NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 64 of 136

✨✨ AUREN HUCE HAUSHI ✨✨ ✨✨ 💎 PAGE TWENTY 💎(20) _______"ya Salam". Zahra ta fada a hankali jin yanda yake hura mata iskar bakinsa a fuskarta, yasa hannuwansa duka biyun ya tallabo fuskarta yana kallon face din very cute da ita, shifa baya gajiya da kallonta komai nata burgeshi yake yi Dan bakinta ya kalli 'yan kyawawan lips din ta pink, gdy yake yiwa buwayi Gagara misali daya mallaka masa ita a lokacin da bai taba zato ba, tunda ya kafeta da ido Bata yarda sun hada ido ba, ba Kuma tayi gigin dogowa ba. Qaran da door bell din tayi shiya kawo karshen 'yar tutsiyen da yayi Mata wani soft kiss ya yiwa gefen wuyanta Wanda har Sai da ta zabura tana fadin "wayyo Allah!". A shagwabe ta janye jikinta daga rikon da yayi mata, shi Kuma ya tashi ya nufi kofa, Bata jira taga waye ba tayi wuf ta nufi ciki jikinta kamar mazari. Tana shiga ta zube a gado tana fitar da numfashi da sauri da sauri kamar wadda tasha gudu, jin alamun bude kofar yasa tayi saurin duba gurin Sajida ta gani tsaye ta tsura Mata ido tana Mata wani kallo cikin mutukar tsantsar farin ciki zahrar ta taso tana fadin "haba bestie kin wani tsareni da ido kina min kallon qurillah irin wannan ko Kinga wani abu a jikina ne?". Ta qarasa fada tana karasowa kusa da ita 'yar madaidaiciyar ledar hannunta tana fadar "Wai meye Kika wani yi shiru kina kallona ne Dan Allah talk to me Mana pls". Biyo bayan zahrar tayi har gefen gadon kafin ta samu kuzarin fadin "Bestie Kinganki kuwa just one day Amma har kin Fara canzawa, Fadi min meye sirrin gaskiya, na tafi jiya da zulumin ki a Raina yau kuma nazo na sameki haka kin wani Kara Zama fresh dake". "Bestie tsakanin mu harda 'yar zolaya zakice Wai na Kara zama fresh?" Zama tayi gefen zahrar tana fadin "wallahi I am serious kin canza a idona gaskiya Kinga ai dole na fada ko?". "To shikenan kin fada bazan hanaki ba, wai da gasken yau Zaki wuce?" Kai ta gyada Mana kafin tace "In Sha Allah meya rage kuma ai gara naje na fuskanci karatun ko tunda na samu nutsuwa kin shigo gidan ki. Alhamdulillahi, ga sauran abubuwanki na wajen Baffan rimi kici baga da amfani dasu dazuma munyi waya da safe yace na bawa Ammah abinda ya Aiko dai ya Kara jardada Mata na a fada Miki kada wani ya kawo Miki abu kici Kuma yace a tura a karbo Miki sako Nan da sati daya". Dan langabar da Kai tayi tana Kara ganin kimar Sajida ta dauki matsalar nan tata bada wasa ba. Godiya sosai Zahra ta yiwa Sajida akan abinda suke mata, sun Dade sajidar na yiwa Zahra nasiha akan ta rike aurenta da kyau ita bataga wani abun ashsha ba gurin Mahmud idan. Nan da Nan idon Zahra ya kawo ruwa ta shiga sharewa da hannunta tana fadar "wallahi bestie na rasa dalilin da yasa nake jin wani abu a tare dashi tun ranar Dana Fara ganin shi naji abun ko kallonsa fa nayi sai naji gabana Yana faduwa heart beat Dina Yana karuwa, kinsan ma inda matsalar take?" Kai sajidar ta girgaiza tana fadar "sai kin fada". "Kinsan haduwar mu ta farko rungumeni fa yayi a cikin jirjinsa tsam kamar.wata baby amman Kamar an dinke min Baki na kasa ko fada Masa magana ne saima wani azababben kwarjini da yayi min harda fadar na ringa kula kada nayi musu asara'. Ai Sajida Bata San lokacin da wata dariya ta kubce Mata ba tana fadar. "Babbar magana kice da wata tsumammiya a tsakani ku tun tuni har kika dauki alhakina gurin hanani kwanciyar hankali tun jiya Allah barci ma ban samu na kirki ba Ina zulumin abinda kaje yazo, Dan ba kowa bane za'a aje masa mace kamar ke ya iya kauda Kai gaskiya" Wani duba zahrar tayi Mata tana fadin "ban Gane ba me kike nufi da maganganunki?. Wata dariyar tayi tana fadin "A'a ba mefa nake nufi kawai dai...... " Sai tayi shiru. Wani zancen ta dauko Tana fadin "Zahra ki tsaya ki nutsu a gidan aurenki ki gyale kowa duk wanda ze raina Miki miji kada ki amince ko waye kuwa Koda ni da nake Miki wannan maganar, Kuma game da Hameeda ki kula sosai Dan a jiya ta nuna Miki jiya ba yau bace, jini kuma yafi ruwa kauri, Koda ta dawo tana neman Kara shiga jikin ki da wata manufar tazo, Dan Allah kiba marada kunya duk yanda ake son ganin lapses dinki kada ki bada damar hakan". In Sha Allah zan kula nagode Bestie Allah yabar zumunci. Zahra ta fada "Ameen" sajidar na ta fada, suna cikin hira akayi knocking din kofar ba'a bude ba Zahra ce Mike tana fadin "ina zuwa, tana kokarin yafa gyale ta rufe gashinta Sajida ta warce ta aje gefen ta tana fadin "haba ke kamar matar liman a daki na da Bata ja ba tayi gaba saboda an Kara buga kofar, budewa tayi Mahmud ta gani Yana tsaye ya canza kaya ya saka Riga da wando na wani yadi light brown dinkin buda yana baza kanshi sa na ibada. Matsawa tayi daga jikin kyauren ganin alamar shigowa zeyi Amma fa Saida yadan shafi fuskarta kadan sannan ya ida ahigewa ciki, tsaye tayi tana binsa da ido tana ayyana "Wai meye ne yake faman shafa mata fuska har a gaban mutane ko kunya bayaji tasan wlh sarai Sajida ta gani sai dai ta basar kawai gashi ta wani rike mata gyale ta wani barta tsurarta".
🏠