ko matsalar namijin Aljani ne ya aureta Amma duk inda akaje da ita sai a ce ba wani iska a jikinta".
Inna maimuna ta fada.
Sun tattauna sosai da Maman Sajida Saida akayi sallar Azahar Sajida ta raka mamanta dakin Mama su gaisa, sun Sami kawar Mama Asabe sun hada Kai suna kus-kus bazaka taba cewa da mutane ba.
Sun gaisa sajida ta fadawa Mama mamanta ce, Basu jima ba suka fito Mama ta biyosu har kofar part dinta Nan godiyar ziyarar.
Sai kusan karfe uku su Maman Sajida suka juya Kano Sajida tace ita saita raka Zahra gidanta zata dawo.
Tun da Mahmud ya Kira Zahra sau daya Bai sake kiranta ba, yau yaji ya kamata ya Kira yaji lafiyar ta ko banza fa yanzu tana karkashin ikonsa ne cinta da Shanta da duk lamuranta suna wuyans Kuma ai Bai kyauta ba gaskiya ace yayi burus da lamarin ta abun sai yayi Mata yawa.
Sai gurin Tara na dare ya lalubo numbarta ya Kira, harta gama ringing ba'a dauka ba sai kawai ya share ya tura Mata text massage ya fada Mata Daman ya kirane yaji lafiyar ta.
Tun bayan tafiyar Maman Sajida Ammah da Inna maimuna suka shiga hasashen abinda kakan Sajida ya fada na hasashen Mai yiwa Zahra bita da Killin nan duk iya nazarain su Basu gano ba sai suka.barwa Allah amma dai innar ta soke kwanan Zahra a can gurinsu tace su dawo dayan bedroom din Ammah suna wanna ita da Sajida da ita innar ya ishesu ita ko katifa sai a saka Mata a kasa ta kwanta.
Hakan akayi su Zahrar suka tattaro suka duk wani Abu na amfaninsu suka dawo dakin.
Kafin su kwanta Saida Inna maimuna ta saka Zahra tayi amfani da duk magungunan da Maman Sajida ta kawo Mata, wanna ne dalilin dayasa innar tace su dawo nan tunda komai na duniya Yana son sirri, duk da Hameeda ce kawai ke kwana a tare dasu Zahra Dan Salma tunda suka dawo ma Bata taba kwana a part din nasu ba.
Tun Hameeda na jiransu Zahra su shigo har tayi barci.
Saida Zahra ta Gama amfani da duk abubuwan da aka kawo Mata sannan ta dauko wayarta rabon data dauko ta tun bayan sallar Azahar data hau online ta duba sakonnin whatapps.
Sajida da Inna maimuna Kuma sunta hirar duniya abunsu.
Missed calls ta gani har hudu uku na mujiba ne sai Kuma wani daya number ce amma kallo daya tayi Mata ta gane ta waye, ji tayi gabanta ya fadi to neman me yake Mata da wanna tsohon Daren haka kawai ya dagula Mata sauran lissafinta. Fita tayi daga call history din sai Kuma taga envelope alama massage ya shigo budewa tayi sakonsa ta gani a hankali ta furta ta "Ya salam".
Allah da gaske fa take jin wani irin lamari a tare da shi.
Da safe ma innar ta saka Zahrar gaba Saida tayi duk abinda ya kamata kafin ta fice tabar dakin dan tun kafin ta Fara Sajida tayi waje ta Basu guri. Saida tayi wanka kafin ta fito yin break bayan sun gama ne Ammah tace Zahra taje Abbansu na kira, gyalen rigar ta yafa a kanta ta nufi gurin Abban, lokacin data shiga ya Gama break Shima, guri ta Sami ta zauna kusa da kujerar da yake Kai tana fadin "Abbana Ina kwana?"
Jaridar dake hannunsa ya aje Yana fadin "lafiya kalau uwata, Ina fatan ba wata damuwa ko?"
Kai ta gyada kafin tace "ba komai"
"Masha Allah ya fada.
Kafin yayi gyaran murya ya Fara fadin "Uwa inaga in sha Allahu jibi da yamma Zaki tafi gidanki Dan dazu ne malam Bukar ya roki wannan alfarmar saboda shi Mahmud din ne zeje wani taron da kunyar da suke aiki dashi suka shirya to Kuma yace baya son ya tafi Baki tare acan gidan ba kada abin ya Zama na magana ace ko ya gudu ne ya barki a nan, to Nima din na karbi nasa hanzarin tunda Masha Allah jikin naki yayi sauki sosai Kuma Baki bani kunya ba kin kwantar da hankalinki".
"To Abba"abinda ta fada kenan tayi shiru, Mamace ta shigo dakin itama Tasha wanka sai baza kanshi take Kamar Kullum. Da barkwwnci ta shigo tana fadin "A'a bamu Gane ba, irin wannan kebewa tsakanin 'ya da uba mu ba'a neman ayi shawara damu".
Ta fada tana fadada murmushinta.
Gaisheta Zahra tayi kafin mamar ta gaisheta da Abban tunda ba itace da girki ba.
Bayan sun gaisa ne yake fadawa mamar "Ba wani shawara muke ba wadda Bata shafeku ba Ina fada Mata ne jibi in Sha Allah zata tafi dakinta tinda Allah yasa ta warrare Kuma shi mijin nata ne zeyi tafiya shi yasa nake son ta tafi dakinta".
Nisawa Mama tayi kafin tayi magana.
"Kamar Yaya zeyi tafiya daga Kai masa yarinya basai ya tafi da ita ba salon ya cuci yar mutane ya lallaba ya budu ya barta tunda tsintacciyar mage ai Bata mage, gaskiya Abban Yara ka tsaya ka duba lamarin nan Mana kada fa azo ana Dana sani kaga masu iya magana na cewa keyace".
Abban ne yace "ba abinda ze faru sai Alkhairi Amma Jibi da izinin Allah uwata zata tafi dakinta, tashi kije Uwata Allah yayi Miki Albarka yanda Kika yi min biyayya Ubangiji ya Baki 'ya 'yan da zasu yi Miki biyayya kema".
A zuciyarta ta amsa da "Amin"
Saida Abbai yaga ta fice gaba daya sannan ya dawo da dubansa gurin Mama yace "haba Rabi'a har yaushe Zaki dinga magama irin wannan a gaban kankanuwar yarinya Kamar Zahra ai Bai kamata ba ki duba kiga yanda aka dunga walagigi akan auren yarinyar nan a baya yanzu Kuma anyi aure Zaki ringa fito