ra ganinsa naji wani irin Abu a jikina wanda ban tabaji ba a kan ko wane namiji sai shi, Kuma yayi min abinda ya kamata na dauki mataki Mai karfi amman wallahi ko magana kasayi Masa nayi, yanzu kuma a haka zan rayu dashi? Ni wallahi bana sonsa Sam Kuma fa Shima yace baya son abin yake ba kawai dai baze iya watsawa su Abba kasa a ido bane". Ta karasa fada hawaye na zubo Mata a fauska.
Lallashinta sukayi da kyar tayi shiru kafin mujiba tace "haba Zahrar ki daina kuka idan kina daga hankalin ki na Ammah ma baze kwanta ba, Kinga irin haka ba Dadi duk da an aura miki Wanda babu soyayya da shakuwa a tsaninku, ita a hakan ma yayi Mata da ace wannan karon ma an fasa aure gara hakan tunda naga alama da ita ake fadan ke kin ratso ne kawai ake fakewa da lamarin ki Dan a Hana duniyar ta zaman lafiya da kwanciyar hànkali, Kuma Baki san dalilin da yasa Abba yayi hakan ba, kinsan dai Abba baze taba aura Miki baragurbi ba kedai kiyi ta addu'a muma muna tayaki, Bari na tambaye ki Mana idan kina addu'a bakya cewa Allah ya Baki miji na gari?"
Hannu tasa tana share guntun hayenta kafin ta harari mujibar tana fadin "Ina yi Mana kuma kawai saina yi sallah na kasa wannan addu'ar dan na Zama abinda na zama ko?"
"A'a ba haka nake nufi ba bayani zan miki shi yasa nayi Miki tambayar dai, Allah ya huci zuciyar Amarya".
"Kina jina mu 'yan adam muna rokon Allah ya zaba mana abinda yafi Mana Alkhairi Amma wani lokacin inda kake zaton alherin ne to sai kaga ba'a Nan yake ba, idan yazo ta inda baka zata ba tunda bakasan gaibu ba, sai kayi watsi dashi idan bakayi sa'a ba haka abun ze kwaranye baka mori komai ba, alhalin Kai ka roka aka baka sai kuma ka Raina abinda aka baka ba tare da kasan shine alherin ba. To Dan haka nake so ki yiwa Allah da manzonsa ki rike abinda Allah ya Baki tunda shi Kika roka Kuma ga abinda ya Baki sai kiyi ta Tahamidi ga Allah kawai, ki nemi Allah ya saka muku kaunar junanku da soyayya da jinkai. Dan kinsan dai idan ba wata kaddarar Ubangiji ba Babu abinda zesa ya rabu dake tunda ya karbi auren Nan wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba yana so, dan haka ki daure kiyi Masa biyayya shi arziki nufin Allah ne, naji ana ta 'yan kananun magamganu ki toshe kunnenki kada ki bada barakar da wani ze kushe Miki miji dan bashi da kudi, Allah ne Mai azurtawa lokacin daya so sai kiga wata Rana sai dai a tada labarin abun".
Sun Dade suna kawo Mata misalai da yawa na irin wannan auren nata daga baya Kuma ya Zama Alkhairi.
********** A matukar gajiye Mahmud ya shigo cikin gidan misalin karfe biyar na yamma tun safe ya kebe kansa a dakin daya Kama na hotel yake ta faman aiki yaso kwarai ya Gama da wuri kafin yamma amma abun ya gagara Dan da gaske aikin ya dauki hankalinsa sosai ga tafiyar dake gabansa Banda Allah yasa wasu abubuwan sun daidaita a jiya da dole tsakanin gobe da jibi dole yabar garin ko baya so. Amma cikin taimakon Ubangiji sai komai ya Fara daidaita, shi kanshi Yana Jin idan ya tsallake ya tafi daidaita wanna gabar Bai kyauta ba Sam, dan jama'a zasuga kamar ya gujewa auren gatan da akayi Masa ne ya watsa musu kasa a idon an Masa gata irin wannan sun dauki yarinyar su Mai tsada sun bashi ba tare da sun San ko waye shi ba, ko la'akari da karancin samunsa suka aura Masa.
Su Habib ya tarar a falon Yana karatun Alqur'ani, Abubakar Kuma Yana ta faman hada Nile sat.
Su duka suka amsa Masa sallamar Nan falon ya aje jakar laptop dinsa abinda bai taba kwatanta zuwa da ita ba kenan Dan duk aikin da zeyi sai dai yayi acan hotel din ya barota, amma yau dole tasa ya taho da ita nan saboda so yake ya raba dare Yana aiki shi yasa ma Kai tsaye ya nufo gidan da ita yasan bashi da matsala dasu duka biyun.
Abubakar ne ya tsaya da aikin Yana kallon Mahmud Yana fadin "Dan Allah Ina ka shiga Wai bakasan kana dagawa Baba malam hankali ba? shifa yafi son daya juya ya ganka, gashi ka Kama ka rufe wayar ana ta Kira a rufe".
Girarsa ta daman ya dan shafa kadan kafin ya zauna Yana fadin "cool down Mana my man Ina kake tunanin zan tafi? Wallahi aikine yayi yawa na wannan NGOs din bakaga har kayan aiki suka bani ba tun zuwan da sukayi wancan karon, yanzu haka ana koya min yanda zanyi amfani da ita laptop din ne yanda zanji dadin aikin, Bari nayi wanka sai muje gurin Baba malam din nayi Masa bayani yanda ze fashimta, sunce ma nan da sati daya ko biyu zasu kiramu zuwa babban taro da za'ayi".
Tunda ya Fara magana Habib ya dakata da karatun da yakeyi yana bin Mahmud da kallo haka nan kawai yaji Kamar ba gaskiya Mahmud din ya fada musu ba, Kamar yana boye wani Abu, shifa tun lokacin daurin aurensa ya lura da yanda Kamar yake baiwa Sameer umarni a wasu lokutan sai idan ya farga ne yakan yi maza ya canza taku, sannan a watannin baya ya taba jin yana waya a kusa da dakin da suke taron abinda ya shafi makaranta lokacin yana duba wasu sabbin forms da aka kawo na Enterprinuership da za'ay a gurin Sam baisan Yana ciki ba tunda kofar a rufe take ji yayi sosai Yana bada umarnin yanda abin ze kasance harda ma