kudan kudin da za'a kashe gurin sawo kayan sana'ar da za'a koyar harda kudin da za'a participants din tunda program din harda matasan unguwa a cikinsa duk za'a Kuma bada kayan sana'ar da mutum ya koya kyauta, tun lokaci yayi masa alamar tambaya sai dai ba wata kafa daya Bari wadda za'a fashimci komai. Bai tabbatar da abinda yaji ba Saida akayi komai Kamar yanda ya bada umarnin, ga Kuma lokuta yawa sai yayi batan dabo ka nemeshi ka rasa Kuma har yanzu baisan takamaiamai Ina yake zuwa ba duk kuwa iya kwakwarsa.
Jakar ya dauka yayi gaba Yana fadin Bari na Dan watsa ruwa na fito. Da ido suka bishi har ya shige corridor din daze kaishi bedroom dinsu,kowa Yana ayyana wani Abu a zuciyarsa.
Ya dauki Kamar minti hamsin kafin ya fito cikin Riga da wando na shadda Fara tas, a gaggauce ya fito ganin lokacin sallar magriba ya kawo jiki.
***
Da dare Zahra tana dakin Ammah suna Hira da Inna maimuna tana Kara nusar da ita yanayin rayuwa Sajida ta shigo da waya a kunnenta ta gaishe da innar ta Mikawa Zahra wayar tana fadin "Baffan Rimi ne yake son magana dake"
Amsa tayi tare da sallama, cikin daki Inna ta nuna Mata da hannu ma'ana ta shiga ciki tayi wayar, Dan sajidar tana Mika Mata ta juya ta koma, haka Nan ta tashi duk da Bata San nufin innar na hanata waya a falon ba.
Gaishe da Baffan tayi tunda Daman ya Santa tun suna makarantar kazaure sunje masa ita da Sajida lokacin da Zahrar ta zauna a kano gidansu sajidar sanda akayi musu hutun midtrem break maimakon taje Azare sai umman sajidar ta nemi Alfarmar Ammah ta barta tayi hutun a gurinta,to kafin su koma ne sukaje Rimin sumailar gurin kakan sajidar, tun lokacin ya baiwa Zahra magunguna sosai yace tayi amfani dasu har Sajida na mita ita Bai Bata irin na Zahra ba, a lokacin murmushinsu manya yayi Yana fadin "yanda aka saka rayuwarta a gaba ke ba Wanda ya damu da taki rayuwar ita akwai tarnaki Mai yawa a kanta Kuma Naga jikin nata ba wani abun azo a gani na tsarin jiki.
Gaisuwar Baffa ya amsa Yana fadin "Ashe haka lamura sukayita faruwa ko Fadima? Dazu Babar taku tazo min da bayanin abinda ya ringa faruwa dake akan aurenki, yanzu haka tana Nan zata kwana saboda akwai abinda nasa ayi Miki gobe in sha Allah zatazo Miki dasu da yanda zakiyi amfani dasu in sha Allah ba abinda ze Kara faruwa dake, lallai akwai shedancin mutane akan lamarin Amma mu dauka Daman haka Allah yayi nufi, wanin Allah Bai Isa yayi maka komai ba face da izinin Ubangiji, ga Uwar taki ku gaisa".
Ya mikawa Maman Sajida wayar.
Bayan ta gaisheta ta Kara da yi Mata nasiha sosai itama, sannan ta fada mata gobe in Sha Allah daga Rimin Nan zasuyo ita da Babban danta Wanda some times shine direban ta idan zatayi doguwar tafiya, kafin sukayi sallama.
Dakin Ammah Zahra ta shiga ta fada Mata yanda sukayi da kakan Sajida, godiya sosai Ammah ta ringa yi tana Kara jinjina kaunar da bayin Allah nan.suke yiwa Zahra dalilin 'yarsu gashi saboda matsalar Zahrar zata taso tazo har Azare.
Washe gari tunda wuri Zahra da Sajida suka Gama gyaran dakin Ammah sukayi wanka sannan sukayi breakfast gurin karfe Sha daya Maman su Sajida da yayanta Ya Abba suka karaso murna gurin Sajida ba magana, dakin Ammah suka nufa da Maman Zahra tasonsu Fara shiga gurin Mama su gaisa Amma Sajida ta Hana tana fadin "A'a ki Bari mu shiga inda ya kamata idan min Gama abinda ya kawo ta sun gaisa da kowa so kike azo a zaune Mana a hana ruwa gudu".
Tarba ta girma Ammah tayiwa Maman Sajida itama ba wata babba bace Dan Bata Kai sa'ar Ammah ba, an sauki Ya Abba a dakin da suke sauke bakinsu yayin da magaji ya shiga shidima dashi.
Bayan Maman su sajidar ta Gama cin abubuwan da aka kawo Mata suka sake gaisawa dasu Ammah da Inna maimuna ta jajantawa Ammar abubuwan da suka ringa faruwa, ta Kuma Dora musu da bayanin da mahaifinta yayi Mata akan matsalar Zahrar inda ya bada tabbacin ko waye yake wannan shegantakar a kusa dasu yake sosai, Kuma dashi ake faduwa da tashi, kuma yace kada Wanda ya kawo wani Abu da sunan naci kona Sha yace a baiwa Zahra da sunan tsarin jiki ko na gyaran aure a barta taci sannan a kula da Koda abincin cikin gidan ne in dai ba ita Ammar ta dafa da hannunta ta Bata ba daga Nan har tabar gidan.
Wata babbar leda ta dauko wadda sukazo da ita ta bude ta Ciro jarka da ruwa a cikin Mai kalar yellow na za'afaran ta dauko wani garin magani Mai laushi ta hadasu da jarkar ta mikawa Inna maimuna tana fadar.
"Ga wanna ruwan addu'a ne da garin magarya zata dibi ruwan addu'ar ta zuba garin magaryar ta Sha ta shafe jikinta safe da yamma,wannan Kuma kafa da hannu kawai zata Riga turarawa sai Addu'oi da ya bada a Bata zata ringa karantawa safe da yamma".
Godiya sosai su Ammah suka shiga jerawa Maman Sajida Kamar ba gobe har sai da ta ringa fadin "Haba Hajiya meye amfanin taren abinda ya shafi Zahra ai ya shafi sajida wallahi shekaranjiya data Kira ta fada min hankalina ba karamin tashi yayi ba wallahi na dauka abin ya kwaranye tunda an dauki dogon lokaci kafin a Kara maganar Auren".
"Wallahi kuwa muma mun dauka na bayan da aka fasa