a abun ya Kare sai Kuma ya canza salo akan mahaifiyar ka, kayi hakuri ka fawwalawa Allah komai shi ze baka wadda tafi Zahra daman Allah hukunta kai ba mijinta bane ayi hakuri".
Kansa Yana kasa tunda ta Fara maganar wani Abu ya tsaya masa a makogwaro yaji Sam ya kasa magana sai Aliyu ne ya amasa da "ba komai Mama haka Allah ya nufa, Allah ya Basu zaman lafiya mu zamu koma".
"To Allah ya tsare ya baka mace ta gari wadda zata maye maka gurbin Zahara'u" Inna ta fada ita kuwa Ammah kasa magana tayi dan da gaske yaran tausayi suke Bata sun kwallafa Rai da juna Amma akayi musu karan tsaye, a zuciyarta ta ayyana "Allah ka biwa yaran Nan hakkinsu duk Mai hannu a cikin Bata lamarin Nan kayi Mana sakayya da gaggawa Dan isar Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w."
Ta window zahra ta leka lokacin da suka fito daga falon kamar ance ya juyo sai ganin zahrar yayi tana kallonsa da sauri ta juya ta rufe fuskarta da hannu ta saki wani marayan kuka ta zube a gado. Su Kuma suka fita zuciyarsa Kamar zata Kama wuta dan ganinta ba karamin fami ya zamar Masa ba, har ji yayi Yana wani layi Kamar ze fadi.
Magaji ne ya shigo falon Yana fadin "Sun tafi, wallahi Ammah naji tausayin Ya Musbahu sosai kinsan har gurin Baba malam yaje Amma magana daya dai kowa yake fada masa yayi hakuri, bayan mun fito ne yace na nuna Masa mijin Aunty zahrar na fada Masa ai shine suka Fara gaisawa dashi bayan sun gaisa da malam, shiru yayi sai kawai Naga ya dafe kansa Yana girgizawa, yace na hakura da zahra nasan wannan baze taba sakin zahra ba. wallahi Ammah sai Naga yana goge hawaye gaskiya Allah saiya saka musu wannan ai zalunci ne Kullum idan Aunty zahra ta samu miji sai an samu matsala".
Ya fada Yana Jan tsakin takaicin.
"To magaji babu yanda za'ayi haka Allah ya hukunta sai hakuri".
Bayan tafiyarsu da Kamar awa daya Abdul Hakeem ya shigo ya fadawa Ammah tazo Abba Yana kiranta.
A bedroom dinsa ta sameshi Yana tsaye ya goya hannunsa a baya Yana Dan Kai kawo a tsakar dakin.
Sallam tayi Masa ya amsa sannan ya sauke hannunsa ya nufi gefen gadon inda Ammah ta zauna tana tambayar "Lafiya kuwa Abba meya faru Naganka a haka?"
Ajiyar zuciya ya sauke Yana fadin.
"Da matsala gaskiya yaron nan ne yazo a rikice yana kuka Kamar yaro karami da kyar muka lallashe shi nida Abdul Hakeem ga mahaifiyarsa da 'yan uwanta kingansu dai nasan mazan ne suka ce ba ruwansu shine ita da kanta ta taso tazo wallahi hawaye bibiyu ta rinka yi min akan na rufa Mata asiri na warware wancan auren a maida kan Musbahu abin har abin tausayin wallahi, shi yasa na turosu cikin Dan ku Basu hakuri tunda wancen zance ya wuce Kuma ji nayi da nauyi na Kira malam wallahi tunda ganin Mahmud nake Kamar Dan cikinsa Kinga na Kira shi akan maganar ai Bai kyautu ba, to bayan sun tafi ne Abdul Hakeem ya Kira Hassan ya fada masa shine ya kirani Yana min magiyar Dan Allah a rakata dakinta yau basai gobe ba da tun farko ma ankaita da hakan Bata faru ba yasan wasu ne daga nan zasu Gaya Masa tunda Yana da mutane sosai suce ai tana gida ma yayi bata tare ba suyi tunanin ko Babu auren ne, Dan haka Nima nayi na'am da maganar tasa, kuje kuyi duk abinda ya kamata da magariba zan mikata dakinta da kaina in Sha Allah, na Kira malam ma na fada masa."
"To hakan yayi duk abinda ka yanke dai dai ne Allah ya nuna Mana lokacin".
"Amin ya amsa"....
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨
❤️❤️
❤️❤️
💋💋
💋💋
MAMAN FATIMAH.
PAGE SEVENTEEN (17)
_________ Karfe biyar mai kyau motar da Alhaji Jafar ya tuko da kansa daga shi sai Zahra a ciki daga bayansa Kuma Abdul Hakeem ne a wata motar ya biyo Abban nasu bisa umarninsa,suka dira kofar gate din gidan Zahra,sau biyu Abban yayi horn Mai gadin ya leko da yaga Alhaji ne da kansa tunda daman ya San Alhajin farin sani yayi sauri ya bude kofar suka shigo gaba daya, da sauri Mai gadin ya karaso Yana budewa Alhajin kofa Yana gaishe shi yayin da Abdul Hakeem ya budewa Zahra ta fito suka zagaya Gurin da Abban yake, Abdul Hakeem suka gaisa da Mai gadin sannan Abban ya Kama hannun Zahrar ya nufi kofar main falon da ita, tasha farar laffaya Mai adon kananan flowers pink, jikinta kamar an Mata barin turare sai tashin kamshi take Mai Dadi. A bakin kofa suka Hadu da Mahmud din ya nufo kofar da sauri Dan Yana bedroom dinsa yaji shigowarsu tun bayan anyi la'asar Baba malam yace Alhajin yace ya same shi a can gidansa da yamma za'a kawo Masa iyalinsa.
Matsawa Mahmud din yayi daga bakin kofar Yana yiwa Abban sannu da zuwa sannan ya mikawa Abdul Hakeem hannu suka gaisa, kan kujera Abban ya zaunar da Zahra sannan ya umarci Mahmud daya zauna kusa da ita shi Kuma ya zauna a kujerar dake kallonsu, Abdul Hakeem Shima ya zauna, sai falon ya dauki shiru, gyaran murya Abban yayi kafin yace "Abdul Hakeem yi Mana addu'a' bayan yayi doguwar addu'a sun shafa Abban yace "To Mahmud ga matarka nan na kawo maka bani na baka ita ba Allah ne ya baka ni nawa idawa ce, gata Nan amanace a gurinka kada ka zalunce ta