NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 71 of 136

Story & Written by Maman Fatimah. 💎 Page twenty three 💎 (2 3) ________Zahra ba ita ta farka b sai gurin bakwai da rabi, sai lokacin ta tuna ta cewa Musaddiq ya fadawa Ammah ta bar kawo abinci zata dafa tunda ba komai take ba, toilet ta fad'a ta Dan sakarwa kanta ruwa Bata jima ba ta fito Riga da Wanda na Pakistan ta saka tayi rolling da gyalen ta saka plat shoes na daki ta nufi falo Amma zuciyar ta tana ta dar- dar kada suyi arangama da Dodon nata, falon ta shigo shiru sai sanyin A/C da daddad'an kamshin da yake ga curtains din duk a sake ga fitilu masu qarancin haske a kunne saiya bada wani irin yanayi Mai saka nutsuwa. Dan waige-waige ta Fara Kamar tana neman wani Abu gurin sai Kuma ta nufi gurin tv ta tsuguna tana hada socket din adapter din tv ta kunna ta kamo tashar Almajid, kokacin sun saka Qira'ar Muhammad Saddiqul minshawi a cikin suratul ISRA'I sai da ta dai daita volume din sannan ta nufi kitchen din a nutse da takunta Wanda da yawa suke ganin yangace da jiji da Kai alhalin ba haka bane naturally haka Allah yayi ta. Kitchen din ta shiga Kusan shigowarta ta uku Kennan, lokar da taga kayayyakin aikin ta bude ta dauko roba mai Dan Fadi ta nufi store ta debo Irish ta fito wanke shi tayi ta fere ta zuba a tukunya ta kunna gas, sai kuma ta dauko kaza guda ta yanka ta wanke ta zuba seasoning da spices ta rufe, ta jona egg boiler ta zuba kwai hudu a ciki. A gefe kuma ta dauko attarugu da Albasa ta yanka kananu ta aje a gefe Irish din ta Fara dubawa taga yayi ta sauke ta zuba a container Mai zurfi tasa fork ta murje ta dora frying pan ta zuba Mai kadan ta saya attarugu da albasar ta zuba a Kan irish din ta zuba magi da curry ta fasa ta yanka dafaffen kwan a ciki sannan ta fasa danye ta zuga ta juya ta aje ta duba kazar itama tayi Nan da Nan ta hada pepper chicken sannan ta jona tanda electric ta Fara zuba hadin Irish din Nan tana soyawa Kamar masa, tana gamawa tayi pepper chicken. Dora ruwa tayi a karamar tunya kafin ya tafasa ta dauko madara ta bude ta diba a wani bowl ta dama sannan ta dama corn flour a cup, jikin kitchen cabinets din ta tsaya tana bin karatun da yake shigowa daga parlour har sun kai suratul D'AHA. Madarar ta zuba taci gaba da tafasa sannan ta zuba corn flour din ta daure da yayi dai dai yanda takeso ta sauke ta Kara Masa condensed milk a cikin ta juye, hadesu tayi a babban tray tayi ta nufi falon, Nan akan dining table ta jero komai sannan ta koma ta dauko sauran tarkacen su cups. Kitchen din ta koma ta gyara gurin tas, sannan ta koma daki wanka ta shiga, tana fitowa ta shafa lotion dinta tayi simple makeup ta saka saka turarikanta na jiki dasu humra Nan da Nan jikinta ya shiga fitar da wani fitinan Nan kanshi, doguwar rigar Dubai Mai kananun stones pink mai duhu ta saka rolling tayi dan Vail din rigar milk colour sai ta fito balarabiyarta sak Dan idan ba kaji tayi maka Hausa ba bazaka taba cewa tasan ko zo da Hausa ba, tayi kyau matuka yarintarta ta fito sosai idan ka kalli fuskarta very cute sai wani annuri take fitarwa. Parlour ta fito gurin dining din ta nufa cikin takunta das das. Tana mamakin Ina ya shiga Dan ko motsinsa babu har yanzu ita kuma bazataje bedroom dinsa ba, idan ya gaji da zaman dakin ya tunda ba yaro bane yunwar cikinsa ta fito dashi. Kunun madarar ta zuba da masar Irish din kwara biyu kawai ta dawo main parlourn ta zauna tana ci tana sauraren karatun, sai da ta gama ta Kai kayan kitchen ta wanke sannan ta dauko Wanda ta zubawa baba Mai gadi ta nufi kofa a hankali take tafiya a cikin harabar gidan iskar bishiyoyin da sauran shuke shuken suna kadawa gwanin sanyi can gurin gate taga baba Mai gadin ya nufa da sauri da alama budewa zeyi.Dan tsayawa tayi daga gefe idonta Yana kan gate din Dan taji dirin mota zata shigo cikin kankanin lokaci motar ta shigo ido cikin ido sukayi da shi shine yake driving din gabanta ne ya bada ras ras Kuma ya kafeta da fitinannun idanunsa cikin gwaninta ya nufi parking lot, Sameer kuwa Kamar wani sakarai haka yake kallon zahrar Yana tsarkake suna Allah a zuciyarsa ya ganta har kusan hudu Amma da alama ganin tsoro yake Mata sai yau yaga zahirin zahrar, da sauri baba Mai gadin ya karaso yana gaisheta ta Mika Masa Dan Karamin basket din ta juya da sauri ta nufi kofar falon har Kamar tana dan sassarfa ta shige ciki, harta wuce idanun Mahmud suna binta Nan da Nan yayi kicin-kicin da fuska daman ga Sameer ya tabo shi ga itama da kalar nata shirmen, cikin zafin nama ya kashe motar ya Kama kofar ze bude Sameer ya kamo hannunsa ya rike Yana girgiza masa Kai kafin ya dungule dayan hannunsa irin na roko din nan yace. "Pls Dan Allah cool your temper kada kaje mata a haka kayi Mata uzuri Batasan Kai ko waye ba, Kuma infact ma laifinka ne ka tafi ka barta a gida har zuwa wannan lokacin Kuma tana ganin hakan da tayi shine dai dai koni nayi supporting dinta hakan shine dai dai ta nuna maka tasan haqqin abinda ka bar mata amana" . A Dan fusace ya kalli Sameer. "Nine na Bata amanarsa da izuninwa ta fito nan wato. ya ka
🏠