NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 59 of 136

a tsaya a gurin kawai, su sajida ma rasa ta cewa sukayi shi kuwa uban gayyar wayar dake hannunsa ya aje Yana kallon Hameeda direct kafin yace " waya fada Miki Mai araha ce bakiji sunanta ba? Zahra fa kinsa ma'anar sunan kuwa? tauraruwa fa a cikin taurari a gurinki take Mai araha Amma ni a gurina tafi zinari daraja, bari na baku indai abin sayen Baki ne in dai shi ne abinda ke shaida Kima da darajar mace a irin wannan ranar gurin kawayenta, ina zuwa". Ya fada Yana mikiwa ya nufi hanyar bedrooms dinsu, tunda ya wuce zahra ta juya da sauri ta nufi daki Bata yi musu ko sallama ba. Bai jima da shiga ba ya fito da wata katuwar leda da Kuma envelope guda uku a hannunsa. Yana zuwa directly Hameeda ya nufa ya Mika Mata ledar da envelope daya sannan ya baiwa Sajida da Mujiba Suma dai dai Yana fadar "ga kayan sayen bakin Nan a cikin wannan envelope din Kuma kunsha ruwa a hanya". Ba kunya Hameeda tace yanzu naji magana ai shi tuwon girma miyarsa Nama mun gode". Taja katuwar ledar tayi gaba abinta mujiba ma tabi bayanta har suka fita Sajida Bata motsa ba ita kollon ikon Allah take akan Mahmud Wai wannan shine Almajirin da ake ta yayatawa a aurawa Zahra har Hajiya Mama na yiwa Abba magiyar kada ya Fara wanna danyan aikin tab wallahi da sake ita tafa abinda ta gani ga tare dashi ai da hasashe ne take yanzu be taga zahiri. Ganin sun fita yasa sajidar aje Masa envelope dinsa a gefen shi tana fadin "kabar abinka na gode, ni fatana ka rike min bestie da mutunci da amana yafi ka bani duk abinda ka mallaka, bansan Kai ko waye ba Amma jikina Yana bani kana boye wani Abu tun lokacin Danazo gidan nan da Kuma irin kayan danaga an kawowa bestie nasan Kai ba kaskantanccen mutum bane, Ina hadaka da girman Allah kada ka bautulcewa Iyayenta da suka baka ita kaji tausayinta marainiya ce, Dan Allah nasan duk inda ka fito ba karamin guri bane ka Zama garkuwarta ka zamar Mata bangon da zata jingina taji dadi duk rintsi. Dan Allah ka Bata kulawa Zahra 'yar gata ce kaddara ce ta zaunar da ita a kasar nan da Kuma kawaicin kakanninta suka hakura suka barwa Ammah ita, Dan Allah ga amana Nima na baka kamar yanda iyayenta suka baka kaji tsoron Allah a cikin zamantakewar ka da ita na San Nan gaba zaka samu zabinka ko Kuma tuntuni kana dashi Dan Allah kada ka wulakanta ta.. na rokeka ka Zama adalin shugaba a gurinta idan kaji yanda rayuwa ta dunga jujjuyata zaka tausaya Mata matuka, Dan Allah badan niba...." Da tayi gaba ta nufi kofa Bata taji me ze fada ba domin hawayene suka ciko Mata idonta idan tace zataci gaba da magana kuka zata fasa masa ne. A bakin kofa sukayi kicibus da Mujiba wadda ta dawo kiranta ganin shirun ya yi yawa. ✨✨ ✨✨ AUREN HUCE HAUSHI ✨✨ ✨✨ 💎PAGE EIGHTEEN💎 STORY AND WRITTEN BY MAMAN FATIMAH. _________ Bayan wucewar Sajida Mahmud ya Dade Bai tashi ba, kwarai yarinyar ta burge shi matuka, da gaske take son Zahra domin furucin da yarinyar can tayi yayi touching dinta sosai, lallai ya tabbatar son da take yiwa Zahra bana Wasa bane shi tun lokacin da Magaji ya fada masa ta baro syprus Dan kawai ta halarci bikin zahrar ya jinjina Mata duk da suna hutu Amma yasan irin wadannan daliban ba kowane hutu suke zuwa gida ba sai dai idan iyayen sun sunci sun tada Kai. Envelope din data aje masa ya kalla yayi wani killer smile ya zurata a aljihun Wando Yana Kara wani murmushin Wanda shi kadai ya barwa kansa sani. Yaso ya shiga dakinta sai ya share kawai Dan yasa baya raba daya biyu kuka take Dan da gaske koshi baiji dadin furucin da akayi Mata ba Kai tsaye bako rusunawa a ciki. Lokacin da Abdul Hakeem ya Parker motar a parking lot na gidan Sajida ce ta farkon ficewa daga motar zuciyar ta na Mata wani zafi Dan da gaske idan ta tsaya zata shatawa Hameeda rashin mutunci ne na karshe Wanda zata Dade Bata manta ba, dan da gaske an shirya ne kawai dan a tozarta Zahra a gabanta mijinta, shi yasa kenan lokacin da zasu ltafi ta shiga part din Mama Kiran Hameedar akan ta fito suje, taji Salma na fadin saura Kuma ki kasa fada ki dawo Mama ta tumurmushi banza, ita Sam Bata kawo komai ba kawai dai ta dauka wani abune can tsakaninsu saida hakan ta faru ta Gane me ake nufi da waceccen maganar. Tana jin Mujiba na kwala mata Kira lokacin data nufi karamin gate wanda ze sada ta da cikin gidan, batabi ta Kanta ba tayi wucewarta ciki ta kyalesu. Koda ta shigo part din Ammah directly bedroom din da suka kwana ta wuce tana yiwa su Aunty Hasana sannu har ta shiga ta fito tana fadin "Aunty Dan Allah idan su Hameeda sun shigo kice su raba kayan su biyu kwai Banda ni". Ta koma da sauri Dan tana jiyo maganar su a kusa alamar Nan suka nufo. Tun shigar Zahra bedroom din Nan ta kwanta rub da ciki take risgar kuka Kamar ba gobe, Hameeda ta Bata mamaki Bata taba zaton irin wannan ranar ba a tsaknainta da Hameeda cewa take ko kowa ya nuna Mata naqi a bangaren Mama ita kadai zata tsaya a bayanta duk runtsi duk wuya saboda a baya ba Mai cin fuskar ta a dakin Mama
🏠