NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 63 of 136

i be shigo ba shi be koma ba ya kafeta da idanunsa. Tunda suka hada ido dashi tayi saurin sunkuyar da Kanta jikinta na wata irin rawa duk ji tayi ta rasa yanda zatayi daga ita sai towel din Nan a jikinta, gashin ta saki ya bazu har gadon bayanta ta matse hannunta a kijinta, sun Kai kamar minti uku a haka Yana Kare Mata kallo son ransa a cikin zuciyar sa Yana tsarkake sunayen Allah da yayi Masa kyautar bazata da wannan kyakykyawar halittar dake gabansa a matsayin matarsa ta sunna halaliyarsa wadda ba wani shamaki a tsakanin su. Cikin takunsa Mai Cike da karsashi Amma a nutse, ya doso inda take tsaye Yana zuwa ba zato ba tsammani taji ya saka hannu Yana tattaro gashin daya bazu a kafadarta yana fadar "Bari na gyara Miki tunda Naga yana neman gagararki". Bata iya ce Masa komai sai jikinta daya cigaba da tsuma, tsab ya hade ya saka ribom din daya gani a kusa mayukan gashin brush comb ya saka ya Kara gyara shi sannan yayi baya a hankali ya zauna akan sofa Yana fadar "ki shirya kizo muje ki bamu break fast gashi can Ammah ta aiko tun wurin 7:30 su Musaddiq suka kawo". Bata amsa ba Kuma ta dago kalle shi ba, d'an gunguni ta fara kasa kasa "kawai ka zauna mun a daki kana kalleni kaki fita a gabanka kake son na saka kayan ko me?". Yana kallonta gefen ido tana magana a ciki baya raba daya biyu yasan complain take akan zamansa. Tashi yayi Yana fadin "idan kin Gama kiyi min magana Ina aiki ne". Ya juya ya fice. Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fadar "innalillahi ni Fatima Naga ta kaina Wai shi wannan waye shi? Nifa wallahi lamarinsa sun fara bani tsoro gaskiya" ta fada tana cuno Baki, sai Kuma tayi sauri har towel din jikinta na neman faduwa key ta sawa kofar, a gurguje ta saka doguwar rigar lace peach colour Mai touching din flowers green Bata daura Dan kwalin kayan ba saita rufa gyale green,Sam batayi wani make up ba powder kawai ta shafa sai lips glow turarenta ta fesa ta nufi kofa ta bude ta fice tsaye tayi a cikin corridor din saita rasa a wane bedroom din yake. Ta jima a tsaye tana saka yanda zata tunkari dakinsa Kai tsaye, cikin yin shahada ta nufi inda take zaton nan ne bedroom din nasa a hankali ta murda handle din ta tura kamar wadda za'a cewa ket ta ruga, wani sanyi da kamshin turensa Dana freshner ya shiga hancinta dakin ba wadataccen haske duk curtains din windows a sake suke can kan sofa ta hango shi da laptop a gefen sa yana ta faman daddanabawa tsaye tayi ita Bata shiga ba ita Bata koma ba, yana kallonta ta gefen ido Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. "Assalamu Alaikum". Ta fada a darare, Bai kalleta ba Amma ya amsa sallamar. Dan Jim tayi kafin tayi karfin halin cewa "na gama shiryawar". Kansa ya dago ya kafeta da idanunsa da yake razanata dasu kafin yace "idan bazaki shigo kije kawai an fada min Ina cinye mutane ne da Kika tsaye a nan". Dan cuno Baki tayi ta saki handle din ta shigo a nutse Amma fa Babu nutsuwa Kota sisin kwabo a zuciyarta ta ayyana "waya sani ko mayen ne tunda abune a duhu". A tsakiyar dakin ta zauna an carpet Kanta na kallon tace Masa "barka da Asuba". Shiru yayi kamar Bai jiba Saida ya Mula dan kansa yace "Lafiya ya kwanan bakunta I hope ba wani damuwa ko?". Kai ta gyada masa alamar eh. Yace "good Bari na karasa wani dan aiki muje muyi break ko?" Ya fada Yana kallonta. Ganin tayi shiru yasa yaci gaba da aikinsa ita Kuma tana zaune duk sanyin dakinsa ya Mata yawa, tana son sanyi amma sai taji na dakin yana neman ya sakata rawar jiki. Baifi minti biyar ba ya rufe laptop din ya Miki, gurin da take zaune ya nufo yana zuwa ya Dan tsuguna kusa da ita Yana fadin "taso muje kada nabar 'yar amanata da yunwa na amsa query a gurin su bestie ko?" Ya fada Yana murmushi. Hannunta ya kama ya dagota tsaye suna shakar numfashin juna Amma ita kanta yana duban kasa, dayan Hannun yasa ya dago fuskarta as usual yanda ya saba. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali Amma bata rufe idon ba kamar yanda ya hanata a jiya Bata manta ba amma ta kauda Kai gefe dan da gaske Bata iya had a ido dashi. Dan kwanto da ita yayi jikinsa Yana juyo da fuskarta yana fadin. "Wallahi kada ki rusa min budget dina kisa na kwashe kunyar nan daga idanunki tun banyi niyya ba matukar zakici gaba da irin wannan dabi'ar". Das das girjinta ya kara bugawa akan wadda yake, tana fadin "oh ni Zahra tawa ta sameni shi Wai wane iri ne haka? sai yayi ta sakin magana ko kunya babu". Saida ya matsa mata taci abincin kirki bayan sun Gama ne suka dawo parlor suka zauna Sam Babu sabo ko kalilan a tsakaninsu kallo ya kunna a Nile sat ya kamo super support suna kwallo live. Ganin ita ba wani gane kan ball din take ba yasa ta Mike zata koma daki ta kira Sajida taji ya maganar tafiyar Dan tun jiya da Abba yace a jiya zata tafi gidanta sajidar tace itama sai gida ta. Takunta biyu taji ya janyo ta ta fada jikinsa ba Shiri ta zaro ido waje hura kata iskar bakinsa yayi a fuskarta dalilin yasa ta rufe idonta kenan a hankali yace "Ina Zaki ki barni a zaune alhalin saboda na tayaki Zama yasa naki fita ko ina". ✨✨
🏠