nyan kuloli sabbi Hajiya mama ce a kofar kitchen din na tsakar gida tana bada umarnin abinda za'ayi, yaran dake shigo da kayan ta kalla "wannan fa daga Ina?".
Magaji ne ya Bata amsa kafin yaron data tambaya ya fad'a Mata "tare muke Mama na abincin bakin Abba ne".
"Ikon Allah Naga ai an kawo wasu da sassafe dazu gasu nan har an kusa Gama aikinsu".
"Eh to shi dai yace a kawo wadannan ma".
Magajin ya fad'a Yana shiga dakin Amma.
"Kai dawa Kuma kake tafiya kana magana"
Cewar Inna maimuna.
Kusa da ita ya zauna Yana fadin "nida Hajiya mama ne kayan miya ne da Naman rago Dana kaji Abba ya Kara badawa aka kawo shine take magana ko yayi yawa kame?"
Dan murmushi Amma tayi "Abban Nan naku baya son a zauna lafiya wallahi magaji kamar zai aurar da Yara uku sai irin wannan shidima yake haka".
Kai magajin ya jinjina "Amma kenan kin manta yanda Abba keson Zahra ai kawai kowa ya zuba Ido ana auren uwar masu gida tab ai kowa sai yasan anayi Yasin, ki Bari kawai Ammah Nan zan kawo nama a ajiye min".
Ya fad'a Yana dariya ya nufi kofar fita saboda sallamar wasu Mata da yaji a kofar dakin.
___
Daki Mahmud ya koma ya samu Habib a tsaye a tsakar dakin da alama daga wanka ya fito, saida ya Gama wayar sannan ya kalli Mahmud.
"Wai ina kaje ne? Naga fitowarka daga gurin Baba Malam kafin na saka caji na nemeka na rasa, Bilya ne ya kirani Wai mu sameshi a hayin Banki shi Yana can yaje da masu aiki su duba yanda za'ayi gyaran"
Dan Dafe Kai Mahmud yayi ya Dan fesar da numfashi.
"Ikon Allah Wai Daman kamar jira kuke ace za'ayi min auren Nan kowa sai rawar jiki yake yi, daga fad'a shine har ya want kwashi jiki da masu aiki ya tafi tun garin Bai Gama watstsakewa ba".
"Naka wasa ne Alaji, aini yanzu haka mun Gama magana dasu Bashir sunce mun gasu Nan zuwa har suna cewa shegen zurfin ciki ne da Kai baka fad'a musu ba jiya ko kunya kakeji irin ta Mata".
Ya karasa maganar Yana dariya.
Har ya nufi gurin mirror ya tsaya "kaji na manta ba Salis yace na tura Masa cikakken sunan da ze saka a IV da zeyi a waya ya turawa friends na kusa".
"Ok ba matsala ka tura Masa kawai da sunan aika Sani ba saina maimaita make ba".
Misalin karfe Sha daya na safe wata bakar Hilux sabuwa kar ta dira a kofar gidan Malam Bukar.
Lokacin yaran sun firfito suna sugogin su masu wanki nayi masu wasa nayi Amma idan ba fada maka akayi bazaka taba cewa yaran Almajirai bane kowa cikin tsabta Kuma a lokacin anyi hutun makarantar book shi yasa basayi tunda suma tsarin makarantar gwamnati suke bi.
Mutane biyu be suka fito daga motar da sauri 'yan samarin dake kusa taso da sauri suna fadin barkan ki da zuwa kasancewar sun saba dasu sosai sune wadanda suke kawo musu tallafi daga organization din.
Da sauri suka bude musu falon saukar bakin Malam kafin wani ya shiga ya fadawa Malam din.
Ba jimawa Malam din ya fito suka gaisa a mutunce, sannan suka gabarwa da kayan abincin da suka kawo sannan suka gabatar Masa da bukatar daukar Mahmud zuwa wani taron karawa juna Sani na makarantun tsangaya Wanda za'ayi a kano, tunda shine Wanda suka dauka aiki a Nan tsangayar yake wakiltar su kuma gobe juma'a za'ayi taron na Rana daya ne kawai.
Dan Jim malam din yayi kafin yace " Ikon Allah malam Sameeru ga koshi ga kwanan yunwa WALLAHI shi Mahmudan dai baze Sami damar halartar taron nan naku ba, domin a goben in Sha Allah za'a daura Masa Aure".
Cikin wani irin madaukakin mamaki Sameer dake kusa da Malam din Kuma jagaban tafiyar ya kalli Malam Yana cewa.
"Aure! Kuma Malam?".
Kai ya jinjina Masa alamar tabbatarwa, "yanzu haka suna can gidan da ze zauna ana dudduba gyaran da za'a Masa duk da gidan Bai jima da kammaluwa ba kasan kullum abin duniya sabuntashi akeyi".
Kai ya jinjina ya hadiye wani yawu da kyar shifa duk ya shiga rudu meye hakan Wai Kuma.
Fara'ar dole Sameer ya kirkiro Yana kallon Malam yana fadar "Masha Allah Abu yayi Dadi to ai mu wannan lamarin namu ne munzo a dai dai kenan tunda Abu ne na ma'aikacin mu koma kunya zatayi Masa malam kada kuyi komai yanzu zanyi waya za'ayi duk abinda ya kamata tun daga abinda ango ze saka har abinda za'aci duk Yana karkashin kularmu tunda mu yakewa aiki, Kuma zamu zauna sai an daura auren damu in Sha Allah. Maganar taron Kuma sai dai a daga zuwa wani lokacin Dan bamaso wani yayi missing gaskiya".
Tunda Sameer ya Fara Kora bayani malam ke jinjina Kai saida yake Aya sannan ya Sami zarafin magana.
"To malam sameeru anyi haka abin fa da yawa kids bakuzo da Shirin wannan abun ba kunzo Kuma kuyi ya kuyi makarbiya ai da wahala abun".
Dariya Sameer din yayi Yana fadar "malam ba abunda ze gagara kungiyoyin masu karfi ne, yanzu ma ga wannan saboda biyan sadaki".
Ya aje Masa cheque na Banki suka Mike Yana fadar "Bari na Nemo shi a waya sai muje muji meye shirye-shiryen nasu, a huta lfy".
Suka kad'a suka fita.
_____
Kyakykyawan guri ne Aunty Hasana ta kama inda za'ayi mother's day din gurin ya kayatu ba karya kudi dai an kashe su gurin Kama event center din, anyi taron Mata 'yan gayu kamar ba gobe amarya tas