NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 50 of 136

akuna uku a hotel idan zasu zauna har zuwa Daurin aure. Saura kwana biyar Daurin auren ne wani abun al'ajabi ya faru da Hajiya Nafisa Maman Mushahu wadda suke Kira da Ammi. Cikin dare tana barci ta farka a matukar razane saboda wani mugun mafarkin da tayi da Musbahun akan auren, addu'a tayi ta koma ta kwanta ai kamar jira ake barcin ya dauketa sai abunda ta gani a wannan mafarkin yafi wancen muni, wasa-wasa barci ya gagareta a wannan Daren kafin safe duk ta wani hargize ga wasu irin tunane tunane sun cika Mata zuciya na rashin kwanciyar hankali kafin yamma gaba daya ta Zama wata marar nutsuwa ba shiri ta Nemo kanwarta Aunty Jamila a waya Nan da Nan tazo tunda ba aure gareta ba, duk ta kwashe komai ta fada Mata akan Bata son auren Musbahun kwata kwata ita fa ko a cikin ranta ta tuna da zeyi aure ji take kamar zata zauce, da farko Aunty Jamilar ta dauki abun Wasa Amma ganin da gaske abin yake yasa ta Kira Babban yayansu Alhaji sulaiman da kanin Baban su Musbahun Alhaji isma'il, Suma da farko sunyi zaton na Wasa ne Amma da suka matsa akan ta Fadi dalilinta na Hana yuwuwar auren sai abun ya ta'azzara ya Zama kamar Mai tabin hankali, ganin abun Yana neman ya Zama wani iri ne yasa Alhaji sulaiman ya kirawo Aliyu tare da tambayar suna ina?. Aliyun yace gasu Nan a hanya sunje Azare ne Amma har sun wuce wudil sun kusa kano ya fada Masa lallai direct su nufo sokoto road su duka. Haka suka shigo suka tarar da wannan dambarwar ana ta fama da Ammi. Ai tana arba da Mushahu ta Kara tuburewa tana fama fadar wallahi matukar ya kafe sai auri Zahra Bata yafe Masa nononta da yasha. Su dai Basu ankara ba sai ganin Mushahu sukayi ya sulale ya zube a sume, da sauri Aliyu ya kawo ruwa aka zuba Masa Amma a banza ganin haka yasa suka nufi Asibitin Nasarawa dashi. Haka aka dunga juyawa da Ammi Amma ta kafe kamar kafiran farko duk Wanda ake tunanin ze kawo gyara a lamarin an fada Masa Kuma yayi bakin iyawarsa Amma ba wani ci gaba da aka nemi a Zafafa sai lamarin yaso ya koma Mata tabin hankali abinda daya tada hankalin Babarsu kenan Hajiya Yaya tace dole a hakura da auren tunda abin yazo da irin wannan lamarin marar Dadi daman tun farko ita bataso lamarin ba sai dai yaran yanzu ne baka hanasu abinda suke so, tunda Daman fa ance shine na uku a Wanda zasu auri yarinyar ana fasawa to shima gashi tun ba'aje ko Ina ba lamarin ya Zama haka. Tashin hankali iya tashin hankali Musbahu ya shiga Dan dakyar aka Sami nutsuwarsa dan kwata kwata ya daina magana da kowa ya rufe duka wayoyinsa shima Deeni ganin kiran Zahra yasa ya rufe layin da suke wayar da ita, Aliyu ne kawai Bai rufe wayar ba Amma baya picking idan ta Kira a halin hake ne su Alhaji sulaiman sukaje Azaren da labari marar Dadi Wanda ya kawo karshen 'yar Wala walar da akeyi da Zahra akan aure ta kawo karshen duk wani makirci da bita da kulli da ake Mata na rushe aurenta idan ya taso abinda ya girgaiza duniyar Wanda suke fake suna tsula ta'addanci ta karkashin kasa. ✨ ✨ AUREN HUCE HAUSHI ✨ ✨ MAMAN FATIMAH Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu. Dan Allah ayi hakuri da matsalar da aka samu gurin turo page fourteen sau biyu hakan ya faru ne saboda wasu dalilai Amma na karshen Wanda na turo shine cikakken fourteen din yanzu kuma na hade fifteen & sixteen guri daya na gode. Page Fifteen & Sixteen 📖🖋️ BACK TO STORY. ________ Gurin Zahra su Sajida suka shiga tana kwance a gado idanunta a rufe tayi zurfi cikin tunanin, Sam bataji shigowar su Sajida ba Saida mujiba ta Dan zungure ta bude ido ta yunkura ta tashi zaune tana dafe kanta dake Sara Mata. Sajida ce ta zauna kusa da ita ta Kama hannun Zahrar tana fadin "bestie Dan Allah ki rage tunani kada wani ciwon ya kamaki, ki yawaita addu'a komai yayi zafi maganinsa Allah. Kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, ke kanki Baki taba tunanin abun ze Zama haka ba, Kuma Allah ya juya lamarin yanda yaso, to saiki gode Masa bisa ni'imar da yayi miki, Kuma nifa mujiba Ina doubting akan wannan da aka daura musu aure, Kuma ki rubuta ki aje zakice na fada Miki kije kiga gidan da za'a Kai bestie, Kuma ki duba kiga irin kayan da aka kawo yanzu kinsan duk Wanda ya hadasu first class ne a gurin gayu wallahi komai bana banza Amma Kuma Wai almajiran malam ne gaskiya I doubt much". Ta fada tana kallon mujibar. Ita dai Zahra ta rasa inda zata Kama komai ya kwance Mata, su damuwarsu kaya da gida, ita Kuma tata damuwar ta yanda za'ayi zaman ne, har yanzu gani take kamar a mafarki Wai wannan karon ma Saida aka samu akasi,ta rasa daga Ina matsalar take, shi kuma auren da aka daura meye ze biyo baya tasan idan ba wani nufi ba na Allah shima sai an Sami wani kalubalen a cikinsa. A hankali ta furta "Ya Salam! Allah ka shiga cikin lamarina, wallahi bestie komai ya kwance min bani da sauran dabara,kwakwalwata ta daina aiki yanda ya kamata kinsan Allah nifa kamar ma tsoronsa nakiyi Dan tunda na Fa
🏠