NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 45 of 136

yi baya tare da rufe idanunta ruf zuciyarta na Kara speed, a hankali yayi magana saitin kunnanta "ki rinqa duba gabanki idan kina tafiya Mana kada kiyi Mana asara pls". Ya fuske yayi wucewarsa ciki Bai Kara bi ta kanta ba. Nan inda ya barta Bata iya motsawa ba, wani Abu ilahirin jikinta keyi itafa ji take kamar kafarta bazata iya daukar ta ba wallahi,.shi Kuma wanene wannan a tare da malam haka? A Ina ya Samo shi Dan a gaskiya baiyi Kama da kolo ba Sam to waye shi?". Tambayoyin dake Mata Kai kawo kenan a kwakwalwarta daga ganin mutum haka kawai ze nemi yayi Mata shiga hanci da qudundune,ga wani irin kwarjini a cikin idanunsa da Bata taba gani a gurin wani namiji ba. Bata ankara ba taji maganar malam Baba Yana fadin " A'a Fatimah ya Kika tsaya a Nan ko wani Abu kike jira?" Da sauri ta bude idanun tana kallon malam da wani yana binsa a bayan. "A'a ba komai Daman gurinka zani jikin Iya Abun ne Naga kamar ya Dan matsa tana ta rawar sanyi". Ta fadan kanta na kallon kasa kamar marar gaskiya, dan ji take kamar malam din Yana Jin mayen kamshin turarensa da ilahirin jikinta keyi. "To Babu laifi muje ciki, yanzu Mahmud yaje ya dauko abokinsa don ya kara dubata tunda jiya sunje Asibiti da Halima matar malam Mudi ance zazzabin typoid ne yake damunta, to da jikin yaki Dadi ne za'a Kara bincike ko na cizon sauro ne zazzabin".. suka wuce ciki sannan zahrar tabi bayansu zuwa falon Iya Abun Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Yana tsaye daga bakin kofar ta waje ya harde hannuwansa a kirji kamar Mai tunanin. Ganin malam din da salahuddeen sun shigo ya daga kansa Yana amsa sallamar su. Mujiba ce ta leko tana fadin" ta tashi din gata Nan fitowa". Bai shiga falon ba Saida malam ya Fara shiga sannan suka biyo bayansa. Sannu salahuddeen din yayi Mata ya dauki jinita take a Nan yayi Mata gwajin maleria ai kuwa ita ke damunta har ta Kai || +. Allura ya dauko Yana fadin " malam allura za'a yi Mata emal, idan Allah yasa an dace shi kenan idan Kuma Bai sauka ba sai ayi Mata Attusunate, amma muna fatan Allah yasa a dace ma". "Allaumma amin ya Rabb". suka fada su duka. Magunguna ya rubuta Mata na ulcer da tayi masa complain na ciwon girji da gefen kafadar ta, sannan yayi Mata Allah ya sawaqe suka fita. Har magariba su zahra suna gidan Baba malam, tun bayan fitar su malam ba dadewa Iya Abu ta koma daki ta kwanta Zahra ta rufeta da wani qaton blanket barci Mai nauyi ya dauketa. Nan falon suka zauna suna Dan tattaunawa da junansu, da tafiya zasuyi Majiba tace su zauna zuwa wani lokacin tunda ansan suna Nan Dan lokacin da zasu shigo mujibar taga kaninta Mubarak tace ya fadawa Mama suna gidan Baba malam. Duk hirar da Mujiba ke yiwa Zahra Sam hankalinta baya tare da ita ta tafi duniyar tunanin abinda ya faru dazu da Wanda aka Kira da Mahmud wai ita Zahra ce kwance a kirjin wani namijin daba muharraminta ba, Kuma ba wani mataki data dauka Koda kuwa na kad'a Masa warning ne yanda gobe baze Kara marmarin rungumar wata ba, Amma Wai sai gata ta b'ige da shakkar idanunsa abinda kaf tarihin rayuwar ta hakan Bai taba faruwa da ita ba, ga wata faduwar gaba ta ba gaira ba dalili data sameta yanzu, ganin nan biyu da tayi Masa duk Abu daya takeji a kansa. Wani wawan tsakin Zahrar tayi Wanda ya tabbatarwa Mujiba Bata tare da ita duk zubar da takeyi kamar 'ya'yan kanya. "Keda waye kike tsaki haka kuma?". Majiba ta fada. "Kedai kawai bari kawai ba komai. Ta fadar tare da you kwafa ta tashi tsaye tana fadin "Tashi mu wuce gida tunda Naga wannan barcin na Iya Abu bana Kare bane, inaga har da allaurar barci yayi Mata gaskiya". A kofar gida suka yiwa malam sallama Yana ta Sanya musu Albarka. Tun daga ranar Zahra Bata sake fita ba tana gida saidai lokaci-lokaci Mujiba na shigowa, a ranar data cika sati daya Abbansu ya dawo murna ba'a maganarta gurin Zahra, duk da tana ganin shi a can syprus din idan yaje Amma hakan bai Hana sun Kai wani lokaci ba suna tattaunawa irin ta d'a da mahaifi. Saida Zahra tayi sati biyu sannan ta nufi Jos gurin Aunty Hasana. Taji matukar dadin zuwanta Jos din. Dan har gidan Aunty Jana sukaje da Yara tunda lokacin da akayi bikin Bata Nan. Duk inda ya kamata taje taje har gidansu Mama taje haka ta kaiwa jannifer ziyara lokacin sunyi hutu tana karatu a Nan University ta Jos. Maganar samari da gaske ta sakata side idan ka ganta tana magana Mai tsawo da namiji to ka tabbatar dan uwanta ne ko wani Mai qirma a idanunta. Satinta daya a Jos suka taho tare da aunty Hasanar da Yara Wanda a satin sukayi hutu, bayan dawowar ta daga Jos ne su Hameeda sukazo hutun semester. A lokacin ne Salma ta fito mata a mutum sak, ta nuna da gaske Bata yin zahra abinda yaso ya kawo b'araka Mai girma kenan tsakanin Mama da Ammah Dan da gaske an Kai hakurin Ammar karshe, maganganu Salmar ta ringa saki kamar lokutan baya, sai dai a wannan karon Zahrar ta nuna Mata jiya fa ba yau bace, idan da tayi tolerating na nonsense din ta a yanzu Kam dai dai take da ita tunda Bata Jan girmanta a gurinta, abinda ya Kara harzika Salmar lok
🏠