NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 68 of 136

Allah kiyi magana Kona Kira Aunty Hasana ne sai ki fad'a mata ko na Kira Miki Ammah". Kai ta girgaiza mata alamun a'a, "to ki fad'a min ko zan iya yi Miki wani abun Mana". Saida kukan ya lafa Mata sannan ta yunkura ta tashi zaune ido zulai ta zuba Mata ita ba yarinya bace kallo daya tayi Mata tasan da wata a kasa ganin yanda take a yamutsa ga labbanta sunyi jajir abinka ga farin Mutum ga gashin kanta duk gyaran ya turje. Zama tayi kusa da ita sai a lokacin taga gaban rigarta a yage Hannun bra dinta guda a tsinke. Kai kawai zulai ta dafa tana Fadin "mezan gani haka ni zulaihatu! Haba Zahra'u me yayi zafi haka ai sai kisa ya illataki a banza, gardama kika yi Masa yayi Miki haka?" Cikin shashhshekar kuka tace "A'a maganar Musbahu yake min shine ya Fadi Abu marar Dadi a kansa shine kawai Dan na mayar Masa da amsa Nima yayi min haka". Ta karasa fad'a tana kuka. Kasake zilai tayi tana duban zahrar kafin tace "Haba Zahra'u da wayonki da hankalin ki Zaki rinka irin wannan abun har yaushe Zaki ringa maganar wani namiji a gaban mijinki har kiyi ikirarin fad'a Masa magana marar Dadi akan shi ai yayi Miki kadan wallahi idan wani ne yau basai gobe ba saiyayi Miki kaca-kaca yanda ko sunansa ba Zaki Kara fad'a a gabansa ba, kada ki kuskura ki Kara irin haka Zaki ragewa kanki kima da daraja a idonsa, duka yaushe akayi daren da shashshawa zata Bata,Ina cewa jiya aka kawo ki amma ace an Fara da haka kinga abin baiyi kyau ba ko kadan, yanzu ki tashi ki shiga kiyi wanka da ruwan dumi zanje na cewa sahura kina wanka ne, mu tafi kawai tunda nasan halinta Abu kadan zata fara yaya tashi tunda nasan badan Allah ta biyoni ba dan Saida na fito harabar gidan ta biyoni. Sallam zulan tayi Mata Tana Kara tausarta akan ta ringa tauna irin maganar da zata ringa fada masa. Cikin karfin Hali ta Mike ta nufi toilet da gaske ya tsumama mata jiki ta jima a toilet din tana kuka maganganunsa sun Mata ciwo matuka har wani gori yake Mata Shima ba sonta yake ba, to an fada masa ita son nasa take har yake wani Mata wulakanci, ita ta rasa a Ina ta kuskuro ne take haduwa da fitintinu daga wannan sai wancan? "Astagafirullah". Ta fada a zuciyarta, alwala ta dauro ta fito ba wani kwalliyar azo a gani tayi ba duk ranta a cunkushe ga 'yar wayar da zata debe mata kewa ma ya dauke, a ranta tace "mugu kawai wani sumumu kasam dashi Kamar na Allah Nan kuwa dan duniya ne Mai lasisi". Tana cikin saka kaya taji karan bell alamun Baki a gurguje ta ida yafe gyalen rigar ta dan fesa turare tayi gaba. ***** Sai Bayan sallar magriba su zilai suka karasa gida dai dai lokacin Magaji ya fito da manya warmers a hannunsa sai Autan Ammah da basket a hannunsa Shima, zasu kaiwa zahra abincin dare. Suna shiga zilai ta wuce part din Ammah ta fada Mata sun dawo ita Kuma sahura ta nufi nasu bangaren sai da zulan ta shige part din sannan sahura tayi wuf ta shige sashen Mama. Salma kawai ta samu a falon tana kallon series na India ko arzikin amsa sallamar sahurar Bata samu ba sai wani kallon banza tayi mata tana Fadin "lafiya Kika wani shigo afujajun haka?". Kafin sahura ta samu zarafin Bata amsa Mama ta fito daga bedroom din ta tana Fadin Kamar maganar sahura nakeji?" Cikin azarbabi tace "nice Mama mun dawo". Ta fada tana Zama a kasa kan carpet. Cikin kwarewa da munafurci ta shiga korawa mamar bayanin abinda ta gani harta Kara da cewa. "Anya Mama yaron Nan kuwa Babu abinda yake boyewa kin ganshi kuwa? Gaskiya wallahi baiyi kama da fakiri Mai neman abincin yau da gobe ba, kayan abincin da muka zuba a store din wallahi ni wani abin ma ban taba gani ba hatta madara wannan manyan gwangwwnaye sunfi ashirin Nama kuwa na kaji kawai sun Kai hamsin Banda na rago Banda na shanu Banda kifi Allah Mama Saida muka cika freezer din cikin kitchen din ga lemuka da ruwa Kamar banza ga...... Bata Bari ta garasa ba ta daga mata hannu "bar shi kawai jeki zan nemeki". Mikewa tayi tana Fadin "a huta lafiya Bari naje nayi sallah naji ana Kiran insha'i". Ta fice. Tunda ta fita Mama ke jijjiga Kai tana kwafa, Sam hankalin salma na can gurin kallon ta Bata damu da abinda su mamar suke ba, Saida mamar ta Kira sunanta sannan hankalinta ya dawo Kan mamar tasowa bayi ta dawo kusa da ita tana fadin. "Mana menene Naga kamar ranki a bace,?". Tsaki tayi tana fadin. "Anya Abbanku da Asma'u ba ninkeni sukayi a baibai ba kan auren yarinyar Nan? ni daman tunda naga daga b'angaren Asma'u da 'ya'yan ta da 'yan uwa ba wata turjiya nasan da abinda suka taka bakiji labarin da sahura tazo min Rashi ba?". Kai salmar ta girgaiza alamar bataji ba, Nan Mamar ta shiga fad'a mata abinda sahurar ta fada Mata, Nan da Nan hankalin salma ya tashi ta shiga fadar "ai laifinki ne Mama Nan nazo na fada Miki naga wani inaso a gurin Baba Malam Kika dinga zagina duk yanda naso ki fashimceni shi ba irin wanda kike tunani bane ni naga abinda na gani Amma Kika shafawa idanunki toka kikaki saurarena ai gashi nan duk fafutukar ki ta tashi a banza ko yanda kika fada min gidan yake ai kinsan da wata a kasa".
🏠