". Ya fad'a Cike da ladabi, hannunsa ya zura a aljihun wandon jikinsa ya dauko wasu ya Kara Masa, sannan ya Kuma dauko wasu ya bashi alamar ya baiwa abokan aikinsa.
Godiya suka dunga jero Masa Dan inda sabo sun saba da Alkhairinsa.
Kai tsaye gurin Ashiru Mai shayin ya nufa duk da dare ya Fara Amma yasan yanzu 'yan term din nasa Basu Isa tafiya gida ba Dan sukan Kai har daya na dare suna hira.
Makullin lifan din ya mikawa Bashir Yana fad'a "Jazakumullahu khairan".
Habib ne yace "Wai Dan Allah Ina kaje a rufe wayarka tun dazu nake nemanka fa daga inje in dawo kawai na nemeka na rasa sai su Salisu ne sukace kazo nemana ka wuce unguwa".
Kusa da Habib din ya zauna na fadin "wash Allah wlh duk na gaji".
"Da kayi aikin me".
Cewar Habib.
"Bari kawai ba aikin da nayi Amma Wanda yake fuskantoni ba sauki kazo muje gida akwai sakonka da Malam ya bani na baka".
Ya fad'a Yana kikewa tare da mikawa su Bashir hannu yayi gaba gurin lifan din Habib.
Dakinsu Mahmud ya bude daki ne madaidaici da gado guda biyu da wardrobe ta jikin bango sai mirror irin na croom din Nan da AC, kasan dakin shimfide da tayil, lokacin da akazo aikin NGOs din ne aka yiwa Malam nashi falon da Kuma irin wadannan dakunan guda uku sai Kuma dakunan Yara almajirai sama da kasa.
Dakin sai kamshi yakeyi, sau da yawa Habib kanshi Yana mamakin wasu abubuwan na Mahmud sai dai ba fuskar da ze tambaye shi duk kuwa da amincin dake tsakaninsu.
Saida Mahmud yayi wanka ya saka kayan barci sannan ya
Zauna a gefen gadon Yana fuskantar Habib kafin yace.
"Kai inaga fa nan da kwana uku zan ankwance".
Ya fad'a yana wani killer smile.
Zabura Habib yayi ya tashi zaune sosai Yana fadar
"Kamar Yaya?"
"Kamar yanda na fad'a maka, tsayar Dani da Malam yayi kenan yace Alh Jafar ya bani auren yarinyar Nan da ake bikinta wadda Abdul Hakeem ya kawo Mana IV last week".
"Ban Gane ba bafa ta Yaya hakan zata faru?"
Kafada ya dage alamun shima Bai Sani ba.
"Dan Allah kayi min bayani yanda zan fahimta a sakani a duhu wallahi".
"Iya abinda na Sani kenan kawai ance an bani idan inaso inyi shawara".
Cikin madaukakin mamaki Habib yace "to Kai ya kace masa?'
"Me zance kuwa na karba na gode, kasan har abada ba jayayya tsanina dasu iyayene sak, sun min abinda kowane uba yakewa dansa sun min gata sun Kula Dani lokacin da bana Gane gabas bane Gane yamma bana Gane fari bana Gane Baki,
Sun zamar min garkuwar data Hana kowane harbi ya sokeni, Toni kuwa wanen irin butulu ne da zan watsa musu kasa a Ido sufa sun san waye ni Amma suka runtse idonsu suka bani basu nuna min kyama ba, sannan ka dubi yarinyar da aka bani diamond ce fa a cikin gold kasan bani da abinda zan tunkari irin wannan yarinyar da sunan soyayya bare har aje ga maganar aure".
Tunda ya fara magana Habib yake Masa kallom mamaki Yana jinjina karfin ikon Allah, lallai wani lamarin sai Allah.
Da kyar ya Sami zarafin fadin "Masha Allah! Allah ya Sanya Alkhairi Abu yayi Dadi amma fa ka daina fadar Wai baka da abinda zaka tunkare ta wlh kafin wanna lagwanin Wanda zata aura say millions shi har wani namiji ne kawai Abu daya Sani yana da kudi mu Kuma bamu dasu Amma muna da abinda bashi dashi".
"Kamar Yaya me muke da shi Wanda shi bashi dashi? ka duba fa kaga irin yanda yake shiga babban yaro ne ga manyan motoci mu Ina muka gansu"
Dan karamin tsaki Habib yayi Yana fadain "ana gabas kana yamma ana maganar nagarta da mutunci da cikar Kamala da siffar mazantaka kana wata maganar, mu an fad'a maka haka zamu dawwama bazamyu arzikin ba".
Dariya Mahmud yayi "maida wukar abin Bai Kai haka ba ko Daman haushinsa kakeji ne ban sani ba?"
Habib tsayawa yayi galala Yana kallon Mahmud kafin ya karayin wani tsakin "Allah ya sauwake zanji haushinsa Ina ruwana dashi kawai da Daman can no banga dacewar su ba Kai Nifa idan Malam yasa Yara suyi Mata addu'a har cewa nake suyi Mata addu'a Allah ya Bata gwarzon miji na nunawa sa'a".
"Amma wallahi Habib baka da mutunci shi wannan ba gwarzo bane?"
"Ina fa namiji Yana rausaya kamar mace".
"Kaga Yi closing din wanna chapter din yayi zamuyi da wannan lamarin kaga dai komai fa Sai a hankali Dan abinda nake Sami daga wannan organization din ba Isa wannan shidimar zasuyi ba ga yarinyar Mai zafi ni kamar ma tsoronta nakeji fa".
Ya fad'a Yana dariya.
Sun jima suna tattaunawa yanda zasu bullowa lamarin.
_______
Tunda garin Allah ya waye Amma take ta kaiwa da kawowa tsakanin kitchen da dakinta zuwa dakin Baki, Saida aka kammala abincin breakfast aka babba mutane sannan ta samu ta koma daki inda ta samu kanwar Babarta Inna Maimuna a uwar daki.
Kallonta tayi "Asma'u ya kamata ki karya kinsan Ina tunanin zuwa anjima gidan ze Fara cika bazaki Sami damar Zama kici wanti abun karki ba, waini ina Hajiya Mama ne Naga yau Bata leko ba?"
"Tana bangaren Alhaji Nima nayi wannan tunanin Amma ai lafiya ita keyin shiru".
"Hakan ne Kam".
Cewar Inna maimuna.
******
Katagum road
A dakin Aunty Hasana Zahra ta kwana ita da Autart Haneefa, sai kusan goma ta tashi daga barci wayarta ta F