NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 39 of 136

bare idan suna dakinsu su kadai ta dinga fadin magana kenan, ko ci kanki zahra Bata ce Mata sai ma wani lokacin Hameeda ke kwabawa Nan da Nan Kuma su hau sama da ita. Ranar da zasu tafi harda ZAHRA a 'yan rakiyar, Mama ma taso zuwa Abba ne ya hanata ya Kama fadan me zatayo. Har hostel Zahra ta rakasu Lokacin da zasu taho ne Hameeda ta Fara share hawaye itama zahra ta Kama, Saida ya Hamza yayi musu Jan Ido suka daina kukan, Yayin da Ya Abdul Hakeem yake musu dariya Yana fadar "Banda tsabar shagwaba ta lalacewa har wani kuka kuke Kamar wasu 'yan J's one". Wani kallo ya ai kawa zahra na Baki Fara kuka ba.sai kin ganki a tsakiyar masu jajayen kunne tukunna Dan ma dai kema samman kalne ya gada a zuciyar sa. Sai bayan magariba suka dawo gidan. Ba'a fi sati biyu da tafiyar su Hameeda ba visa din su Zahra ta fito ita da Abdul Hakeem. Sai ana ya gobe zasu tafi Ammah ta fadawa Mama. Ai Kuma tayi korafin abin Dan har Alhajn ta fadawa yace shima jiya yake Jin labarin tunda Saida komai ya kankama sannan suka Kira suka fada Masa Dan kada ya Hana. Da safe Bala dureba ta dauke sai kano inda zasu tashi. Satin Abdul Hakeem hudu a can Dan Bai taho ba Saida ya raka Zahra har syprus din a gabansa komai ya kammala ranar da ze tafi Zahra tayi kuka Kamar idonta ze fita sai a sannan taga ba karamar wauta tayi ba data yarda da wannan karatun, dadin ta daya da uncle Haisam a kasar ko banza tana da gurin zuwa a debe Mata kewar gida. Ta Fara karatu cikin nasara Bata da wata matsala ta zahiri saidai sau da yawa tana shiga dogon tunani akan al'amuranta ta rasa Gane daga Ina ne ake samun irin wannan akasin? matsalar dai iri daya ce, Kuma salon tafiyar iri daya ce sai Dan banbancin da baza'a rasa ba. Suna yawan waya dasu Ammah da mutanen Jordan, lokacin data Kira Hameeda mita ta ringa yi Mata akan tana boye Mata wani Abu tunda gashi Saida ta bar kasar kana ta Kira ta. Da kyar ta fashimtar da ita abun ne yazo da gaggawa itama Bata sani ba Saida komai ya Zama ready, Kuma tayi ta try din ta sameta Bata Samu ba lokacin ana fama da matsalar network a area dinsu. Zahra najin dadin Zama a kasar duk karshen sati a gidan uncle Haisam take yin weekend din ta, sai Monday da safe motar Embassy take dawo da ita. Tsakanin syprus science University din wadda take kyrenia city a arewacin syrups din da capital city din dake Nicosia tafiyar kilometers talatin ne, kawai daga Baya ma da uncle din cewa yayi ta baro cikin makarantar ta dawo gidansa kawai da Zama sai a ringa kaita kullum itace taqi tana ganin Kamar abun da wahala yau da gobe sai Allah daga nesa nesa dai. Yau ma Monday da wuri motar Embassy din ta kawo ta, tayi gaba da wasu daliban zuwa mabanbantan makarantu inda suke karatunsu.Ganin da saura Kamar awa aya da rabi kafin su shiga lectures yasa ta wuce hostel Dan ta aje kayan da tazo dasu. Tana cikin tafiya tazo gota wani hostel Kamar a mafarki sai taji Kamar ana hausa a dakin abin ya Bata mamaki tayi Kamar ta koma ta duba sai dai tayi gaba tunda bin kwakwkwafi haramun ne. Lokacin da suka Gama lectures din Bata koma hostel ba, karatu suka zauna sunayi da wata course mate dinta 'yar kasar Lebanon Asseyeh tasu tazo daya sosai saboda itama akwai nacin karatu ga Kuma kwanyar Allah ya hore itama, uwa uba ga rikon addini tunda su dai kasar sai a hankali kawai culture din ta rinjayi addinin, Dan wasu Ma sai kaga suna sallah zaka Gane musulmi ne. Yamma likis su Zahra suka nufi hostel, haka nan Zahra taji tana son karabi ta wurin inda taji ana magana da Hausar nan, can ta nufa bayan sun rabu da Aseeyeh. Very lockly kuwa tayi Dace da wata daga ciki ta fito tana waya bahaushiya sosai.A shape ce a jikinta ta atamfa sai karamin hijabi a jikinta da alama Kamar fita zatayi.Dan tsayawa zahra tayi har ta karasa wayar, cikin nuna zallar farin ciki zahra ta nufeta tayi Mata sallama. Da sauri ta juyo Jin an Mata magana da Hausa cikakkiya. "Wa'alaiki Salam" yarinyar ta amsa Mata tana kallon zahrar da murmushi itama a fuskarta. "Masha Allah wallahi naji dadin ganinki kema daga Nigeria kike". Zahra ta tambaye ta. "Eh daga Nigeria muke muna da Dan yawa zamu Kai goma". Mamaki ne ya Kama zahra ganin Bata taba ganinsu ba Koda wasa. "Ikon Allah! Amman dai baku Dade ba ko?" Kai ta gyada "Mata gaskiya Kam ai ba school daya muke ba mu a Nan mu hudu ne, sauran suna different Universities ne on transfer mukazo nan daga Sudan tunda can rikici ya d'ai d'aita Qasar. Zo mu shiga ciki ki gaisa da sisters Dina kafin na dawo zan fita na samo Ko fizza ne yau bamuyi girki ba". Ta fada tana juyawa ciki, bayan ta zahra tabi suka nufi ciki. "Khadijah ! Fatima,! Sajida! Kuna Ina ku fito gashi mun Samu qaruwa". Kowacce barin abinda take tayi ta nufo kofar tana fadin "Anisa menene?". Ai kafin tayi magana Zahra tayi Arba da sajida Musa, sajidar ta ta FGGC KAZAURE. Cikin wani irin farin ciki suka rungume juna Zahra sai kuka Dan wani abune da Bata taba zata ba robonta da sajidar tun suna cikin bala'in Sudan kafin wayar sajidar ta salwanta shi kenan suka da
🏠