NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 46 of 136

acin da Zahra ta kalleta tayi tsaki tace "Wai wannan ce mace,kina duba mirror Kuma kina ganin kanki kuwa?gara ni da har kike min gorin ana saka aurena ana fasawa, Ina laifi tunda har ana ganina ana sona, kaddarar Babu mijina a cikin su ce take rabani dasu, kefa ko Kare Bai taba zuwa yace Yana sonki ba, baga kanwarki Nan ba Ina cewa har anzo tambayar aurenta? kije kiji da abinda ya dameki Zaki zauna kina fada da kanwar bayanki". Tana Gama fada Mata maganar ta nufi hanyar ficewa daga dakin. Cikin fushi salmar tayo kan Zahrar ta fardota baya saura kadan ta Fadi dai dai lokacin Kuma sahura ta shigo zatayi musu sharar yamma ta tarar da wannan badakalar, da sauri ta shiga tsakanin tana Basu hakuri ta Kama salmar ta fita da ita daga dakin tana faman zagin Zahrar abinda ya janyo hankalin Amma dake main kitchen din gidan tana yiwa Abba gas meat saboda Yana sonsa sosai yawanci idan Yana gida kusan duk dare sai anyi Masa shi. Da sauri ta fito tana tambayar "me yake faruwa ne?" Sahura ce ta fada Mata abinda ta shiga ta gani tsakanin Zahra da salmar, juyawa kawai Ammah tayi ta koma taci gaba da aikinta Bata Kara lekowa ba tanaji Mama ta fito tana fadan daman ai ba tun yau ba ta fuskanci Zahra ta Raina Salma, Kuma komai runtsi dai Salma ai gidan ubanta ne Nan ba Mai hanata sakewa. Zahra ce ta fito zata wuce zuwa part din Ammah,har ta gota Mamar batace komai ba, Mamar tace. "To fiqe kafi qaya tsini da Kika Samu guri kina yanda kikeso a gidan wallahi duk rintsi bazaki Kai matsayin 'ya'yan gida ba, tunda har abada ba'a canzawa tuwo suna" Har zahra tayi kamar ta maida Mata martani sai taji bazata iya ba babba babba ne, kawai ta shige part dinsu. Har Mama ta juya taji maganar Ammah daga bayanta, dan harga Allah batasan Ammah ta fito main kitchen din ba, Sam duk da tana jiyo kamshi ta dauka a can part dinta take aikin. Bata juyo ba Amman ta tsaya. Ammar tace "Haba Mama ban zaci haka daga gareki ba wallahi, cewa nake da Zahra da su Hameeda dauka daya ne a gurinki, ai saiki tambayi meya hada fadan?kiyi musu fadan gaba daya ba wai ki nuna Salma itace taki ba, kina fadin maganganu irin haka ai na dauka ni duk binda lauje ya yayo a gidan Nan ya kamata ki dauke shi ciyawa ne na gode amman ki sani Banda komai nufin Allah ne Zahra tafi karfin ace Mata 'yar karere tunda Mai gidan ne da kansa ya karbo rikon lokacin da aka nemi tafiya da ita kema Kuma sheda ce kinsan su waye kakanninta ba bakinki bane, dukiya idan ana gadonta kinsa Zahra 'yar mun gada ce, ko shi Wanda kike takama da dukiyar tasa yasan tazarar da nisa a tsakaninsu da kakanninta idan kina tunanin karya ne idan yazo ki tambaye shi ze Baki cikakken bayani". Bata jira taji abinda mamar ke kokarin fada Mata ba tayi gaba abunta ta nufi part dinta. Tun daga ranar Ammah ta daukewa Mama wuta gaisuwa kawai ke hada su, a kwana na biyu da Mama ta karbi girki ta kasa hakuri ita abin yafi damunta ta fadawa Abban Ammah Bata Mata magana, yayi mamaki matuka da gasken gaske Dan wannan shine karo na farko da irin haka ta faru da matan nasa duk tsawon shekarunsu. Bai taba rabasu akan sun Sami matsala ba Koda wasa, dan haka ya Kira Ammah a waya yace tazo part dinsa Yana son ganinta. Batayi mamakin ganin Mama a zaune ba tasan za'a Rina tunda kaf tasan halin Mama na zahiri. Gaishe da Abban tayi suka Kuma gaisa da Mama, tambayar ta Abban yayi ko akwai abinda ya hadasu da Ammah ne?. Ba wani kwana kwana ita Daman tun can baya Bata da munafurci ko kadan. Dan haka ba wani ta fadawa Abban duk abinda ya faru tunda Saida ta tutsiye Zahrar akan ta fada Mata abinda ya hadasu da Salma da kuma abinda mamar ta fada, shi kanshi Abban yayi mamakin abinda Salma tayi sosai, itama Mamar ya nuna Mata kuskurenta na fadar wannan maganar ya Kara da cewa. Ban tabi yiwa zahra kallon ba nine na haifeta ba, bil hasal ma shine dalilin da yasa ban aura Mata Daya daga cikin 'ya'yana ba, ita kadaice ba uwa ba uba tun batasan inda kanta yake ba, mu ta sani a matsayin iyaye sauran yaran Kuma 'yan uwanta. Idan na aura Mata wani a cikinsu ba zata Zama feel free tare da ni ba, idan damuwa ta shiga ba Wanda zata fadawa kinga ai anyi adoh badan kyau ba". " Haka ne suka fada. "To karna Kara Jin makamanciyar irin wannan maganar, ba Wanda ze kawo min rarraba kan iyalin gidana. Zahra 'ya tace kawai na saka sunan mahaifinta ne Dan haka shari'ar musulunci tazo dashi, badan in nunawa duniya bani na haifeta ba, a kiyaye kodon gaba". "In Sha Allah". Suka fada. Bayan tafiyar iyayen yasa suka turo yaran yayi musu fada sosai sanan ya Kare da nasiha. Tun daga lokacin abubuwa na zahiri sukayi sauki sosai. Kusancin Zahra da Hameeda ba abinda ya taba shi saima Kara shakuwa sukeyi a kullum suna Jin dadin butun, Zahra suna waya sosai da Ummee da Mama Hanifa harma da uncle Haisam a wasu lokutan. Lokacin da hutunsu ya kusa karewa duk sai Zahra ta nemi walwalarta ta rasa ko da yaushe kamar marar lafiya ana saura kwana biyu ta tafi Ammah ta matsa Mata taje Kiran da Baba malam yake Mata, dan sau kusan uku yana turo Yara t
🏠