makukar tana gurin Koda kuwa mamar ce, Amma yau Hameeda da bakinta Kuma a gaban idonta take fadar magana irin wannan, to meya canzata daga Hameedar data sani Mai sonta da kaunar ta da Bata kariya da kulawa a kowane janibi. Saida tayi Mai isarta har ta baiwa uku lada, sannan ta hakurkurta da Kanta ta tashi zaune. Kanta taji ya Sara Mata a hankali ta furta "Alhamdulillahi ala kulli halin. Allah na gode Maka duk abinda kayi nufi a gareni na karba ka bani ikon cinye jarabawar Nan dan isar Annabi Muhammad s.a.w.w".
Hannu tasa ta dafe Kanta dake matukar Sara Mata, wannan wace irin rana ce a gareta? ranar da duk wasu masoya keda tarin burika a Kanta Amma ita ranar ta ta farko ta kasance ranar cin fuska daga inda Bata taba zato ba, ba tarairaya duk burin da suka dade sunaci na irin wanna ranar ya tashi a banza. "Astagafirullah Ubangiji ka yafe min zunubina daya janyo min irin wannan rayuwar Mai tarin qalubale a cikinta".
Ajiyar zuciya ta sauke tana Kara dafe Kanta da gaske jinsa take Kamar ze rabe gida biyu, ba zato ba tsammani taji an bude kofa Bata daga Kai taga ko waye ba dan kamshinsa kadai ya Isa ya fada Mata Mai shigowar, Kuma ma waye ze shigo haka Kai tsaye a irin wannan lokacin, sallama yayi Mata Amma Allah baisa ta amsa Masa a fill ba ta dai amsa a zuciyar ta.
Takowa yayi a hankali har zuwa inda take zaune, har lokacin Kuma Bata daga Kai ta dube shi ba farar ledar dake hannunsa ya aje kusa da ita ba tare daya tanka Mata ba ya juya ya nufi kofa yana juya baya ta dago da sauri ta kalli bayansa kananan Kaya ne a jikinsa sabanin dazu da yake sanye da wani lallausan yadi fari tas da hula, sai taga Kamar yafi kyau yanzu akan dazun, kananun kayan sunfi karbarsa akan manyan da yake sakawa, hannun daya saka ya Kama handle din kofar idonta ya Kai taga hannun wani fresh dashi Kamar Mai rayuwa a kasashen sanyi. Ganin Kamar ze juyo ne yasa tayi saurin kauda Kanta Dan kada ya kamata da wadannan idanun nasa tana kallonsa. Kofar tabi da kallo bayan ya fice a hankali ta sauke ajiyar zuciya da gaske fa mutumin Nan yana Mata wani irin kwarjini, ga wani tsare gida naba gaira ba dalili da yake saiya karta Abu ya wani maze Yana Shan kamshi.
Karan bude kofar ne ya dawo da ita daga tunanin data shiga na wucin gadi, kusa da ita ya zauna daf da daf dan ji tayi Kamar numfashi daya suke sharing dashi, a hanakli yasa hannu ya dago fuskarta data Kama idon ta rufe, a zuciyar ta tace "na bani ni Fatima shi Kuma kome faskar Nan tawa tayi Masa? shi dai ya taba jikina kawai ya sani, muryar shi ta jiyo cikin deep voice yana fadin "Pls open your eyes and look at me mana".
Kai ta shiga girgiza Masa alamar a'a.
Shi abin nata ma mamaki yake bashi, a ranar da suka samu wannan arangamar da ita soron gidan Baba malam yaga ta rufe idanu ya dauka ko tsabar razanar zata fadi ne. Amman sai yaga abin na neman ya Zamar Mata jiki indai zata ganshi to kuwa sai ta rutse idanu Kamar taga wani abun tsoro, a haka zasu rayu da ita ai baze yuwu ba gaskiya dole yayi wani abun daze cire koma meye yake haddasa Mata hakan a tare dashi.
"Ok Ashe zamu kwana a haka kenan tunda bazaki bude idanun ba, ko Kuma wallahi na shayar dake mamaki yazun nan".
Shiru tayi Masa kirjinta Yana fat, fat da sauri kusancin yayi yawa duk ya kanainaye ta.
Batayi zato ko tsammani ba taji harshensa akan fata idonta Yana lasa yana busa mata iskar bakinsa kamshin Lister mint mouthwash Yana dukan fuskarta ciki Shirin fita hayyaci tayi baya da sauri ta fada kan gadon da baya idanun nata tar akan fuskarsa da yana mata wani Yana Mata wani kallon kasa - kasa nan da Nan taji tsikar jikinta tana tashi sai hawaye zurrr...
"Why! meyasa? Ai da sai ki barni na kwashe abinda yake hanawa kina kallon nawa Mana, oya tashi abinci zakici bazaki kwanta da yunwa ba kisa na Fara karya Alkawarin dana daukar Iyayena na kula dake,dan kowa amanarki yake bani da jaddadda min na rikeki da amana da gaskiya cikinsu harda bestien mu kuwa".
Ya fada a kasalance Yana kashe Mata ido.
Sai Kuma ya dan zamo kadan ya dauko plate Wanda ita Sam Bata San lokacin daya ajesu a gefenta ba, ledar ya bude wani kamshi ne ya doki hancinta Mai shegen Dadi kaza ce wani irin gashi akayi Mata Kamar na tsire da vegetables a ciki ya juye Yana fadin.
"Oya tashi kici kafin ki kwanta kinsan yunwar dare tana kawo ciwon ulcer,kada ta kamaki ace Ina barinki da yunwa ni d'an malam gara na Kara kiwataki duk wanda ya ganki ace Masha Allah! Kamar ba matar Almajirin Baba malam ba".
Ya fada da alamar zolaya a karshen maganar tasa. Itafa Yana Bata mamaki wallahi zata iya rantsewa idan aka saka Masa hannu a Baki baze ciza ba amma dubi yanda ya wani zage yana magana Kamar bashi ba.
Ganin da gaske zata Bata Masa lokacin shi Kuma Yana da abinyi da yawa yasa ya matsa sosai kusa da ita ganin Yana nema Kara mannata a jikinsa yasa tayi saurin tashi zauna tana kikkibta idanu tana kallonsa. Da hannu ya nuna Mata plate din, cikin Rashi kuzari a maganar tata tace Masa "na koshi bazan iyaci ba kaina ciwo yake".
Ta fada murya a shagwabe ga