NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 136

ina Jin juma Amma kullum zahra da fargaba take kwana har zuwa lokacin da ta Samu labarin dawowar su sajidar a bakin Maryam Suraj wata kawarsu. Kallo saiya koma sama Wai shaho ya dauki giwa ita Mai kawo bakuwa sai duk suka Zama 'yan kallo. Hannun zahra sajidar ta Kama ta nufi bed in ta da ita tana fadin "wannan wace irin ranar farin ciki ce bestie wallahi ranar nan tana daga cikin ranekun da bazan taba mantawa dasu ba cikin tarishin zamana a syprus, pls bestie talk ya akayi haka ta faru Dan Allah kece ko gizo idona yake mini ne Dan Allah kiyi magana". Ita dai zahra ba baka sai kunne, ai ita nata mamakin yafi na sajidar sau dari idan da Wanda Allah ya yiwa gyadar dogo ai ita ce, ba zato ba tsammani Allah yayi Mata irin wannan suturar bama 'yan Nigeria ba A'a aminiyar ta sukutun ya kawo Mata kasar, ba abinda zata cewa mahalicci sai godiya take a Nan tayin sujudushshukur ga Allah. Sai da ta goge hawayenta sannan ta Samu damar magana suka gaisa da sauran yayin da Anisar ta cire hijabin tana fadin "Ai Kuma saidai kowa ya hakura da cin fizzar Dan na fasa fitar kawai ayi abinci tunda Naga bakuwar tamu ce ko sister" ta fada tana kallon sajida. "Kwarai kuwa ai dukkanku kowa ya kwana da sanin Zahra Muhammad sani ko?". Gaba daya suka zubawa Zahra idanu suna fadin sosai ma kuwa, niba har gaisawa munayi ba some times idan Kuna vedio call lokacin muna Sudan" inji Khadijah. "To ai ita ce gata a gabanki zahiri" Khadijah ta Dade tana mamakin abun ita sai taga Kamar canza Zahra akayi tasan dai yesss ba karya zahra Mai kyauce na a bugi kirji a fada, amma sai taga wannan Kamar ma Bata taba hada dangantaka da 9ja tamu ba, komai nata classic ne. Nan suka baje hajar hirar yaushe gamo, har kusan karfe goma na agogon kasar suna tare anan su sajida suka fada Mata gwamnatin tarayya ce ta dawo dasu Nan tunda suna under scholarship ne shine aka rarrabasu kasa kasa su Allah yasa suka shigo cikin daliban da aka kawo Nan din. Har daki suka raka Zahra a Nan ta Basu fizzar tunda Daman tazo da ita daga gidan uncle Nan ma sun jima kafin su koma. Ai tun daga ranar wata nutsuwa da kwanciyar hankali suka Samu kyakykyawan muhalli a zuciyar Zahra, haka itama sajidar duk da Daman ita tana da masu dauke Mata kewar gida, Suma su sajidar sau da yawa suna bin Zahra a wasu weekend din zuwa gidan uncle Haisam din Amma su basa kwana duk da irin nacin da zahrar ke musu. A haka karatunsu ya Mika har sukayi exams, Mama Hanifa taso Zahra taje Mata tayi hutu Amma Haisam yace tayi hakuri sai hutun karshe session. A haka suka Kare hutunsu suka Dora da karatu, ba Sajida ba hatta su Khadijah suna Jin dadin Zama da zahra gashi Sam abin duniya Bai rufe Mata ido ba, Dan ta ko'ina kudi ne ke sauka a Account din ta ba daga 9ja din ba, ba daga Jordan ba, ba daga turkey ba, kowa kokarin farantawa zahra yake zuwa lokacin tayi wani irin mahaukacin kyau na ban mamaki ga wayewa da wayon zaman duniya ta Kara Zama 'yar gayu Kamar me Dan ba karya matar Uncle Haisam Yar gayu ce sosai kamar Auntyn ta Hasana tasan yanda ake tattalin jiki matuka. Har zuwa lokacin ba ruwan Zahra da saurayi bil hasal ko aboki namiji Bata dashi, akwai wani Dan Syria Omer yaso Zahra Kamar kaddara Amma ta shafawa idanunta toka tace ba wannan maganar yace to su Zama friends Nan ma tace lah lah. Dole ya hakura saindai duk inda zasu hadu sai yayi Mata magana idan abu ta saya duk yawan kudin shi ze biya. Lokacin hutun karshen shekara Zahra taso zuwa Nigeria tunda taga su sajida nata Shirin tafiya, ta kwallafa Rai sosai akan zuwan Amman sai Ammah ta hanata zuwan tace taje Jordan idan hutun ya kusa karewa ta dawo Nan gurin Mama Hanifa ta karasa Abdul Hakeem zezo ya ganta. Ba haka taso ba da har tayi niyyar Kiran Abban ta fada Masa sai Kuma tayi tunanin kada Ammah tace ta Kai Kara dole ta hakura tunda Bata San nufin Ammah din ba data hanata zuwan. Taji dadin zuwa Jordan din sosai, dan Ummee na Shirin zuwa Saudi Arabia ne ma zuwan Zahrar ne ya kawo Mata tsaiko, tare suka tafi bayan ta huta, a can suka tarar da Aunty Nawwara wadda taje zuwa na musamman tunda lokacin ana daf da bikin aurenta inda za'a kaita Bagdad (Iraq). Sunyi sati daya zuwa suka nufi makka sukayi Umara, sosai Zahra ta mayar da hankali gurin addu'a akan matsalolinta na yanda rayuwa ke walankekuwa da ita Bata rasa komai ba Amma aure Yana neman yafi karfinta dah kudi ko kyau ke sawa mace ta auru tasan da yanzu ba wannan zancen ake ba, sai dai tasan duk Dan Adam baya wuce tasa kaddarar sai dai neman sauki gurin Allah s.w.a. Madina suka koma da suka Gama umarar,basu Dade ba suka koma Jordan. Lokacin da hutunsu ya taho garewa zahra ta koma syprus. Gidan uncle ta Fara Zama kafin daliban su dawo tunda ana saura one week ayi resuming ta dawo. Karatu suke ka'in da na'in ba Kama hannun yaro, amincin ta da Sajida ya Kara karfi tamkar uwa daya uba daya suke, Dan lokacin da sukaje hutu sajidar har Azare taje ta gaishe da Ammah ta karbowa Zahra sako. Duk lokacin da za'a yaye dalibai makarantar tana hada gagarimin taro tana baiwa bes
🏠