NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 61 of 136

daman tasha kukanta. Sai yaji ta Kara bashi tausayi abun ne yayi Mata goma da ashirin. Cikin sigar lallashi yace. "To kici ko kadan ne saina kawo Miki magani kisha kinji" Ya fada yana Kara nuna Mata plate din da idonsa, kadan taci duk a takure shi har mamaki take bashi a yanda yake ganinta ai ta wuce ace tana jin irin wannan kunyar ko tsoron irin haka, tunda da gani wayayya ce ta ajin karshe, ga Kuma yanda ta ringa ta'ammali da samari kala kala, a yanda yaji labari fa sau uku ana fasa aurenta Wanda ba Wanda yasan dalilin hakan, yasan kawai rainin hankaline irin na Mata, yanda zamanin ya Zama abinda ya Zama Amma dai ai gaskiya zatayi halinta komai daren dadewa. Ba laifi ta danci tace masa ta koshi tana kokarin fitar da kwalla. A zuciya yayi yana jinjina saurin kukanta Kamar wata 'yar goye Sam yaga kuka ba wani wahala yake Mata ba, tana kuka tun abun kukan Bai Samu ba to idan ya samu yaya za'ayi kenan?. Kwashe kayan yayi ya fita dasu Bai jima ba ya dawo da p.c.m tablet a hannunsa da ruwa marar sanyi, farm fresh yogurt ya Fara zuba Mata ta karba Tasha sosai dan tana sonta sosai lokacin tana Jos har kamfanin take zuwa ta sawo musu, tayi Mata Dadi sosai sanyin moderate ba Mai cutarwa ba. Saida ya tabbatar da tadan samu relief kafin yace Mata. "Ki tashi ki canza kayan jikinki ki kwanta idan kikayi barci kan ze daina ciwon, in Sha Allah, Kuma na fada Miki tun kina Asibiti ki rage damuwa Bata maganin komai sai Karin matsala Amma idan Kika hakura komai Mai wucewa ne Zaki sameni fiye da yadda Kika tsammmata kiyi hakuri komai da Kika gani hukuncin Allah ne ba Wanda ya Isa ya canza idan Ina tunani akan kaina na duba yanda connection din ya faru nasa ba Wanda ya Isa ya tsara haka sai Allah Dan haka ki Barbi abinda ya Baki Koda bakya so kinda ance wani hanin ga Allah baiwa ne tunda gashi ya Baki Dan malami sukutum ai tsakaninki da Allah sai godiya". Ya fada Yana kafeta da idanunsa masu sakata ladabin dole. Kai kawai ta gyada Masa, ba baka sai kunne, mikewa yayi da cup da robar farm fresh din a hannunsa ya nufi kofa a hankali ya juya very lockly suka hada ido kashe Mata ido daya yayi Yana Dan murmushi Wanda Batasan Kona menene ba, sannan yace Mata "good night". Yaja kofar wasu sabbin hawayene taji Kuma ita harga Allah bada niyya ba jinsu kawai tayi hakika tana tausayin kanta, da gaskiyar masu iya magana da suke cewa cusa Kai ba kwarjini yawa ne yau ta gani ganin idonta Wai ita Amarya ce wadda zayati kwanan farko a gidan miji. "Ya illahiy!!! Wannan wace irin ranace haka? Yanzu da Musba.... Astagafirullah". Ta fada da sauri tasan tunanin wani irin haka haramun ne da aure a kanta. Ta jima a gurin tana sakawa da kwancewa Amma dai duk inda ta juya amsar daya ce aikin Gama ya riga ya gama sai hakuri da zubawa ikon Allah ido Dan shine alimil gaibi. Tunda Mahmud ya shiga nasa bedroom din ya kasa samun nutsuwa Banda yayi namijin kokari ya kauda kansa da lallai sai ya rage zafi gaskiya idan yayi haka baimata adalci ba. Dan shi a nasa bangaren kamai ya gama zamar Masa daidai, saidai ita uwar gayyar batasan wainar da yake toyawa ba dan idan da abinda shi Kuma Bai lamunta ba yayi Mata dole yafison komai Daren dadewa taso shi da muradin kanta yafi son ya koyar da ita yanda zata soshi fiye da kowane da namiji data taba so a rayuwarta, ba Kuma ya son tasan koshi waye bama ita ba kowa ma dake tare dashi a nan, yafi son ya Gina kanshi a gurinta a wannan matsayin na yanzu. Wanka yayi ya saka pyjamas dinsa farare sol nasu laushi, yana jinsa cikin watan irin nutsuwa, maimakon ya kwanta sai ya dauko laptop dinsa ya dosa aiki sai gurin biyu da kwata ya ture computer din ya tashi ya nufi kofa ya fita dakinta ya nufa dakin zahrar yana zuwa yana turawa yaji kofar a bude Kuma dakin da haske yayi zaton ko barci ne ya dauketa tabar wutar Mai haske a kunne. Yana turawa ya ganta akan sallaya tayi sujuda Amma shashhshekar kuka take Allah kadai yasan abinda take roko tsakaninta da mahalicci ya jima a tsaye kafin yaja Mata kofar ya fita jikinsa a matukar sanyaye dan ba karamin qima ta kara a idonsa ba ya Kuma Kara godewa Allah da yayi Masa kyauta da wannan yarinyar yasan Allah sami'uddu'ai ne yasha raba dare Yana rokon Allah ya bashi mace ma'abociyar addini, sai gashi a inda Bai taba zato ba Dan gaskiya Bai taba kallonta a wata mujahida ba yafi Mata zaton bokon ya rinjayi bangaren islamar ta. Koda ya koma shima Bai kwanta ba Saida yayi nafilfili sannan ya kwanta da tunani kala-kala a zuciya. Hudu da minti arba'in ya farka ka'idarsa kenan ta tashi sallar Asuba, wanka yayi ya saka jallabiya milk colour ya bude kofa har ze wuce sai yaga Bai Dace ba gara ta tasheta ta. Sanda ya tura kofar har ta Fara raka'atanul fajri ta Riga ta tashi, lallai ya jinnina Mata gurin ibada sai yaji ya qara samun wata nutsuwa a tare da ita da sauri yaja Mata kofar ya nufi falon jin za'a tada sallah.l ✨✨ ✨✨ 🔷AUREN HUCE HAUSHI 🔷 ✨✨ ✨✨ MAMAN FATIMAH 💎 PAGE NINE
🏠