NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 58 of 136

u kenan? haba kiyi hakuri Dan Allah ki share hawayenki wallahi nasan yanzu zuciyar masu binki da mugun nufi tana can kamar zata fashe Dan ba haka suka soba duk da bansa daga Ina matsalarki take ba, ai kodan makiya kin kwantar da hankalinki ki rungumi mijinki ki ba mara d'a kunya, Amma kin tsaya kina wani Abu kamar wata karamar yarinya" Tayi tsaki tana kallon zahrar da tayi kozai kozai ido ya kode Mata abinka da farin mutum. Suma su Hameedar ban baki suka dunga yi Mata, da kyar ta hadiye kukan ta kallesu tana fadin "wallahi bazaku Gane bane ni kadai nasan me nakeji, komai ya kwance min Sam duniyar bata mun dadi". "Hakurin dai zakiyi ki Kuma yawaita addu'a in sha Allah komai ze wuce kamar ba'ayi ba, muda muke son next year by now mu dawo suna". Sajida ta fada tana murmushi. Wani kallo zahrar tayi Mata ta juya kanta gefe tana fadar "Allah ya kiyaye min wata haihuwa can". Mujiba ce ta kwashe da dariya tana fadar "A'a Banda cika Baki dai 'yan Mata Nan da labari yasha banban zamu tsinceki kina faman 'yan amaye amaye, lokacin ne Zaki gane Baki da wayo ko ba wata haihuwa can ba?". Zumburo Baki tayi tana fadin "sai kiyi Kuma haka kawai Zaki jaza min, wani ciki ko dadin fada ma Babu". Saima zahrar ta zame ta kwanta, tana jinsu suna ta faman zolayar ta har aka Kira sallar insha'i a Nan sukayi sallah kafin su shiga Kara gyara Mata Fallon da Kara masa freshner da turaren wuta Hameeda ta Kara karfin A C a falon ta gyara cutains din, bedroom din data fito suka shiga Mujiba bakinta ya kasa shiru tunda dai suka Samu zahrar ta daina 'yan koke koken sai ta balle da santin gidan Dan bayan sun idar da sallar ba inda Bata shiga ba ta leka can ta shiga can bedroom din Mahmud ne kawai Bata shiga ba tunda a rufe yake, fada take "wallahi zahra ki Kara godewa Allah, irin wannan haduwa haka wallahi ko makiyi Saida yaki fada Amma dai duk wani gata kin same shi sai dai fatan zaman lafiya kawai". Ita dai Zahra ba baka sai kunne.Dan ita kadai tasan abinda ke Kai komo a zuciyar ta, su inda suka dosa daban ita inda ta dosa daban, ko tayi musu bayani ba ganewa zasuyi ba, domin su duka ba wadda ta tab'a shiga irin gararin data shiga, rayuwa Rumi rumi saika Gama sakankancewa da mutum Rana tsaka Abu ya lalace, uwa uba ganin da tayiwa Musbahu ba karamin famu yayi Mata ba, saboda da ta cire shi daga ranta kwata kwata ta hakura, Amma tana ganinsa komai ya rikice Mata da tana zargin kamar da niyya mamansa tayi haka saboda ya taba fada mata Maman nasa taso ya auri 'yar Yayarta shi Kuma ya ringa sharewa ana haka ne Allah ya had'a shi da zahrar abinda ya kawo karshen wancan dambarwar kenan. Amman tasowar mamansa da 'yan uwanta dashi kanshi takanas ta kano har Azaren don bada hakuri da neman gyara idan lamarin Mai gyaruwa ne, sosai abin ya tashi hankalinta, wata sabuwar soyayyar sa ce ta sake bijiro Mata idan tana tuna yanda yaci buri a irin wannan ranar da za'a kawo Masa ita a matsayin matarsa ta sunna halalinsa, irin abinda yake fadin ya tanadar Mata ita a wancen lokacin idan Yana fada kamar zata nitse kasa dan kunya Amma shi ko a jikinsa. Wasu sabbin hawayene suka zubo Mata masu zafi tana ayyana shike nan komai ta Zama tarihi, ga inda kaddara ta kawo ta gurin da ba'asan darajarta ba ko alama sai aukin taba Mata jiki da yake Wanda ta fashimci hakan tun haduwarsu ta farko, ba kunya ya wani saka hannu ya rungumota Wama ya sani ko Dan duniya ne aka hadata dashi, tunda ance ba Wanda yasan asalin sa kuma tasan yanda yake din nan ko bashi da sisi mata zasu ringa kawo Masa rida tunda sun ganshi smart dashi. Wani tsaki tayi tana ayyana to Ina ruwanki da wani smartness dinsa. Mahmud Bai dawo gidan ba sai bayan sallar insha'i ganin takalma yasan akwai baki cikin gidan baya raba daya biyu 'yan uwanta ne ko kawaye, dakinsa ya wuce yayi wanka ya canza kaya ya fito falo, bai shiga dakinta ba daga inda yake yana jiyo mganganun bak'in, ita dai baiji tata maganarta ba Sam Zama yayi yana daddana wayar hannunsa. Acan Kuma dakin Zahra Ya Abdul Hakeem ne ya Kira wayar Sajida Yana fada Mata su fito su tafi ya dawo daman lokacin daya basu kenan bayan sallar insha'i lokacin daya kawo su. Sun fito falone suna zolayar Zahra Basu kula da mutum ba sai da suka sauko daga steps din da ze sada ka da corridor din bedrooms din suka ganshi a zaune Yana ta faman Danna waya, kallo daya Zahra tayi Masa ta kauda Kai haka kawai taji gabanta ya fadi, ta rasa wace irin masiface wannan. Kansa ya dago yana amsa gaisuwar su Sajidar Yana fadin "har zaku koma ne?". Hameeda ce tayi farat tace "To ba dole mu tafi ba yallabai tunda angon yaki zuwa ya sayi bakin amaryarsa ba Yana ganin Mai araha ce bai Sha wahalar komai ba aka bashi ita". Ba Zahra da aka ciwa fuska a fakaice ba hatta Sajida da Mujiba Saida sukaji kamar kasa ta nutsa dasu a gurin Dan kunya, gaba daya suka zubawa Hameeda ido har shi uban gayyar, wani abune Wanda Zahra Bata taba tunanin Hameeda zatayi Mata ba, dan wannan cin fuska ne qarara bako kawaici a cikin maganar ko kad'an. Zahra kasa gaba ko baya tayi t
🏠