NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 42 of 136

adu dashi Dan Basu da masaniyar komai akai. Gwaje -gwaje suka rubuta ayi Masa Dan binciken lafiyarsa. Basu Dade ba suka koma gida saboda a ranar Alhaji Jafar ze shiga Bauchi suna da meeting da gwamna Amma ya bar kudade a hannun Abubakar saboda magani da sauran hidimar Asibitin. Da yamma Habib ma ya shigo ya duba marar lafiyar nasu, Wanda har lokacin baya magana. Likitoci sunyi iya nasu binciken basuga komai ba a tare dashi, sai dai rashin maganar kawai Amma Kuma Yana Jin komai da ake fada. Bayan sun Gama bashi taimakon daya kamata suyi Masa suka sallame shi, Magaji ne ya dawo dasu gidan malam, Nan dakin malam na waje aka ajeshi tunda aka dawo dashi gida malam ya dukufa da Yi Masa addu'a Dan yayi bincike akan lamarin ya fashimci inda matsalar take, har Taraba ya tafi gurin malaminsa da yayi karatu a gurinsa ya fada Masa matsalar yaron, kwanansa biyu ya dawo Azare aka dukufa da rokon Allah da maganin hausa, haka zalika Alhaji Jafar ma Yana taho Masa dashi daga wani Islamic chemist da yayi musu bayanin matsalar yaron a can Abuja. Cikin ikon Allah ba'a rufe wata hudu ba ya Fara magana sai dai idan yayi sau daya sai a wuni bai sake wata ba. A haka aka dunga bashi taimakon har Allah yasa ya dawo normal Yana magana. A lokacin ne malam ya zauna dashi da Habib suka fada Masa inda suka same shi da halin da yake ciki a lokacin shiru yayi kafin yace musu shi dai yasan wata Rana Yana gida ciwon Kai ya takura masa har ya kasa fita, jzuwa dare yasha magani ya kwanta, to tun daga lokacin bazece ga yanda akayi ba shi dai ya farka ne ya ganshi a Asibiti tare dasu a hankali Kuma ya Gane a wani garin ma yake daban ba garinsu ba. Lokacin da Alhaji Jafar yazo garin malam ya fada Masa komai yanda sukayi da Mahmud din, Alhajin yasa aka Kira shi ya Kara jajanta Masa sannan ya nemi ya fadi garin nasu a mayar dashi Dan da gani Dan manyan mutanene. Nan fa ake yinta Dan kekashe kasa yayi yace shifa ya manta sunan garin nasu akayi juyin duniya yace sai dai ko Nan gaba idan Allah ya nufa ya tuna, abinda ya tuna ma daga baya tunanin yazo Masa, haka suka hakura badan sun amince ba bayan ya tafi sun tattauna da Malam din akan lamarin inda Suke hasashen ko bacin Raine ya baro shi da gidan ya gwwmmace yayi zaman sa a Nan kafin ya huce ya nemi komawa gidan. Nan yaci bada da Zama da Malam Yana kwasar ilimi kala kala. Nan da Nan ya Zama Dan gida suka dinke da Habib duk da ze iya girmar Habib din da Kamar shekara biyu dan yayi Kamar sa'an Abdul Hakeem. Bai cika wata shida ba Allah ya kawo aikin NGOs din Nan Wanda aka sakewa makarantar fasali da tsari suka sayi wani katon fili na makudan da sunan makarantar akayi gine ginen hostel din Yara suka dauki ma'aikata suka gyara tsarin karatun saboda kwazon Mahmud har co-ordinator din Shirin Muhammad Sameer ya dauke shi aika a shiyyar Katagum local government din ya Zama shine idon su a Nan, tunda ya iya rubutu da karatu. Habib ma Yana bada gudunmawa sosai a aikin duk da Shima nasa aikin da ma'aikatar ruwa ta Nan local government din tasu. Wannan kenan. ____ Syprus. Zuwa lokacin su zahra karatu ya Mika, tun tana saka Rai da zuwa Nigeria har ta hakura Kuma abinda ya Kara Bata mamaki sau biyu Abba da Abdul Hakeem suna zuwa ganinta idan harkar kasuwanci ya kawo sun Istanbul.Amma Koda wasa Basu taba ce Mata ga lokacin da zataje gida hutu ba. A haka har suka hada shekara biyu a kasar, da gaske gida take son zuwa shi yasa lokacin da hutunsu ya gabato batayi shawara da kowa ba ta kama shirin barin qasar, online tayi komai Kamar su Sajida sai da komai ya Zama daidai sannan ta fadawa Uncle Haisam Shima bai hanata ba yasan tayi hakuri, Mama Hanifa ma ta waya ta fada Mata Nigeria zata wuce kawai, haka Ummee ma ta wayar itama ta fada Mata taso ta hanata Amma sai tayi wani tunani kawai tayi shiru kudade dai to tura Mata masu yawa Wanda har saida Zahrar ta Kara kiranta tana tambayar kudin ma meye haka da yawa? Tace ta turo Mata ne kawai ko idan take zatayi wani abun, godiya tayi Mata sosai hakan Kuma dabi'ar Zahrar ne komai kankantar Abu idan akayi Mata alherinsa zatayi godiya Kuma ko waye ta Bata Bata duba ai iyayene. Kwana biyu suka Kara da akayi hutun shima visa din su Khadijah ne Bata Zama ready ba. Lokacin da jirginsu ya dauka a Aminu Kano international airport taji ta sauko ta shaqi iskar Nigeria ji taji Kamar a Aljanna take lallai kowa yabar gida gida ya bar shi, saukar safe sukayi wurin karfe Sha daya ba yanda su zahra da Khadijah Basu da zahra ba akan ta zauna ta Dan huta kona awa daya ne a gurin sajida Amma tace A'a Azare tayi Kira su Anisa ne da Fatima suka bi Sajida Su dan huta kafin driver dinsu ya karaso tunda ba nisa tsakanin kazaure da kano, Kuma Gwammaja kan hanya ne. Shatar taxi Zahra ta dauka ta kaita Kano line Dan direban taxi din ta tambaya Ina zata samu motar zuwa Azare ya fada Mata akwai gurare Amma ita Kano line yafi Mata kusa. Har cikin Tasha Mai taxi din ya shiga da ita gurin motocin arear Bauchi, tayi Masa godiya sosai ta kuma Kara Masa kudi akan yanda ya bukata.
🏠