duk inda yanayin rayuwa ya kaiku na baka ita ne saboda na yaba da nagartarka na Dade Ina monitoring dinka ban tabaji ko ganin abun ashsha ba a tare da kai, kullum addu'ata Allah ya bani ikon sauke nauyin marainiyar Allah dake hannuna, kuma Alhamdulillahi na sauke gata nan marainiya ce Bata da uwa Bata da uba ba wa ba kani ita kenan iyayenta duka suka rasu suka barta, kada ka zalunce ta Dan girman Allah ka tausaya Mata saboda Mai rauni ce, ka zamar Mata uwa uba abokin Shawara kuyi dariya tare kuyi kuka tare ka jibinci lamarinta gwargwadon iyawarka. Ina Kuma Kara gode maka bisa share min hawayena da kayi baka watsamin kasa a ido ba lokacin Dana baka aurenta, na gode kwarai Allah ya saka maka da Alkhairi ya yaye maka damuwarka ya kawo maka mafita a bisa lamuranka".
Suka amsa da "Amin"
Sannan yaci gaba da fadin "ke Kuma Uwata ga mijinki nan kiyi Masa biyayya abisa abinda Bai sabawa Allah ba, ki girmamawa shi ki kiyaye bacin ransa ki kiyayie mutuncinsa da rike Masa sirrinsa kindaraja mas iyayensa da 'yan uwansa lokacin da Allah ya hukunta ku hadu dasu,nkiji tsoron Allah a cikin zamanta kewarku ki saka hannu ki Barbi duk abinda ya biyo bayan aurenki dashi Mai Dadi ko sabanin hakan. Dan Allah ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri da abinda Allah ya hukunta a kanki komai Kika gani rubutacce ne daga Allah sai dai mu 'yan adam mu karasa shi, Amma tun ran gini tun ran Zane dama haka kaddarar take, ko shi mijin naki idan yayi nazari zega wata kila wannan kaddarar auren ce ta rabo shi da asalin inda yake, to Dan haka kowa ya rike tasa kaddarar wata Rana sai labari komai na duniya Yana da iyaka ikon Allah ne kawai bashi da karshe, Allah yayi muku Albarka ya kauda fitina a tsakaninku ya tabbatar da Alkhairi a cikin rayuwar aurenku, Mahmud sai anyi hakuri da Mata su masu rauni ne kwarai da gaske".
Tunda Abba ya Fara magana yaji kamar ya dauko wani gaigimemen dutse ya Dora Masa aka.
Cikin ladabin da baisan Yana dashi ba ya furta "in Sha Allah Abba ba wata damuwa Kuma amana na karba na rike Allah ya bani ikon saukewa nike da godiya Allah ya saka da Alkhairi ya Kara Nissan kwanaki masu Albarka"
"To Masha Allah, Abdul kayi Mana addu'a mu tafi kada almuru tayi Mana a nan, Uwata ki daina kukan Nan haka bana sonsa kiyi hakuri kowa da haka ya girma Allah yayi Miki Albarka, ga makullin motarki wadda mukazo da ita takice na sai miki, kudin dayar ta wajen Abbie suna gurin Alhaji muttaka tunda aka sayar da ita nace ya juya Miki kudin zuwa lokacin da za'a bukaci wata motar Dan haka in Sha Allah cikin sati Mai zuwa za'a kawo Miki dayar ma".
Suka tashi suka fita Mahmud yayi musu rakiya har gurin mota Saida suka tafi sannan ya dawo ciki, a inda ya bar zahrar anan ya sameta ta kwantar da kanta a kan cinyoyinta tana kuka Mai tsuma zuciya a hankali ya zauna kusa da ita yasa hannu ya dago kanta daga jikin cinyoyinta idanunta a rufe sai tsiyayara da ruwan hawaye suke. Ba zato ba tsammani kawai taji ya sakata a girjinsa ya kwantar da kanta ya saka hankici Yana share Mata hawaye, daya hannun Kuma Yana tapping din bayanta kamar yanda ake yiwa yaro idan ana so yayi shiru Yana kuka, jikinta gaba daya ya dauki rawa ta taso da niyyar zare jikinta Dan wani Abu takeji duk ilahirin jikinta Amma Dan bawan Allan nan yayi kememe yaki sakinta ba arziki ta hadiye kukanta, sai sauke ajiyar zuciya kawai ba kakkautawa saida ya tabbatar ta Samu dan nutsuwa sannan ya saketa Yana fadin " sorry Baby ki daina kuka bana son kuka Sam koda kuwa na karamin yaro ne".
Hannunta ya Kama ya mikar da ita ya nufi daya daga cikin bedrooms dinta guda biyu da suke mallakinta, Saida ya zaunar da ita a gefen makeken gadon sannan ya juya ya nufi kofa Yana fadin " it's time for prayer"
Ya fice Yana ja mata kofa.
Sai ta dauki kusan minti biyar kafin ta Samu kuzarin warware Laffayar dake nannade a jikinta, doguwar rigar material ce a jikinta anyi Mata dinkin fitted gown tayi Mata kyau sosai kofar data gani ta nufa tasan toilet ne, lokacin data shiga abin ya girgizata irin kayan amfanin data gani a ciki ita ba bakuwar abin bace tasan ba kananan kudin aka narkar ba a cikinsa, abin ya Bata mamaki sosai sai dai wa zata tambaya? ta Jima a ciki kafin ta dauro alwala ta dawo dakin.
Ido ta ringa wurgawa ko zata ga sallaya tunda ita dai bakuwa ce a dakin can gefen sofa taga wani stool kamar coffee table da sallayun akai ta shimfida ta Fara sallah.
Tana cikin sallah ne taji kamar karar door bell kamar sau biyu, Saida ta idar ta tashi ta fito har lokacin tana share hawaye jefi- jefi, gurin kofar ta karasa ta bude Sajida da Hameeda da Mujiba ta gani ai batasa lokacin data fada jikin Sajida ba tana dakin kuka Mai tsuma zuciya.
Ciki suka shigo Sajida na fadin "haba bestie wallahi Dana San har yanzu baki daina kukan Nan ba da bazamu biyo bayanki ba, haba Ashe bazaki karbi kaddara yanda tazo Miki ba? ki Kuma godewa Allah a kowane Hali Kika Samu kanki, bake Kika halicci kanki ba ballantana ki tsarawa kanki yanda Zaki rayu, kin taho kina kuka duk kin dagawa Ammah hankali itama, kin kya