ya Mika hannunsa ya kamo nata ya natso da ita kusa dashi Sosai Yana Fadin "kin tashi lfy?". Ya shafi gefen fuskantar, cikin siririyar murya tace masa "Ina kwana? Shiru yayi Kamar beji ta ba, ya janyo ta suka Fara tafiya a cikin corridorn, sai da suka Fara gangara steps din taji yace waya Baki izinin fita gurin watchman din can?" Ya Dan matse hannunta dake cikin nasa. "Wash!!! Allah ta fad'a ba tare data shirya ba. Dan da gaske matsewar ta shigeta dago Kai tayi cikin narke fuska Kamar zatayi kuka dai dai lokacin Sameer ya dago Kansa daga daddana wayar da yakeyi Jin maganarta Sam beji tahowarsu ba wani irin perfect match couples ya gani sun masifar dacewa da juna ya Dade bega ma'auratan da suka burge shi kamar su ba, a zuciyarsa yake Fadin. "Masha Allah". Zahrar Tace masa. "Ba kowa, Dan Allah ka sakar min hannu wlh zafi...." Ta fada cikin shagwabar da Bata San tayi ba. Murmushi Sameer yake ta saki daga inda yake Dan ba karya yasan muhmud yayi dacen da Basu zata ba abun kamar a film yake ganinsa. Dan lokacin da suka Fara ganinta da Kuma furucin da shi Mahmud din yayi ashe Allah ya karbi addu'ar. Dan gyaran murya Sameer yayi Yana kallon Mahmud din tare da fadar. "Yallabai a bar madam ta karaso mu gaisa Mana ni ba mazauni babe gaba nayi daga Nan" Ya fada da sigar zolaya duk yaga har yanzu kamar Yana Jin zafinsa tun maganar da yayi masa na Safnah. Sassauta rikon hannaun yayi suka ida gangarowa directly dining area ya nufa yana zuwa ya ja Mata kujera ya zaunar da ita sannan Shima ya janyo ya zauna. Gurinsu Sameer ya karaso daga inda yake zaune Yana fadin. "Madam barka da Asuba kingan ni sai yau ki?". Ya fad'a yana Zama kusa da Mahmud. A kunyace ta amsa da "lfy kalau Ya Sameer ya kaje gida? Ina madam?" "Komai lfy ya hakuri damu?". 'yar dariya tayi kafin ta Mike ta Fara bude abincin Wani daddad'an kamshin ne ya doki hancin Mahmud har Saida ya lumshe idonsa, Dan kallonsa tayi sannan ta kalli Sameer tace "me za'a zuba?". Kai Sameer ya girgaiza Yana fadin "ai ni na riga ku ci tun shigowarmu naji bazan iya jiran masu gidan ba saina shide Ina jin kamshin delicious Amma ace saina jira". Ya fad'a Yana dariya.Dan murmushi Mahmud din yayi. "Wato ko Ina saika nuna halinka ko?". "Pls zuba min kawai". Kallonsa tayi kasa-kasa, tace "Toh" Masar dankwalin turawan ta zuba sannan ta zuba pepper chicken din ta tura Masa sannan ta zuba kunun Madarar sannan ta koma ta zauna a darare. Wani cup din ya zuba kunun Madarar ya dauko da fork ya matso kusa da ita da plates din abincin yace. "Oya saka hannu muci". Ya wani hade gabas da yamma alamun ba wargi Kai ta shiga girgaizawa alamar ta koshi Shima ture abincin yayi Yana duban Sameer. "Muje kawai" Ya fad'a yan Jan kujerar baya. "Zanci". Ta fada a gajarce. Komawa yayi ya zauna Yana fadin "fine tunda zakiçi gara Idan mutuwar zamuyi mu mutu tare Dan naga abinda Mata suke yayi kenan Idan aka Basu Wanda ba shine zabinsu ba su kashe shi su auri wanda sukeso". Tunda ya Fara Kora bayani Zahra tayi masa kur da ido tana Mai maita. Kai Sameer ya shiga girgaizawa Yana mamakin wani sabon hali da Mahmud din ya tsira, yaga alama nema yake ta Hana yarinyar Nan sakat. Ita Kuma tunda ta furta zanci Bata Kara tofa ko kalma daya ba, sai kawai ta dauki
🏠