r ya juya suka gaisa, kafin suka fita zuwa inda suke meeting.
Stepdown training zasuyi da school base management committee Basu tunda tsarinsu ya koma sun bin tsarin makarantun government ne sai kuma officially da suka gayyaci Mahmud zuwa gurin taron da zasuyi a Lagos nan da kwanaki biyar masu zuwa. Bayan Gama taron Sameer ya dauki Mahmud a mota suka fita hotel din suka nufa a hanya Sameer ya kalli Mahmud Yana fadin "yallabai meye labari naga text dinka komai an sawo zuwa anjima motar zata karaso amma sai nake ganin kamar kayi tafiyar nan da ita tunda zaka jima a can Kuma kaga duka kwanan ta nawa zaka tafin baka ganin abin ze iya Zama na surutu ko ace ma guduwa kayi amma dai ya kake gani?".
Dan Jim yayi kafin yace.
Tafiya da ita ba shine solution ba na dauketa na kaita Ina ko Kuma nace Mata wanene ni Nan nace Lagos zani can Kuma taga sabanin hakan ya kake tunani ka tuna fa she's educated, zatayi saurin gane komai ni kuma nafi son na Gina soyayya ta a zuciyarta ba tare da tasan who I am ba, I hope you understand?".
Kai ya gyada Masa alamar eh.
Sun Dade suna tsaya yanda program din ze kasance da abinda za'a batar da abinda za'a kashe a makarantar zuwa lokacin da zasu dawo suna cikin aikin direban daya dauko kayan ya Kira Sameer ya fada Masa ya shigo Azaren ya fada Masa inda yake tattara komai sukayi suka wuce gurin da direban yake, Sameer din ne ya shiga gaba direban na binsa a baya har zuwa gidan Mahmud din.
Mai gadi ya taya direban sauke kayan, kayan abinci ne da sauran tarkacen girki hatta nama da kifi daga can aka kawo kayane masu matukar yawa.
Ciki Mahmud din ya shiga tararwa ya yi tayi Baki har su zulai da sahura, a tsaitsaye suka gaisa yayi gaba zuwa bedroom dinsa.
Ganin idon su zilan yasa zahra mikewa tabi bayansa dai dai lokacin Kuma Yara suka Fara shigon kayan masarufin da aka kawo, ganin zahrar Bata Nan yasa su sahura shiga dasu store din kayan abincin suka hada da wanda Abba yasa suka kawo dazu da kayan gara su gireba dasu dublan da alkaki.
Sunyi mamakin yanda yara ke shigo da kayan abincin basu Kara Shan mamaki ba Saida aka Fara shigo dasu Nama da kifi ga drinks Nan ko ba'a fada ba Wai ance ido ba mudu ba amma yasan kima sun San kayan na manyan kudi ne, ko wacce da magana a bakinta Amma bata furta ba.
Zahrar na shiga corridorn ta waske zuwa nata dakin.
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨
✨✨
💎 PAGE TWENTY ONE 💎 (21)
...............…... Sai da su zulai suka gyara Mata komai yanda ya kamata sannan suka gyara parlourn,lokacin da Mahmud ya fito bedroom dinta ya nufa baiyi wani knocking ba ya tura kofar a gaban gado ya ganta ta cire bedsheet din ta zubo da pillows din da alama wani Abu take nema sallama yayi mata cikin muryarsa Mai nutsuwa yana kallon ta, cikin takunsa na cikakken namiji ya karaso Yana tambayarta "lfy me kike nema ne haka Kika birkita gurin haka?".
Jiki sanyaye tace Masa "wayata nake nema tun safe banganta".
Dan matsowa yayi kamar ze tayata dubawar Yana fadin "Kuma tun safe Baki ganta ba Kuma Baki nema ba sai yanzu, to su waye suka shigo dakin ne?".
"Shiru tayi kawai tunda tasan daga ita sai sajida ne a dakin Kuma tun bayan tafiyar ta ko Baki ne 'yan ganin daki Bata ahigo dasu Nan Dan gani take yaushe za'a dinga shigo da jama'a har dakin barcin mutum su dai dayan tunda ba a ciki take ba.
Dagowa tayi ta Dan kalli gefen shi da gani wanka yayi ya canza kananun Kaya tana mamakin sa ita tunda take ganinsa Bata taba ganinsa da shiga irin wannan ba Kullum manyan kaya ne Amma daga jiya zuwa yau ya zamar Mata wani daban, Sam ba wancen bane take gani.
Kamar ze wuce ta bayanta sai Jin Hannun Mutum tayi ya zagayo ta cikinta ya manna bayanta a kirjinsa ya kwanto da kansa dai dai saitin kunnenta iska yadan hura Mata kadan tare da hucin numfashinsa kafin yace.
"Ki daina wahalar da kanki tana gurina tun safe na dauka, nayi mamakin da baki nemeta ba sai yanzu? Na cire sim din saboda Naga wani sakarai ya kiraki da number din to nasan ze iya bibiyarki tunda naga bashi da taushidi ko kankani Bai hakura ba da hukuncin Allah so yake da karfi saiya kwato abinda ya kubce masa".
Kasa ko kwakwkwaran motsi tayi sanda yake jero Mata maganganun. Amma jin ya Kira Musbahu da sakarai marar taushidi yasa taji Zuciyarta ta wani baci, idan beji tausayinsa na abinda ya faru ba ai baze Masa bita da kullin irin wannan maganar ba, shida ya tsunci dami a kala har ya samu bakin magana irin haka. Nan da Nan taji ta samu wani courage wanda Bata San tana da shi ba, cikin muna bacin rai ta fara kokowar raba jikinta da nasa tana fadin.
"Wallahi Musbahu ba sakarai bane, ba Kuma marar tauhidi bane,dan ya biyo abinda yake halalinsa amma kasan dai Banda qaddara ba abinda ze rabani dashi, dashi muka tsara planning na rayuwarmu Amma lokaci daya ka rusa Mana budget din mu ka yarda da aurena da aka baka Kuma wallahi tunda nake dashi bai ko taba rike ko hannuna ba, amma Kai kuwa fa ranar Dana fara ganinka a duniya dame ka Fara min bada rugumata ba?" Kai kenan baka da aikin y