nufi nasa gurin duk da makarantar ta Sami cigaba sosai kamar ba makarantar amajirai ba anyi Mata tsari sosai a zamanace Dan har hostel garesu sama da kasa da gurin koyon sana'a Kuma ana musu abinci basa zuwa bara, sannan akwai malamai da aka dauka suna koyar da karatun boko tun daga mataki primary, junior, zuwa senior, secondary suna kokarin Fara turo dalibansu zuwa manyan makarantu, sun Sami wannan cigaban ne karkashin wata kungiyar NGO ne.
Lokacin da Mahmud da Habib zasu fita Malam yayi gyaran murya duk su biyun suka juyo, Mahmud yayiwa alama daya dawo shi Kuma Habib ya fice..
Nan kusa da Malam ya zauna ta lakwashe kafafuwansa kamar zaman daukar karatu.
A hankali Malam yake Kare masa kallo shi kadai yasa abinda yake kissimawa a zuciyarsa sai Kuma Allah daya hallice shi.
Sun dauki kamar minti uku a haka kafin Malam ya magantu.
"Mahmud"
Malam ya Kira sunansa.
Cikin ladabi ya amsa Masa da "na'am Malam".
"Kasan dalilin dayasa nayi kiranka?".
Cikin ladabi ya amsa da "A'a"
Cikin wani irin yanayi Malam yace "wani nauyin Kuka aka Dora min Wanda na rasa ta inda zan Fara maka bayani".
Zamansa ya gyara Yana Kara fuskacin Malam din Yana fadin "Malam ka fad'a min ko menene ni maiyi maka biyayya ne In Sha Allah".
"Ai kasan gidan Alhaji Jafar nawa za'ayi bikin yarinyar gurinsa ko?"
Kai ya gyada Masa tare da cewa "Eh na Sani ba Zahra za'a aurar ba?"
"Eh ita fa, to an samu wata matsala ne wadda ta haddasa kasa auren a wannan karon ma kamar lokutan baya Amma wannan sai yafi na bayan Muni domin kuwa saura ba kaiwa ga Fara bikin Amma wannan Saida abun ya kurace har an saka yarinyar a lalle sun Fara duk kwaramniyar su ta Mata a lissafi saura kwana uku daurin aure sukace sun fasa, shine shi Alhajin yace na meni shawararka idan ka amince zaka iya auren yarinyar ya baka za'a daura muku aure ranar juma'a inshallah Allahu".
Da sauri Mahmud ya dago Yana kallon Malama bakinsa har rawa yake yama kasa furta maganar dazai fad'a Kai ya shiga girgizawa dafa shi Malam din yayi Yana fadin "ka nutsu bazamuyi maka dole ba idan bass sonta sai a nemi wata mafutar"
Da kyar ya tattaro nutsuwarsa ya kalli malam yace
"Ba haka nake nufi ba, gani nayi yaushe nakai matsayin da za'a bani irin wannan yarinyar aure kamar tafi karfina ni almajiri ne wanda ban aje ba banba wani ajiya ba, kuma tana da ilimi Mai zurfi ba lallai ta yadda ta zauna dani ba".
"Ba wannan nake son jiba daga bakinka fadin Kai ko wanene ba taso ba Alhaji shi yafi sanin Kai ko waye amsa muke bukata zaka iya aurenta ko bazaka iya ba ?".
Cikin alamar sarewa yace "wane ni ice bana son wannan yarinya na karba na gode Allah ya saka da Alkhairi".
Ya fad'a cikin wata irin murya Mai sanyi.
"A'a kaje ka nutsu kayi shawara sai ka fad'a min duk huku cin daka yanke, tashi kaje dare ya farayi".
Yunkurawa yayi ya tashi Yana fadar "sai da fade"
"Allah ya tashe mu lafiya" cewar Malam.
Daga falon malam Mahmud bakin titi ya nufa inda yake tunanin ganin Habib Yana son ya karbi lifan dinsa zaije wata unguwa.
Gurin Ashiru Mai shayi ya Fara zuwa baya nan sai su salisu da Bashir Suma duk mutanen Mahmud ne hannu ya Basu saka gaisa sannan ya tambayesu Habib wani ne daga can gefe yace "ai yanzu ko runhu ka rike yana gurin Ubaidat kasan mutumin naka Yana neman dauko dala ba gammo".
Ya karasa fad'a Yana dariya Bashir ne yace "ko wani Abu ne Naga ko Zama bakayi ba"
Da tsaki yayi Yana Dan dafe kujerar kusa dashi Yana fadar "wlh lifan dinsa zan karba zan danje unguwa".
"Kai haba saboda lifan kake wannan zagaye zagayen ga nawa kayi amfani dashi mana".
Ya fad'a Yana Miko Masa makullin ya karba Yana godiya.
Kai tsaye zaranda hotel ya nufa.💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️
MAMAN FATIMAH.
✨Page two✨
________📖🖋️
Safa da marwa take tun bayan gama sallar insha'in ta, ta Kira layin wayar tafi sau shurin masaki Amma ta kasa samun Wanda take nema, gumi ne yake fama tsatsato Mata daga goshinta, ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Gafen gadonta ta koma ta zauna Kara kiran tayi cikin ikon Allah sai Kiran ya shiga da sauri ta nufi kofar toilet dinta na daki ta shige.
Bata tsaya amsa sallamar wadda ta Kira din ba ta Fara magana "Asabe me yake faruwa ne tun jiya nake neman wayarki Bata shiga Ina cikin tashin hankali komai fa Yana nema dagulewa, ba alamun nasara a wannan karon tunda komai ya kankama".
Shiru tayi tana sauraran wadda ta Kira Asube ta jima tana sauraran ta kafin tayi dariya tace "haba yanzu naji magana da har hankalina ya tashi ki rike sauran maganar sai kin shigo gobe ma karasa".
Ta kashe wayar ta bude kofar toilet din ta fito cikin farin ciki da walwala sabanin yanda ta shiga.
___
Mahmud.
Ya jima a cikin hotel din kafin ya fito zuwa gurin securities din da alama sun saba sosai Dan yanda suke bashi girma sai abin ya baka mamaki makullin lifan din Wanda ya barwa ya miki Masa tare da fadar
"Yallabai an zubo petrol din".
Lokaci daya Kuma Yana Miko Masa kudi, kallon na mine yayi masa.
"Kudin sunyi yawa ne a sayan man Saida naje na duba maga yawansu