NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 62 of 136

TEEN 💎 (19) AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu. Ina mika sakon jaje gan Alummar maiduguri bisa ibtila'in daya samesu na karyewar Alo dam, Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya Wanda Kuma suke gida da Asibiti Allah ya basu lafiya, abinda aka rasa na dukiya Allah mayar musu da ninkin abinda suka rasa. _______________Mahmud tunda aka idar da sallah Bai shigo gidan ba sai kusan karfe shida da rabi, ya Dan jima da Mai gadi kafin ya shiga ciki dakin Zahra ya nufa a kwance ya sameta akan sallaya da gani batasan lokacin da barci ya dauketaba yasan kusan kwanan zaune tayi, a hankali ya matsa daf da ita Yana karewa fuskarta kallo idanunta sun dan tasa alamun kukan da tasha da Kuma rashin barci, wayarta ce a gabanta a kunne tsugunawa yayi ya dauka Qur'an ya gani tana karantawa barcin yayi gaba da ita, baiyi tunanin tashin taba kada ya katse Mata barcinta. Kan stool na madubi ya zauna da wayar a hannunsa Yana dubawa haka nan yaji Yana son ya shiga ya duba received calls da missed calls nata, a hankali ya ringa bi Yana dubawa yawanci kawayenta ne sai Kuma Ummee da ya gani har ze aje sai yaga Kamar number din guyn da zata aura Dan lokacin daya tafi da wayarta ya canza mata wayar da sim card din a Nan ya haddace number din tasa sai Kuma yanzu daya ga Kiran jiya dai dai lokacin suka bar gurin Baba malam, Nan da Nan yaji ransa ya sosu duk da Kiran daga gurinsa ne ba daga gareta ba. Tashi yayi tsam yabar dakin da wayar a hannunsa shima kwanciyar yayi, can cikin barci yaji alamun ana Danna door bell da kyar ya tashi ya nufi kofa, Musaddiq ne da Faruq din Aunty Hasana suke kawo break fast cikin ladabi suka gaishe dashi ya amsa yana Basu hanya suka shigo da basket din dake hannun Musaddiq ya Dora akan dining table. Musaddiq ne ya juya ya nufi kofa yayin da Faruq yayi tsaye, har Musaddiq yakai kofar fita daga falon ya juyo Yana fadin "Faruq me kake jira ne ka tsaya? kasan driver Yana jiranmu fa".. "Taya zamu tafi bamu gaishe da Aunty Zahra ba?". Mahmud ne yace "Faruq Auntyn barci take sai dai zuwa anjima sai ku dawo kaji". *** Cikin damuwa da matsanancin tashin hankali Mama ta tashi, tunda garin Allah ya waye ta tasa kayan da Hameeda ta shigo dasu jiya a leda da envelope din kudin da mijin Zahra ya Basu a gaba ko bakasan kayan kwalliyar Mata ba kaga wadan Nan kasan ba Karabiti bane ga uwa uba kudin daya lafta musu ita abin har ya Fara Bata tsoro, dan a zahiri kowa yasan fakiri ne wanda Bai ajeba bai bada ajiya ba amma a badini abubuwan da yakeyi suna da ban mamaki. Wayar ta ta dauko tayi dealing din wata number ba'a Dade ba aka daga Bata koyi sallama ba ta Fara magana "Asabe kome kike kizo anjima da matsala babba komai Yana neman ya dagule fa kizo kiga abinda wancan tsintacciyar magen ya baiwa su Hameeda jiya harda fadin magana dan Hameeda ta fadin maganganun danace ta fada wallahi Ina kokonto akan lamarin yaron nan Dan jiya da dare Dana Kira malam na BANDE cewa yayi Wai mun kuskure wani abu shi yasa har Alhajin ya iya daura mata auren Kuma yayi duk iya yinsa ya kasa ganin komai akan mijin nata sai wani haske kawai yake gani". Daga can taji magansr mamar ta amsa da "hakane ba damuwa sai kinzo din ta aje wayar tana jan karamin tsaki ta tashi ta shiga toilet. A bangaren Ammah kuwa bayan Sajida da zulai sun Gama aikin break fast din da aka Kai gidan zahra, sajidar wanka tayi ta Shirya kafin ta fito falo su karya, bayan sun Gama ne ta kalli Ammah tana fadin "Ammah in Sha Allah yau an tafi gida Ina son na wuce school ne daman na jira ne saina raka Zahra gidanta tun last week muka Fara lactures". Ta fada a ladabce. "To Babu laifi hakan Allah yayi Albarka, sai Magaji ko Malam Bala wani ya Kai ki mun gode madallah, kunyi sallama da mutuniyar tun jiya kenan!" Ta tambaye ta. Kai ta girgaiza tana fadar "A'a sai anjima zan shiga muyi sallamar". ___ Zahra Bata tashi ba sai wurin takwas da rabi tayi Mika gami da salati tana Kara ware idanu tana kallon dakin da alama kamar ma ta manta inda take Sai a hankali ta dawo cikin nutsuwarta "ya Salam". Ta furta hankali tana ware sexy eyes dinta, wallahi Sam ta Manta da waifa a dakin gidan aurenta take ba a dakin Ammah ba, tashi tayi zaune kan sallayar tana Kara kallon Kanta har lokacin hijabin da tayi sallar ne a jikinta. Toilet ta shiga duk jikinta ya Mata wani irin nauyi Sam Bata jin dadin jikin nata ruwa Mai dumi ta hada ta shige ciki tayi kwance tana shakar kamshin turen wanka data zuba ta jima sosai a cikin ruwan kafin tayi wanka ta fito sabon towel ta dauko mai kalar purple Babba ta daura ta fito gurin mirror taje lotion ta dauko ta shafa a jikinta, tashi tayi ta nufi gurin wata jaka kayan gyarab gashinta ta dauko, zuwa tayi ta zubesu yanzu da a gida ne da Ammah ce zata gyara Mata tsab ta hade shi guri daya, tana kiciniyar daureshi taji alamun bude kofa da sauri ta kalli gurin, Mahmud ne cikin shigar kananan Kaya yayi wani irin fitinannan kyau, hannunsa ya nade a kirji ya jingina da kofar ya zuba Mata idon dake figitata, sh
🏠