NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 65 of 136

Direct gurin mirror ya nufa ya zauna a Kan stool, Yana fadin "Bestien mu zuwa nayi muyi sallama naji Abdul Hakeem yana maganar Zaki wuce yau ko". Ya fada Yana murmushi, itama murmushin tayi masa tana fadar. ",In Sha Allah yau sai kano tunda Allah ya cika min burina Zahra ta shigo gidanta fine". "To mun gode kwarai Allah ya saka da Alkhairi sai munzo visiting idan madam zata dauki nauyin zuwan mu Kinga Nima sai Naga duniya ko madam?" Ya zubawa Zahra narkakkun idanunsa Yana Mata wani kallon qasa qasa. Shiru Zahra tayi tana yafa gyaren a kanta, Sajida ce tace "gaskiya Kam haka za'ayi". Tashi yayi ya Dan tako kadan zuwa gaban Zahra kamar ze hadeta da jikinsa da sauri tayi baya tana turo Baki yi yayi kamar Bai gani ba, envelope ya Mika mata Yana fadin ki Bata sskonta ne na jiya data Bari nayi niyya bazan canza ba sai dai idan bataso ta bayar, nizan shiga gurin su malam". A hankali tace "an gode madallah a dawo lfy". "Amin to bestie sai munzo ko". Bai jira abinda zata ce ba yayi ficewarsa. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana Zama kusa da Sajida Mika Mata envelope din tayi tana fadin "yaushe ya Baki kikace bakya so?". "Jiya Mana lokacin da zamu tafi sanda wannan jikar marokan ta zubar da darajarta ta rokeshi, yanzu Dan Allah me Hameeda ke nema? wane irin rufin asiri ne Allah Bai mata ba. Amma ta lalace gurin roko? shi yasa na aje masa kudin sa nayi gaba kayan ma nace bana so su rike". Dan murmushi Zahra tayi tana fadin "Saji danger wato halin na Nan ko? To nidai gashi nan tunda a gaban ki ya bayar saiki karba". "Bude mu gani to" Sajidar ta fada. Stalling founds ne na ingila musu yawa a ciki kallon kallo sukayiwa juna kafin Sajida tace wallahi bestie akwai kukus a shinkafa zakice na fada Miki, Wai kuwa kin tsaya kin Kare guyn nan kallo kuwa?". Kinga ya Miki Kama da Wanda baida abinyi ko wanda ya tashi a cikin rashin wadataccen ilimi da mugu? Dubi muhallin daya ajeki, ance malam ya bashi gidan sai kungiyar da yakewa aiki sukayi renovation din gidan ki kiyasta nawa yaci gurin aikin kinsan da an kashe abinda yafi kudin ginin duk yi Masa akayi? Ki tuna Nan fa ba garinsu bane ance bako ne kuma yaki fadin garinsu anyi magana ance yace ya manta komai sai a hankali idan ya tuna hankali ze yarda da hakan? Kuma kina tunanin Abba ze daukeki ya bashi ba tare da yasan wani Abu a tare dashi ba? Kiyi nazarin abin Mana ni dai ina fada Miki kibi komai a hankali kuma yanda na fashimci wani Abu a maganar da Kika fada min kinfa kamu da son guyn Nan tun sanda kuka hadu ba tare da kin sani ba, Kuma Shima Naga yanda yake shige Miki ko kunya ta Bai jiba kinsan sai a hankali kawai kwanan Nan labarin ze sauya irinsu basayi da wasa fa". Ta garasa fada tana dariya kasa-kasa. Suna cikin tattaunawa Kira ya shigo wayar sajida "Ya Abdul Hakeem ne" ta fadawa Zahra kafin ta daga. "To" Kawai tace ta kashe Kiran tana fadin. "To bestie ya Abdul Hakeem Yana jirana Wai a she shine ze Kaini nifa daya fada na dauka da Wasa yake lokacin da Ammah tace Magaji ko Malam Bala dureba zasu kaini sai kawai yace su Bari Shima Yana son yaje kanon Sai ya tafi Dani". Dariya Zahra tayi tana fadin "idan tayi wari munji batun, yanzu ba fa Naga Ya Abdul Hakeem Yana dama dama dake ba bai fada min ba Amma zakice na fada Miki Ina ga target dinsa kenan yau yake son ya yad'a manufarsa shi yasa yayi Riga malam masallaci yace Wai daman kanon zaya". Kin magana sajidar tayi sai murmushi kawai. Zahra tace "bestie ko dai komai ma ya kankama ne ban sani ba Ina shirme?". Kafin sajidar ta Bata amsa wani Kiran ya shigo da sauri ta dauki jakarta tana fadin "To bestie sai gani na gaba Allah ya bada zaman lafiya ya kade fitina, sai anyi ta hakuri kafin komai ya dai daita ki kwantar da hankalin ki zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah". Har gate ta rakata babbar ledar dake hannunta ta Mika mata tana Mata addu'ar sauka lfy. Amsa tayi tana Mata godiya ta bude gate din ta fita, ya Abdul Hakeem Zahra ta gani a mota a zaune cikin mamaki tace. "Ya Abdul Hakeem daman kana Nan waje Amma baka shigo ba?". Fitowa yayi ya karaso gurinsu Zahrar ta gaishe shi, sannan ta juya ta koma ciki duk zuciyarta ba Dadi Kamar ta Hana sajidar tafiya amma ba hali. ********* Mahmud Yana fitowa direct Famfon shanu ya nufa tunda lifan din Habib a gurinsa ya kwana, tun jiya daya karba da yamma Bai koma unguwar ba. Lokacin daya karasa yayi arba da motar Sameer wani murmushi yayi Yana fadin. "magulmaci kawai". Kafin ya shiga Saida suka dinga gaisawa da jama'a anata Allah sanya Alkhairi, Binya ya tambaya Ina Habib yace yaje Kai wani sako da malam ya tura shi ya Kai gidan sarki. Gurin Malam din ya shiga shi dasu Sameer ya samu suna magana da malam din Yana shigowa da sallama mlm din yace. "Yauwa Dan halak yanzu nake cewa bazaka jima ba zaka shigo, mutanen ku ne sukazo da wasu ayyuka gasu nan dai zasuyi maka bayani. Ya wajen iyalin naka!?" Dan sosa kansa yayi Yana Dan sadda shi qasa yace "Lafiya kalau tace a gaisheka" . "Masha Allah. Allah yayi Albarka" Gurin su Samee
🏠