NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 54 of 136

da maganganun da zasu iya sakata a wani Hali ai kwantar da hankali uwata take bukata ba irin haka ba, mu bita da addu'a in sha Allahu Alkhairi na hada Wanda a gaba duka sai sun gode min koda kuwa bana duniyar ne". Tunda Zahra ta shigo ta kwanta a kan sofa a nan falon Ammah na kallonta tasan kan zance dan tunda Abba ya dawo daga masallaci ya fada Mata, zancen da suke da Inna ma kenan ta shigo suka bar zancen. Da hantsin Ammah ta Kira Aunty Hasana ta fada mata. Zuwa Sha biyu tana gidan suna zaune a falon Ammah Mama ta shigo ita da kawarta ta amana Asabe wadda kwanan Nan ta mayar da gidan gurin zuwanta sabanin baya da sai a share watanni Bata zoba, Nan suka zauna akaci gaba da tattaunawa akan tarewar Zahra har Asabe ke fadin zata saka wata 'yar gusau da suke makwaftaka ta yiwa Zahra hadin kazar amare da daka shine nata Gudunmawar. Da yamma Aunty Hasana ta umarci Sajida da Hameeda da zilai Mai aiki suzo suje gidan Zahrar a gyara abinda ya kamata tunda jeren ya dan jima da yi. Sun fito zasu tafi ne Abdul Hakeem ya tsayar da Auntyn Yana fadin "sai Ina Kuma Aunty mu?" "Gidan Zahra zamuje a Dan Kara gyarawa jibi Abba yace za'a kaita kaga kuwa ai dole a shiga a duba ayi abinda ya kamata". Komai tsab suka sameshi da gani ana gyarawa Kullum dan har wani hadaddan kamshin freshner ke tashi a falon haka bedroom din Shima komai neat yake a toilet ne abin ya bawa Aunty Hasana mamaki an zuba kayan wanka masu azabar tsaba Bata Kara tsinkewa da ta janyo locker ta jikin mirror taga wasu designers din turaruka na Mata Kuma da yawa na kamfanin Al -haramain ne harda irin Wanda Zahra take amfani dasu. Ita dai Hameeda Yar kauye ta Zama a gidan Dan ko a mafarki Bata taba kawo Wanda aka aurawa Zahra, ze Kama hayar gida irin wannan aljannar duniya haka ba. A kitchen ma Nan Hameeda da zulai suka lalace komai na gurin saiya burge mutum, Nan ma Saida Auntyn taga wani fregde ash colour a cikin Dan ack din jikin kitchen din irin Mai kofa Kamar ta wadroof ko ba'a fada ba kasan kudi sunyi kuka a gurin. Burner Auntyn tasa aka jona aka zuba turarikan wuta Wanda aka hadowa Zahra daga Saudi Arabia tun wancen lokacin tunda basa komai saima Kara kamshi. Basu baro gidan ba sai kusan magariba. Aunty Hasana taso ta wuce da Zahra gidanta amman Ammah tace A'a ba inda zata so suke ace Mata tsohuwar banza idan so suke su tafi to ita zahrar ta Kira ta fadawa mijinta idan ya amince ita nata Mai sauki ne ita kuma Zahra tace lahlah a barshi kawai. Wajen goma saura aunty Hasana ta dauki yaranta suka wuce gida. Da safe Saiga Asabe da dahuwar kazar amare da jarkar zumar Mata da ta tsimi tayiwa gidan tsinke, part din Ammah ta shigo direct, bayan sun gaisa ne ta mikiwa Ammah babbar ledar data zubo kayan tana fadin "Ina Amarya tazo gashi na cika Alkawari tazo ta cinye ta bani kashin tace a koma Mata dashi zata hada Mata wani Abu dashi. Inna maimuna ce tace "ai kuwa yanzu taci abinci ta shga daki saidai a aje zuwa anjima sai taci ko gida ne sai a aika Miki da Qashin, mun gode kwarai madallah Allah yabar zaman tare". Asaben ta amsa da "Amin ai bama sai an tashi mutum ya kaiba Nima saina jira taci din ko Nan da yamma ne" ta fada tana mikewa tayi musu sallama ta nufi dakin Mama. Bayan fitarta ne Ammah ta dubi Inna maimuna tana fadin "nifa jikina Bai bani ba akan taci wanna abun Dan ni tunda ta fada jiya naji abin Bai kwanta min ba,mutuniyar da gaisawa ma sai ta kure akeyi da ita Amma fa ki duba sai wani rawar jiki take akan abinda Bai shafe ta ba ko alama, Kuma kar nice wani abun arziku sukeyi da zahrar Dan ko gaisawa saita kure, Amman ki duba ki gani yanzu sai haba haba take da Zahra. Dakin Ammah aka shiga da kayan ammar tace zata cire tsokar tabar musu kashin, hakan ne ya kasance tayi komai ta baiwa auta ya kaiwa Asaben dakin Mamar. Saida Asaben ta tabbatar auta ya fito ta kwashe da dariya tana fadin "wallahi Maman yara kinsan ta kan mugumta, yarinya har yarinya amma ta Kare a auren marar asali Wanda ko danginsa ba'a sani ba" Kwafa Maman tayi "barni kawai Asabe wallahi tun lokacin da aka dauko yarinyar nan hankalina ya kasa kwanciya, saboda babu ta inda Allah ya rageta duk abinda ake so jikin 'ya mace to Allah yayi Mata ga uwa uba yanda mazan zamanin nan suka jarabtu da son Mata irinta nasan ba karamin mutum ne ze dauke taba Ina zaune sai dai na Zama 'yar kallo ga nawa 'ya'yan a gabana, wallahi baze yuwu ba ai hankalina Bai Kara tashi ba Saida na raka Aunty Ladi gurin wani Mutum a can jos nayi Masa maganar Asma'u to cikin binciken ne maganar yarinyar ya Fado yake fada min na kyale maganar Asma'u don ba yanda zanyi da ita jikinta a shirye yake haka Shima Alhajin ba abinda zeyi tasirin da ze rabashi da ita, Amma ga wata yarinya Nan duk gidan ba 'yar da zata wuceta a sa'ar rayuwa a gurin aure Dan mijin da zata aura ba karamin mutum bane Kuma dai..... Sai kawai bawan Allahn Nan yayi shiru da bakinsa nayi nacin duniyar nan Amman yaki karasa mana zance, haka muka tasho Aunty Ladi nata zugani kada na kuskura na Bari ta auri Mai maiko duk yanda zanyi nayi
🏠