NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 136

ara dubawa ta tarar da missed calls rababa Amma Sam babu nasa ko na wani daya dangance shi, duk na kawayen da abokanin arziki Bata bi rakansu ba ta shiga toilet wanka tayi, lokacin data fito Sajida ta Samu a dakin ta shigo Mata da breakfast dinta nan, tunda ta fito Sajida ke kallon ta har ta karaso gurin mirror inda sajidar ke zauna murmushi Zahra tayi Mata tana fadin "wannan kallon fa ko na canza Miki ne?". Kai ta gyada Mata "gaskiya Kam ba haka na Saba ganinki ba, meye yake faruwa ne? nifa tun jiya nake nema Deeni da wannan cussing din na Mushahu Aliyu, ta Aliyun tana shiga ba'a dagawa Amma su sauran wayoyinsu switch off". Da rausayar da kanta tayi tana Dan watsa hannuwa "wallahi bani da masaniyar me yake faruwa nima hakan take kamar ke Amma nasan dai kome aje ciki yau dole su shigo garin. Ni wallahi da Aunty Hasana zata yadda da an hakura da wannan mother's day din nifa duk abin ya fice min daga Rai gani nake shima wannan aure ba yuwuwa zaiyi ba nasan dole da wata a kasa ai ba haka muka tsara abubuwan ba Amma kin ko daya fa basuyi attending ba". Ta karasa maganar idanunta na cikowa da hawaye. Hannunta Sajida ta kamo ta rike tana fadar. "Hqba Bestie kada kiyi Kika in Sha Allah ba wani matsala sai Alkhairi kada ki Bata lokacin farin cikinki mana". Aunty Hasana ce ta shigo da sauri alamar wani Abu zata dauka turus tayi tana fadar "ke me zan gani Zahra kukan dai? haba you have to be very strong Mana kada ki yadda aga rauninki a kowane janibi ki Zama jaruma Mai iya fuskantar ko wane kalubale, kada ki kara saka damuwa a zuciyarki zan fita Amma in Sha Allah bazan Dade ba ki shirya kuje sama naji suna cigiyarki". A bangaren Mahmud kuwa bayan anyi sallar Asuba a masallaci ya zauna yayi azkar dinsa Saida gari ya Fara haske sannan ya fito lokacin su Malam sun Gama karatun da sukeyi da maza magidanta. Da sallama ya shiga falon nasa lokacin Abubakar Yana mayar da littatafan mazauninsu, sai da ya zauna sannan ya Dan rankwafa Yana gaishe da malam, Amma sai ya moko Masa hannu sukayi musabiha Yana fadin. "hakan shine sunnar Annabin Rahama Muhammad s.aw.w." Shiru falon ya dauka bayan fitar Abubakar Malam Bai tofa ba haka Mahmud shima, Malam ne ya kauda shirun "Ya ake cikin Mahamuda wace shawara ka yanke?". "Ba damu Baba Malam na karba na gode ayi min godiya Allah yasa hakan yafi Alkhairi". "Allahumma Amin. Allah ya Sanya Alkhairi ya Baku zuri'a Mai Albarka Allah yasa ace gara da akayi hakan" A zuciyarsa yake ta amsawa da Amin. Harya yunkura zai tashi Malam yace "koma ka zauna, Ina zaka bamuyi maganar inda zaka ajeta ba da sauran shirye-shirye". Sadda Kai yayi haka Nan yaji wani irin nauyin malam din ya taso Masa. Kansa Yana kallon kasa yace "so nake muyi shawara dasu Habib yanda muka yanke saiya fad'a maka". "A'a ba haka za'ayi ba nizan bada sadaki da kayan goro da alewa sai Kuma shaddoji da za'a kawo an jima Suma dinkakkune tunda abun yazo a kurace, sai Kuma gidan Nan na Hayin Banki mukullin na gurin Binya tun jiya na bashi nace yau zakuje a duba abinda za'ayi Masa". Mahmud kasa magana yayi shi wannan gatan har yayi Masa yawa komai anyi Masa. Rarrafawa yayi kamar yaro har gaban Baba Malam ya rinka godiya har Saida yayi Masa fad'a. ******** Amma ce da Inna a uwar dakin Ammar bayan dawowar Ammar daga bangaren Alhaji cikin tashin hankali Innar ta kalli Ammar tana fadin ke Asama'u wace irin magana ce wannan yaushe hakan ta faru duk bamu da masaniya?" Dan nisawa Ammar tayi. "Wallahi Nima ban sani ba Amma yace kada yaji kada ya gani naja bakina nayi shiru yana zargin kowaye yake lalata lamarin auren yarinyar Nan na kusa yake tunda yace min Malam Bukar ne yayi binciken Dan haka bazai cewa kowa komai ba har sai bayan daura auren tukunna". "Ya fad'a Miki waye mijin?" Kai ta girgaiza Mata alamar A'a. Nifa Ina gudun garin AUREN HUCE HAUSHI a kwaso bara gurbi Wanda za'azo ana Mana dariya". "Gaskiya bana tunanin haka Inna mu bita da addu'a kawai Allah ya Zama gatanta yasa albarka a ciki. 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️ Story & written By ✨MAMAN FATIMAH.✨ INA MIQA SAKON TA'AZIYYATA GA 'YAN UWANA HAJIYA MARIYA ALIYU ( JIMMAN ADO) HAJIYA BILKISU ALIYU (UMMA IKKI) HABIBA ALIYU (UMMA HABIBA) Na rasuwar mahaifinsu ALHAJI ALI DAN HAYA MAGAMA KAZAURE. Allah ya jikansa ya jaddadda Rahama a gareshi tare da sauran musulmi. Page three 🔷 📖🖋️ .............. Tunda Mahmud ya fito daga gurin Baba Malam yake nazarin yanda zai bullowa lamarin, baya son ko kadan a Sami kurkure, guri ya Sami nesa da makarantar kasancewar Alhamis ce Yara basa karatun safe sai ya zamana yawancin su suna dakunan su. Waya ya Ciro daga aljihun wandonsa yayi dialing din number Bata jima tana ringing ba kada daga magana ya Fara "kana jina Sameer sakon Dana turo maka kada a samu kuskure kayi kokarin ganin komai yayi yanda ya kamata fa". Dan Jim yayi alamun ana fad'a Masa wani abu "Ok to shi kenan take care". Ya kashe wayar. __ Nama ne da kayan miya ake ta shigo dasu cikin gidan da ma
🏠