NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 55 of 136

Naga hakan Bata faru ba. Nayi ta fama duk Wanda zezo gidan Nan gurin yarinyar nan zezo duk kuwa da Fadi tashin da nake akan su Salma amman a banza, maganar dai daya ce Zahra, ni Kuma nayi Alkawarin badai Zahra tayi aure ta barmin Yara a gida ba,Kuma badai ta auri Mai rufin asiri ba, gashi kuwa ta Kare a Wanda ko asalin kirki bashi dashi Abu daya ya tsaya min a Rai yanda Naga gidan da zata zauna da abin yaso razani sosai Dan ba haka na zata ba, amman duk da hakan ma yayi tunda ai gidan ma Malaminsa ne ya bashi aro su zauna, Kinga kuwa karshe sai dai a Kare a yawon haya cikin Yama yamar matan alarammomi, Kuma wannan kayan da ake qafafar an saka a gidan karshen wasu kayan saidai a sayar Dan Babu abinda za'aci dasu Dan an sawo da zimmar su tafi Abuja sai gasu sun Kare a gidan Alaramma". Ta fada cikin izgilanci. ** Duk yanda Zahra taso ta kwantar da hankalinta abin ya faskara dan da gaske zulumi takeyi na yanda zata fuskanci wannan sauyin da yazo Mata a bazata Wanda Bata tab'a tunanin hakan ba ko cikin mafarki, lallai tayi zaton daga kan Mushahu komai ya kwaranye Amma sai wata matsalar ta taso wadda tafi ta baya. A kwance ta wuni duk ta tsangwami kanta Sajida sai tausarta take duk da itama tata zuciyar a kusa take Dan da gaske tana tausayin zahrar ba kadan ba. Gurin karfe biyu ne sukaji alamar Kamar anyi Baki a gidan da alama ma da dan damarsu. Sajida ce ta fito ta gaishesu zata koma cikin ne Ammah tace taje ta Kira Mama tace tazo su gaisa da Baki Iyayen Musbahu ne daga kano. Ta fita tana mamakin to meya kawo su Kuma. Tare suka shigo da mamar Dan sajidar na fada Mata ta nufo dakin cikin rawar jiki. Ciki Sajida ta wuce yayin da mamar ta zauna tana gaishe da bakin nasu Kafin Inna maimuna ta Fara Mata bayanin Maman Musbahu ce tazo da 'yan uwanta ta bada hakurin abinda ya faru Wanda ita kanta Bata San yanda akayi ba sai daga baya ake fada Mata shine tazo taji ko da yanda za'ayi a gyara matsalar tunda ta dawo hayyacinta take cikin damuwa domin kwata kwata Musbahun baya cikin nutsuwarsa tun bayan samun labarin an Aurar da zahrar, ganin lamarin nasa ba sauki ne yasa suka nufo nan Ashe har da yaron sukazo sun jima a gurin Alhaji ma kafin su shigo nan din, hakuri kawai ya basu akan aikin Gama ya Gama tunda yanzu matar wani ce ita. Kallonsu Mama ta karayi tana tambayar "Ina mamar tasa take" Hajiya Nafisa kanwarta ita ta nuna Maman Musbahun tana fadin "gata nan" "Ayya Allah sarki Hajiya sai hakuri Allah Bai nufa matarsa bace ba sai dai yazo ya duba wata tunda da sauran yaran a gidan". Mama ta fada tana kafe Hajiyar da ido. "Kayya a yanzu dai bana tunanin haka zata yuwu sai ko a gaba tunda ban taba ganin abinda Musbahu ya kwallafawa Rai ba Kamar auren yarinyar nan tunda kuwa ya rasa ta bansan Kuma lokacin da ze Kara maganar wani auren ba". Sun Dan Jima kafin Ammah ta tashi ta shiga gurin su zahra tace ta fito su gaisa da Baki zasu tafi. Jiki ba kwari ta nufo kofa doguwa rigace a jikinta kirar Bahrain Mai duwatsu har kasa blue black gyqlenta kwai ta Dora a kanta Dan Sam Zahra Bata fiye son saka hula ba a kanta Dan Sam santsin gashinta baya Bari hular ta zauna ta dunga zamewa kenan. Cikin takunta na nutsuwa ta shigo falon hade da sallama Kanta na kallon kasa ta karaso cikin nutsuwa ta zauna gefen Ammah a kasa kan carpet, tunda ta shigo suka bita da idanun kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. "Masha Allah! tubarakallah 'yata matso kusa dani dole my son yayi kamar ya zauce da labarin rasaki ya riskeshi" abinda Aunty Nafisa ta fada kenan tana nunawa Zahra kusa da ida, jiki ba kwari ta karaso ta zauna tana gaishesu. Suka amsa jiki a sanyaye su kansu sun San dansu yayi wani babban rashin da maida shi sai nufin Allah, tunda Daman shiya hada shi da Zahrar kuma shiya raba lokacin daya so. Nan sukayi sallama suka fita cikin matukar jimami Dan da gaske sunyi rashin sirika. A daki Zahra kwanciya bayi ta rufe fuskarta da hannu biyu Batasan lokacin da hawaye ya zubo Mata ba, Wai shike nan komai ya Zama past tsakaninta da Musbahu duniya ba tabbas. sajida na kallonta Bata hanata ba Dan itama Saida ta matse, lokacin zahra na falo Mushahun ya Kira wayar ta, sajidar ta dauka yanda taji maganarsa ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba kuka yake shima da idanunsa Dan abinda ya fada kawai ya karya Mata zuciya, kalamai ne na bankwana ga masoyi da da given off akan Abu, da kyar ta iya fada Masa ba zahra bace itace magiya yayi Mata dan Allah ta fito Masa da zahra yayi Mata sallamar karshe Amma hakuri kawai ta bashi tunda yanzu Zahra matar aure ce bashi da hurumin yin magana da ita. Sun Dade a haka kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa nkafin su jiyo maganar Magaji Yana fadin "Ammah ga Ya Mushahu zaku gaisa yazu tafi ne". Su biyu suka shigo suka gaishe dasu Ammah a nan Inna maimuna ke fadin "kayi hakuri da hukuncin Allah kaji kada kayi fushi da mahaifiyar ka itama bayin kanta bane duk uwa bataqi ace danta yafi kowa sa'ar abokiyar Zama ba, irin wannan matsalar ta Jima tana bibiyar yarinyar Nan to munyi zaton daga kank
🏠